16

239 21 9
                                    

Washegari girke² akeyi tamkar ana biki a gidan Abbu kowa na gidan yazo duka 'ya'yan Ummy mata guda biyu Aunty Maryama da Adda Khadija hatta Mai martaba sanda yaxo ya gaida Malam tare da masa godia sosai kan rike kanwarsu da yayi shima ya zama kamar dan uwa Inna kuwa suna tare da Mama Muniba an kulla kawancen tsofoffi bayan anci abinci nan aka tarasu kan maganar auren yaran tunda kowa yana nan harda Baffa Auwalu sai a nan Ammi take jin cewa ashe akwai maganar aure tsakanin Yarima da Hafsat taso tayi gardama kan maganar Mami amma Malam ya tsawatar yace "Kul Fatima Allah bai haramta ba"

Nan Mus'ab ya gabatar da kudirin da ya dade da kudirtawa a ransa ya dubi Abba Sadiq yace "Abba na daman dalilin hada zumunci kuke son hadani aure da Hafsa ko"

Suka ce Eh yayi murmushi "to Hafsa dai bata so na amman ta karbi zabinku sbd biyayya amman indai sbd zumunci kuke son hadamu to baza'a fasa ba don wani zumuncin ne zai hadu sbd Hafsa da Sadiq suna son juna ba tun yau ba amma ya sun hakura ne don alkawarin dake tsakanin mu"

Kallone ya koma kansu duk suka sadda kai kasa Abbu ya shafa kan Sadiq dake kusa da kafafun shi yace "Abubakar da gaske ne maganar da dan uwanka ya fada kana son Hafsatu"
Sadiq ya gyada kai alamar eh Abbu yakai duba kan Hafsa dake wasa da hannun ta yace "Ke Hafsatu kina son shi kema"

Mikewa tayi ta fice da gudu tana daria Mami ta rufa mata baya suma iyayen daria sukayi Mama Muniba tace "Ja'ira tana sonshi tunda ta gudu kuma ai sai ku fice ku bamu guri"

Su Yarima sukayi waje suna fita Sadiq ya rungume shi yana fadin "thank u Bro u r d Best"

Ture shi Yarima yayi yana fadin "dalla matsa ni yayan ka ne fa kuma har ynx na fi ka tunda ni mijin mace biyu ne" dariya sukayi kuka fice daga gidan gaba daya

Mami ta rungume Hafsa tace "wayyo Besty matar yaya na ashe abinda kuke kullawa kenan ban sani ba kuma wai daman Yarima ne yaje neman aure na ai wlh badan an fasa dake ba da bazan aure shi ba"

Hafsa ta harareta "ai bamu kadai muke boye abin ba ehe don haka koda ba'a fasa ba haka zaki hakura mu aure shi tare tunda kina sonshi a gefe guda kuma ga Xee"

Tabe baki Mami tayi "yo ance miki tsoronta ni nake duk da ma yanxu naga tayi hankali ai kuma 'yar uwata ce so ba wani abu In Sha Allah zamu zauna lfy"

"Allah yasa" cewar Hafsa

Abbu ya gyara zama yace "to Maa Sha Allah tunda ga abinda ya faru Malam muna neman auren jikar ka Hafsatu da fatan zaka bamu"

Malam yayi murmushi "duk da cewa kanin mahaifinta na nan amma ko shi ni na daura mai aure sbd haka nine madaurin auren ta kuma na baku sannan mu ma muna neman auren jikar ka Hafsa"

Abbu ya murmusa "muna godia kuma mu ma mun baku bama son kuma a dauki lkc In Sha Allah"

Nan aka tattauna aka saka ranar aure Sati biyu haka kowa ya tashi cikin farin ciki Abbu ya kira Mai martaba da Waxiri ya sanar dasu cewar ya saka ranar auren Yarima kuma tare da na Zainab duka rana daya basuyi musu ba don tamkar mahaifinsu suka rike shi komai nasu yakan iya yanke hukunci tun bayan rasuwar Baban su Mu'ayyad mahaifiyarsu Umma Zainab bata yadda su aikata wani abu ba tare da shawaran shi ba

Malam suka fara shirin tafia gobe yayin da za'a bar Ammi ta kwana biyu da dangin ta Malam,Baffa Auwalu da Inna ne suka tafi an musu shaa tara ta arziki mota guda Sarki ya bayar aka maidasu har gida

Shirye²n biki aka fara angwaye duka ba zama Abbu da kanshi ya biya sadakin dukansu uku yayin da Mai martaba ya sai musu gidaje Yarima a Tambari Housing Estate gidanshi mai bangare uku nashi,na Zee da kuma na Mami shi kuwa Sadiq a Gombe tunda chan kasuwancin shi yake shima gidansa bangare uku ne shi da matar shi da kuma Ammi, Abba Sadiq shi yayi musu kayan daki har da Xee yayin da aka bar su Ummy dasu Adda Maryama da hada kayan lefe a bangare daya kuma Amaren suna ta shan gyara domin na musamman aka baiwa Aunty Halima Juzy Saloon & Spa aka bata kwangilar duk wani gyara da amare ke bukata hatta kunshi da kitso nan aka musu suka fito shar dasu tamkar a sace su a gudu

Ana saura kwana biyu daurin auren Ammi ta tafi dasu Gombe  don achan aka shirya musu Kamu da kuma Family & Friends din da zasuyi in suka dawo Bauchi kuma ayi dinner Zee ance ta shirya su tafi tace a'a ita nata daban zatayi in yaso dinner din ayi tare gaba daya tayi sanyi tunda taji cewar Mami ma 'yar Familyn su ce gashi kawarta Sauda anyiwa mahaifinta Transfer sun koma Ibadan haka dai ta daure take komi tunda tana sonshi babu yadda ta iya face ta zauna da abinda yake so wato Mami

F&F din duk su Adda Khadija sun halarta a Gomben banda Ummy ya kayatar sosai a Custodian Hotel akayi yayinda a ranar ita kuma Zee tayi nata Kamun a cikin gidan sarautan anyi hakan ne don ango ya samu hhalartan duka F&F din washe gari su kuma su Mami sukayi Kamu da yamma a Aliens garden washegari dubbannin mutane suka shaida daurin auren Yarima da Hafsa aka dunguma aka dawo Bauchi kuma aka daura auren Sadiq da Hafsa da kuma Yarima da Zainab  karfe takwas aka shirya tafiya Dinner a Zaranda Hotel sun sha kyau kwarai da gaske Yarima Mus'ab da matayen shi biyu a gefensa Sadiq kuwa da amaryar sa Hafsatou buki ya kayatu kwarai da gaske Maa Sha Allahu

Zamansu lafia sukeyi da farko Zee taso kawo raini amman Mus'ab ya tsawatar mata ya nuna mata sam bzai lamunta ba Mami gaba take da ita tunda itace Uwargida haka dole ta hakura ta fara bata girma

Sadiq da Hafsat ma shiru suke zaune abinsu ko Ammi dake gidan bata jin Kansu

Baffa Auwalu yayi nadama sosae ya kuma baiwa Ammi hkr tare da neman yardan ta kan cewar yana son aurenta amma firr taki yarda a ranta tace bata isa zaman kishi da Amina ba matar sa don akwaita da bala'i har gaban Malam yakai zancen Mlm yace tunda bata so a barta don haka dole ya hkura



Tammat bi hamdillah anan na kawo karshen wannan gajeren labarin nawa da fatan kunji dadin shi sannan duk wanda yaga kuskure ciki to kofar gyara a bude yake

My Heedah nd aysherudahmad nagode kwarai da bibiyar lbrna da kukayi

Amina Abubakar (Meenauwal)
Hussain 80k
Humayrah B Melody (Cwt Melo)
Meenat
Mommyn Mufeeda
Ma'ani
Dr Zain
Omaymerh (Ashmad)
Deejerh 'yar Mama (Lil Sis)
Kamaal Dan Gombawa
Faltex Farhana (Maltex)
Fatima Usman (Momma)
Kingboy Isah (Son)
My Ablancy
Surayyahms
Billyn Abdoul
Da ma duk wanda ban ambato ba I luv u all💓💓💓💞💞💞


YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now