03

345 30 1
                                    


Kuka sosai Xieey takeyi ta kama hanyar ofishin principal don bata jin zata iya hakura yau din nan
Nocking tayi bata jira ya bata izini ba ta afka ciki ganin ita ne ya girgiza kai cike da takaicin rayuwa irin ta 'ya'yan manya Sam babu tarbiyya babu ko gaisuwa ta fara magana "Sir ka kira min Daddy na yanzu please" baiyi magana bai sai wayar da ya tura mata cikin gaggawa tayi saka lambarshi don bata da lokacin duba contact ta kira babu jimawa aka dauka domin Dad din yana ganin kiran yasan ita ce yadda yake masifar kaunar ta kasancewar ita kadai ya haifa mace cikin kuka tace "Daddy help me please" hankali tashe jin kukan ta ya furta "me ya faru Momy nah waye ya tabaki fada min duk fadin garin nan" cigaba tayi da kukan tana fadin "nidai Dad zan dawo gida please ka aiko a daukeni YARIMA ne" cikin lallabi yake bata hakuri har dai ya samu ta sassauta kukan nata "to fada min me Yayi miki daga zuwanshi makarantar" "nikam a'a Dad kawai nafi so muyi maganar gani gaka" ta fada cikin shagwaba "to kiyi hkr kinji idan kukayi hutun mid term zan aiko a dauke ki kinji Mama nah" a haka ya lallashe ta ta koma hostels badan taso ba.

A yayin da MUS'AB ke chan gurin su Hafsat suna ta nishad'in su don zuwa yanzu 3ple H itama ta sake dashi sai raha suke (nikam ina mamakin wannan dan Sarkin da sam babu ji da kai da kuma miskilanci irin na sarauta a tare dashi). yana daria yace "wai ni Hafsatou black meysa kike son Fanta ne? don zaman mu anan kinsha Fanta uku" ta harare shi cikin sigar wasa "Allah ni Angon Besty ka daina yaushe nasha uku?" Ganin yadda ta turo baki suka hadu suna mata daria ta musu shiru Lamido tace "Yaya in fada maka gaskia Kaine ai baka gane ba wato fa in baka sani ba Besty fullo ce shiyasa take kaunar Fanta da burodi" zaro idanu yayi harda wani kama baki kamar mace "au daman fullo ce ai ban lura ba sbd naganta Blacky shiyasa, kice ma harda Burodi" suka sake kwashewa da daria ita kuwa ta shaka kiris take jira ta fashe ta fara magana "eh anji bak'ar ce kaima ai naga ba fari bane kuma da akeyi da Fulani Allah yasa kuma tushenku kenan sbd haka bazanji haushi ba" ta mike zata tafi suka tashi suma Lamido ta tattara plates din da sauran ledojin suna cigaba da tsokanar ta banza ta musu tayi gaba abinta.

Bayan sati biyu sukayi hutun midterm break don haka wadanda ke cikin gari suka fara shirin zuwa gida don yin kwana biyu kuma da yike alhamis da juma'a ne sai ya hadu da weekend so sai Sunday zasu dawo amman banda masu nisa don sukam babu inda zasu je cikin su harda Hafsat Blacky (nima na d'ana sunan) kasancewar ta 'yar Gombe tun safe Lamido take mata magiyar kan tazo suje gidansu amman taki yarda Sam har MUS'AB yazo tafiya da ita tace "please Yaya ka kira min Ummi a waya mana" babu musu ya kira ta ya mika mata wayar jin Ummin ta dauka "Hello Ummi nah" murmushi tayi jin muryar Hafsat "Baby nah ya akayi ance kuna tahowa amman shiru naga har Zainab ta dawo" "eh wlh Ummi kinga Besty tak'i tahowa kuma kinga babu inda zataje shiyasa nace muzo tare amman ta k'iya" ta karashe cikin jin haushi Ummi ta murmusa "Oh Hafsatou kenan sam bata son shiga mutane bata wayar" (Ummin tasan ta ne sanadin Hafsat Lamido da yake tana zuwa mata visits) mik'a mata wayar tayi Hafsatou da ta kama kai jin ankai k'arar ta tasan dole taje ta amshi wayar tana gayar da Ummi cikin girmamawa "Haba Momma nah kuma shine zaki ki biyo 'yar uwar taki ko baki son zuwa waje nah ne?" Ummi ta fada bayan sun gaisa 3ple H ta girgiza kai kamar tana ganin ta "a'a Ummi ba haka bane yanzu zan shirya mu taho" "yauwa ko ke fa 'ya ta maza kuyi sauri ina Yayan naku yake?" Kallon shi tayi wanda ya zuba mata idanu tun fara wayar yana jin dadin yadda take girmama Ummin tashi sbd yana kaunar ta bai kuma hada ta da kowa ba Hafsatou ta amsa "gashi nan Ummi a bashi?" Ummi tace "a'a kice dai ya taho min daku da wuri tunda direban ya iso" to tace sukayi sallama ta mika mishi wayar tana hararan Hafsat Lamido da har ta hado mata kayanta don zumudi....

Shima hararar ta yayi "malama Blacky yadai kike hararan mata ta" murguda baki tayi "to itama wa yace takai karata gurin Ummi!" yayi daria "ai maganin mai taurin kai kenan kuma nima daga yau na gane in kikayi abu da Ummi zan dinga hada ki" ya fada yana daukan karamin akwatin kayansu zuwa mota da sauri driver ya kariso ya kar'ba ya sanya a but suka shige baya shi kuma ya shiga gabar motan direba yaja suka kama hanyar cikin gari suna d'an taba hira shi da Malam Idi yayin da Hafsat Lamido bacci ya kwashe ta daman ko baccin dare taki saboda za'aje gida 3ple H tana ta kallon gefen hanya yanda ciyayi ke tsere tana murmushi kamar ance ta dago suka hada idanu dashi ta madubi yana kallonta..............

Muje zuwa readers

#Mushaf
#Oneluv

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now