Murmushi tayi tare da Kawar da kai ganin kallon nashi ba mai karewa bane har suka iso bata sake kallon inda yake ba Babbane kuma ya hadu matuka wato Fadar Sarkin Bauchi a ranta tana mamakin wadan da suka fito daga wannan masarauta masu mabanban ta halayya wasu mai kyau wasu kuwa ko kare bazai ci ba misali Xieey
Ta tayar da Hafsat tana fadin "ke kasa tashi dallah an iso" ta tashi tana dan waro idanu "Amman gaskia anyi sauri" bata tanka ta ba illah fitowa da sukayi suna rige²n isa bangaren Ummi da gudu suka shige tana zaune kuyangu suna matsa mata k'afafu ganin shigowar su ta musu alamar su fita da hanzari suka mik'e suna gaida su sannan suka fita su kuma karisawa sukayi suka rungumeta suna farin cikin ganin ta shigowa yayi guard dinshi na dauke da akwatin kayansu bayan ya ajiye ya fita Mus'ab ya balla musu harara "da'allah Ku d'aga ta so kuke Ku karasa ta" Ummi tayi daria "oh to ina ruwan ka su da Ummin su?" ya wani shagwabe fuska "Allah ni zan tafi gidan Mamy na naga daga zuwan wad'an nan yaran har an fara min wariya" gwalo suka mai Ummi tace suje suyi wanka su fito cin abinci suka wuce dakin da Hafsat ke sauka idan tazo hutu gidan komai tsaf suka same shi wanka sukayi Hafsat ta sanya riga da skirt ita kuwa 3ple H doguwar riga ta saka Sea Green sai farar hula ta fito fes da ita domin shigar ta dace da kalar fatar ta mai duhu
Suka fito falo nan suka tarar da Mus'ab har yayi nashi wankan yana zaune a kasan kafet kusa da k'afafun Ummi ya daura kanshi bisa cinyar ta tana shafa kanshi suna tad'i sai zuba murmushi suke su Hafsat suka kariso wajen Lamido ta zauna gefen shi tana d'an turo baki " Allah Ummi a daina min haka ba nice auta ba" MUS'AB ya mata daria Ummi ta d'an ture kanshi "dallah tashi na manta ynx kai ba auta na bane" gwalo yayi mata "Ummi kin ganshi ko?" ta fada "rabu dashi Baby nah" ta mike tana nufar d'akin cin abincin dake 'bangaren nata tana fadin "kuzo kuci abinci kar Ku biye ma wannan matsokanin" sai lokacin ya juya yana kallon Hafsatou murmushi ya mata yana fad'in "Hafsy Blacky an mata ki tashi kije kici abinci munsan hali daman" murgud'a baki tayi "eh d'in dadin abin ma kowa yana ci" tayi gaba abinta suka bi bayanta suna mata daria har suka shiga dinning room d'in MUS'AB yana fad'in "Blacky acici tafi a hankali mana" bata kulasu ba taja ta zauna wata kuyanga dake tsaye tana jiran su zazzauna ta zuba wa kowa abinda yake so ta fara tambayar su murmushi Hafsatou tayi "jeki kawae zan zuba" cike da girmamawa ta rusuna tare da barin d'akin Ummi ma ta mike tana fad'in "ni fa kunsan yau Alhamis ina azumi bari in shiga gurin Umma(surukar ta) idan kun gama kuje Ku huta kunji " to suka amsa suna fad'in a fito lafia a babban faranti ta zuba musu Dambun shinkafa sannan ta zuba wa kowa lemon kwakwa ta tura musu kallonta kawai yake yi komai nata a nutse take tamkar wata babbar mace suka fara cin abinci har lau dai idanun shi na kanta Hafsat dake kula d duk wani motsin shi tayi murmushi ya bude baki zaiyi magana kawai ya k'ware ya fara tari (kunsan sha'anin Dambu) da hanzari ko wacce ta mik'o mishi ruwa suna ta faman sannu duka biyu ya karba ya shanye sannan suka kalli juna suka tuntsire da daria shima cikin dariyar yace "to ba shikenan ba nasan halin Ku da rikici duk wacce nak'i karbar nata ynx zata tara min mutane" harara Hafsatou ta aika mishi tare da mikewa alamar ta k'oshi suma mik'ewar sukayi zuwa cikin falon suka zazzauna Hafsatou ta d'auki remote ta chanza channel zuwa MBC Bollywood su kuma suka fara hirar dangin su.Xieey zaune gefen Dad d'inta tana ta kuka gaba daya hankalin shi ya tashi yayin da Umman ta ta mik'e tare da ta'be baki domin tana jin haushin yadda ya sangarta yarinyar ta fice zuwa Sasan surukar tasu nan suka had'u da Ummi suka fara hirar su
Da k'yar ya samu tayi magana "Haba uwa ta ya zaki taso ni daga fada sa'an nan kuma ki zo ki tasa ni gaba kina kuka kink'i ki fada min damuwar ki" ta share hawaye "Daddy ni wlhy YARIMA nake so kuma in ban same shi ba kana dab da rasa ni" "subhanallahi haba uwa ta ya kike kiran min rasa ki please ki daina in dai YARIMA ne ki kwantar da hankalin ki da zaran kin gama makaran ta zan same shi da maganar nasan yaro ne mai biyayya so bazai bada matsala ba" ta sake fashewa da wani kukan "wlhy ban yarda ba Daddy ni yau nake so kuyi maganar in ya yarda shikenan" dafe kanshi yayi yana takaicin rashin jin magana irin ta 'yar shi (LAIFIN WA?) oho "to shikenan naji je kici abinci anjima zan kira YARIMAn yazo muyi maganar dashi........" Mik'ewa tayi tana kwalawa baiwar dake kula da bangaren abincin ta kira kan ta kawo mata abinci tayi hanyar d'akin ta............Da DARE...............
BINABASA MO ANG
YARIMA MUS'AB
Short StoryAminan juna ne Hafsat da Hafsat wadan da suka kasance kuma masoya ga mutum daya wato Yarima Mus'ab yayin da a gefe daya kuma ga Zainaba masoyiya ga Prince din Hafsatus (Lol) wacce take ikirarin aurenshi ko ta wacce hanya tare da kudurin rabashi da k...