07

315 37 4
                                    


am back! Done wid ma Exams am sorry my peepss na saka ku jira....

Yayi kokari kwarai wajen ganin yayi yaki da damuwar shi da safe ya isa bangaren Abbah ya gaidashi kamar yadda ya saba idan har yana gidan sedai sama² ya amsa mishi ba yadda ya saba ba murmushi yayi na gefen baki domin yasan makircin waccan matar ce don yana da yakinin ita ce ta zuga Abbahn nashi kan maganar daren jiya..

Mikewa yayi ya nufi bangaren Ummi da sallama ya shiga suna zaune a falon tare da ita suna ta fira wanda rabi ta makarantar su ce bayan ya gaida ta suma suka gaidashi Hafsa ce ta fara gaidashi "Gud morning Yaya" ya amsa da "Mrng Wifeey" cikin yanayin shi na tsokana zaro idanu tayi kafin ta rufe fuska alamun taji kunya shikam dariya ma ta bashi Hafsatou cikin kulawa tace "Barka da safiya Yaya" murmushi yayi yana kallonta yace "Barka dai Bestyn mu hope kin tashi qlau" a takaice ta amsa da "lafia lau" nan Ummi tace "to maza masu lattin tashi tunda dai kun makara mukam munyi Breakfast sai Ku tashi maza kuje kuyi anjima kuje ku duba Maryama da jiki don bata ji dadi ba" amsawa sukayi da to suka nufi wajen cin abincin shi da Hafsatou tambayar shi tayi mai zaici yace "duk abinda zaki ci zuba mana" ta zuba musu sannan ta hada musu tea suka fara karyawan cikin nutsuwa take komi yayin da shi kuma duk abinda yake idanun shi suna kanta Ummi na ankare dasu daga inda take zaune "Fatan dai kayi bacci baka saka damuwa ba cikin ranka" Hafsatou ta fada ba tare da ta kalle shi ba "ni kuwa a duniya mai zai hanani bacci tunda kina cikin gidan nan" bakin shi ya furta ba tare da yayi zato ba
Kallonshi tayi da alamun tambaya yayi  saurin saita zancen shi wajen fadin "eh mana daman ai rashin fahimta nayi wa zancen amman tunda kika nuna min yadda abin yake tuni na gane kinga ko babu abinda zai hana inyi bacci" ta harare shi domin tasan ba gaskia bane amman duk da haka ta kyale shi ganin taki cewa komi ya dubeta "Anya ko Blacky kinyi bacci kodai tunani na ya hanaki sukuni ne? fada min" zaro ido tayi kardai mutumin nan ya hango jirgin ta yau ta boni duk yadda take yaki da zuciyarta wajen ganin ta hana ta son abinda take ganin ya haramta gareta amman sanda ya gane, ita kam zuciyarta batai mata adalci ba

Amman cikin karfin hali irin nata ta gallamai harara tare da nuna Hafsa tana fadin "kai Malam gata can fa kar santin abinci yasa ka mance da wadda kake tare" shi kuwa da daman tsokanar ta yake don har ga Allah bai fahimci komi a tare da ita ba yace "ke 'yan mata ai naga Bestyn ki ce so indai da gaske kuke da amincin naku ba sai kawae ku rokeni in hadaku ba hankali ku kwance" ta mike tana fadin "a kai kasuwa nikam domin duk mijin da Besty ta aura tamkar ya haramta ne agareni  beside ma ni mai zanyi da mai mata har biyu kuma gaka baki wuluk" ta karasa maganar cikin dariya shi kuwa gabanshi saida ya fadi domin ya razana da jin kalamanta ya mike da gudu ta wuce daki tana mishi gwalo ganin ya biyota ya girgiza kai "Zaki fito ne ai bani kike kira Baki wuluk ba kin manta kwalta ne ni" ya wuce zuwa wajen su Ummi wacce duk abinda suke tana kallon su a ranta tace "yau na shigesu yaran nan ga dukkan alamu sun kamu da soyayyar junan su ya zanyi in ya furta domin tabbas nasan YARIMA sarai baya boye maitar shi"

A fili kuwa dariya tayi tana fadin "ai ramako da azaba nan ka Saka ta gaba da fadin Blacky don kawae yau ta rama"
Hafsa tace "ai kam dai daman Besty bata barin bashi wlhy duk abinda akai mata sai ta rama shiyasa a Schl su Xieey suke ragar min wani abun don suna tsoronta ba karamin aikinta bane ta kamasu ta jibga kuma babu yadda suka iya"  

Ummi taji wani abu ya darsu cikin ranta amman ta yaya hakan zai yuwu kuwa? MUS'AB yace "ke kuma daman tsayuwa kike kina kallon su kenan amman dai bakici sunan ki ba don ko Granny bata daukar raini lkcn da take 'yan mata a kauyen su, a hakan zaki zauna ta dinga rainaki kenan idan na aure kun?" 
Remote Ummi ta lalubo ta jefa mishi ya kauce yana dariya "Sannu mai Ido ba dan ciki wato Uwar tawa kake bada labarin lkcn da take budurwa ina ka san hakan?" Cikin dariya yace "to Ummi ba Abbah Sadeeq bane yake bani lbr" 

  "To naji Zubairu je ka shirya kuje maza ku dubo Addar taku ni banson shiririta irin taka" ya fice yana murmushi abinshi Hafsa ta maida duban ta kan Ummi tana neman Karin bayanin zance shi na idan ya auresu ita da Xieey? Nan Ummi ta kora mata bayanin yadda akayi jiya tana bacci hankalin ta bai wani tashi ba sbd daman bata daura wa kanta kishi ba domin tasan gidan sarauta ba'a cika zama da mace daya ba to amman tana tsoron yadda zata kaya tsakanin su da Xieey wata zuciyar tace to ba ga Hafsatou ba ai zata tsare miki koma miye, wata Zuciar ta sake fadin to tare zaku zauna kenan idan kinyi auren ai itama komawa garinsu zatayi tayi nata auren nan hankalinta ya dan tashi tunawa da tayi cewar ba gari daya ma suke ba ynx ya zatayi? Can wata shawarar ta fado mata to ki roki Yaya Mus'ab mana ya aureku tare ba shikenan ba kuyi zamanku gida daya 

Murmushi tayi jin shawarar da zuciyarta ta bata ta mike tana fadin "Ummi bari in shirya kar Yaya ya fito"

Ummi ta bita da kallo tana jinjina sanyin hali irin na diyar ta a ranta tace ko ya zata kaya idan dukkanin su suka fahimci Auta yana son Hafsatou oho  fatan ta dai Allah ya kawo musu abin cikin sauki domin tasan tabbas sai ya furta....

Hey wattieeys! To ya kuka ga chappyn yayi kuwa after a long kwanaki without posting?

Ina jiran Comments dinku sbd fast update tomorrow kunsan yabawar ku ita ce kwarin guiwa na

Pls Vote and Comment line by line....Luv ya all..!

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now