10

198 21 8
                                    

Sai la'asar suka tashi daga nan sukayi wanka da sallah suna kan wanke² su Yarima suka shigo niki² da kaya a hanunsu Hafsa ce tayi saurin dauraye hanunta taje ta amshi kayan dake hanun Yaya Sadiq tana cewa "sannun ku da zuwa Yaya"

Ya dago ido suka kalli juna tuni yaji wani abu na motsi cikin zuciarsa ita kuma da sauri tayi kasa da kanta ta shige falo da kayan ta koma wajen da suke aiki Mami kam tuni ta dauraye nata hanun tabi bayansu tana raba ido

Sadiq da ya gama fahimtar inda ta dosa yaki ko kallon ta Ammi itama da ta fahimce ta tace "Wuce kije ki tayata ku karisa tun dazu ita ke ta aiki banda shirme ba abinda kk iya"

"Kwadayayya" cewar Sadiq

Tana dan turo baki ta fita har Hafsa ta gama tana share wajen suka dawo dakin suka zauna Yarima ne ya jawo ledar ya mika mata "ke lallai Blacky akwai kwadayi in ba baki akayi ba babu zaman lfy"

Da sauri ta karba "eh dai naji" ta ciro roba daya ta mika ma Hafsa "Besty Ungo naki"

Ta amsa amman ta kasa sha don duk dago idanu sai taga Sadiq yana kallon ta nan ta kasa sakewa a wajen Ammi da ta lura sai ta shiga daki ta kira Sadiq ya zauna kusa da ita

"Ammi na ba dai laifi nayi ba koh?"

Tace "a'a naga dai ka tsare 'yar mutane da ido ne ta kasa sakewa"

Ya dan sosa Kai cikin jin kunya "to Ammi ni yaushe na ke kallon mata balle wannan Karamar yarinyar"

Jan kunnensa tayi "zaka ma fadi gaskia ne"

Sai kusan biyar na yamma suka Kama hanyar Bauchi yayin da Yarima da Sadiq abota mai karfi ta shiga tsakanin su da alkawarin Sadiq zaixo Bauchi kwanan nan Mami har da kukan ta Hafsa ma ji tayi kamar kada tabar gidan don sosai take kaunar ahalin Bestyn nata

Suna isa gida suka fara shirya kayansu kuwa Ummi tasha lbrn Gombe sosai

Washe gari Sunday suka koma Schl suka bar Ummi cike da kewar su

Haka suka cigaba da rayuwa a Schl komi da Yarima sukeyi babu ruwansu yayinda Xee sam ta fita harkar su duk da cewa tanajin haushin yadda yake nan² dasu amman Saudat ta bata shawaran cewa ta gwada basa gabanta tunda har Daddy ya tabbatar mata Yarima Mijinta ne

Shakuwa ne ko kuma ince soyayya mai karfi ya shiga tsakanin Mami da Yarima ita kam Hafsa tana ankare da duk wani motsin su ita daman ba son shi take ba balle tayi kishi sedai ta amince da aurensa ne kawai don biyayya kuma tasan shima hakan take a wajensa

3rdterm yazo sauran students sun fara Exams su kuma SS3 aka basu hutun 2 weeks kafin su fara WAEC

Ranar da sukayi Hutu Sadiq ne yaxo tafiya da Mami suna tare da Yarima har Mami suka fito da kayansu kamar hadin baki Yarima ya nufi Mami ya karbi akwatin ta shima Sadiq ya nufi wajen Hafsa ita dai kanta na kasa don sam bata son kallonsa gabanta faduwa yake sosai in suka hada ido mika hanu yayi ya riko akwatin da hanzari ta sakar mishi ta matsa gefe yy murmushi dan y lura kamar tsoronsa take ya bude motar Yarima ya saka mata sukayi sallama tare da rugume juna ita da Mami suma mazan hakan sukayi kafin kowa ya shiga motarsa suka bar Schl din...

Yau satin su guda Mami tana kwance duk kewar Mus'ab ya dameta ynx kam ta gama tabbatar da cewa son shi ya gama mata babban kamu domin 'yan kwanakin nan da bata ganinsa duk hankalin ta ya tashi Ammi tayi tmbyr duniyan nan tace babu komi da ta damu sai tace ciwon kai take a dole tasa tasha magani duk da lfyrta lau

Yau ma tana kwance abin ya damu Ammi ta kira Sadiq cewar yaxo y kaita asibiti ya shigo yana amsa waya sai dariya yake
  "Prince zan kira ka anjima bari in Kai Baby asibiti"

Jin an ambaci Prince tayi zumbur ta tashi zaune shi kanshi Sadiq saida ya bita da kallo

Daga daya bangaren kuma Yarima hankali tashe yake tmbyr Sadiq me ya sameta coz yasan ita Sadiq ke kira Baby

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now