JAWAAD part 1-2

7.1K 304 4
                                    

_*JAWAAD*_🌷

_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

_*PAGE 1~2*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

K'auyen DOSO Niger...,",
Gudu take sosai yayinda wani mayunwacin Zaki kebin bayanta, gudu take tamkar zata tashi sama saboda tsananin tashin hankalinda take ciki wanda yasaka sam batamasan hanyarda take biba kawai gudun take domin ta tsere da rayuwarta,, azuciyarta kuwa Addu'oi ne barkatai takeyi naneman kariya ga ubangiji kada wannan mayunwacin zakin kar yai nasara akanta,,,,.

Tafiya suke akan doki su uku kyawawan matasan samari biyun yan kimanin shekara 23 sai d'ayan kuma dake gabansu d'an shekara 27,, suna cikin tafiya sai nagabansu d'in yamasu alama da hanu sudakata su tsaya, umarninsa kuwa sukabi suka tsayarda dawakinsu cakk shikuma yasakko daga kan nasa dokin sannan yaciro kibiya da mashi waenda ke a bayansa tareda takobi mai kaifin gaske, ahankali yafara tafiya yana zagaya dajin yana dube dube kaman dai yanda mafarauta keyi idan suna fataruta,,,gefenda yakejin kukan zakin yabi yana tafiya ahankali yana dube duben inda zai hangonsa cikin sa'akuwa yana juyawa gefensa na dama sai yahangota tana gudu tamkar zata tashi sama shikuma Zakin yana bin bayanta saurama k'iris yacimmata,,,,,..

Kibiyardake ahannunsa yaciro dasauri yasaitata dai d'ai wuyansa sannan yacira sama dak'arfi yaharba masa ita tareda bin bayansa dagudu, bata kaiga wuyansaba amma tasameshi a k'afa hakan yasa yai wata iriyar k'ara mai sautin gaske wacca tasaka dik wata halitta dake cikin dajin tashin hankali sannan kowacce tagudu domin ta buya kar tarasa ranta kona y'ay'anta,,,,,kibiyar tashigesa sosai hakan yasa yad'an rage gudun ammafa bai dainaba yayinda itakuma tacigaba da gudun tana shesheka, dikda tagaji sosai amma takasa tsayawa saboda dikta waigo saita gansa baidaina bintaba,,,,..

Wata kibiyar yasake cirowa yana gudun yasaita sannan yaharbamasa sai a cikinsa ganin haka yasa yasake ciro wata yaharbamasa takai a wuyansa,, Zakin akwaishi da wayo GA nacin tsiya dik abinda yasaka a gabansa to lallai saiyaci nasara agareshi, ganin jikinsa yafara rauni kaman zai rasata yasa yacira sama zai damk'ota nan shikuma matashin shima yacira yasha gabansa yaciro takobinsa dake a bayansa ya yanka masa ita a wuya sannan yasaka d'ayan hannunsa yarik'o yarinyar yai sama da'ita sannan yawurgata gefe d'aya yacigaba da fad'a da zakin yayinda take k'ara yankamasa takobin shikuma zakin ke k'ok'ari damk'osa yakai bakinsa, haka sukacigaba da gobzawa har yacinasarar kaishi k'asa saidai dikya yayyakuceshi da fartunansa masu shegen kaifi kaman takobi,,,,,..

Yarinyarkuwa tinda yawurgata gefe tasamu dakyar tamik'e a tsaye tab'uya a gefen bishiya tana kallon yanda suka gwabza dakuma yanda matashin yanuna jarumta da salo daban daban nanuna tsintsar Jarumtaka a fili,, ganin yakaisa k'asa ba'alamun zai iya tashi yasa tafito daga maboyarta tana tafiya ahankali tana d'ingishi ta'iso gunsa tai tsaye tana kallonsa yana goge jininda yazuba a jikinsa, juyowa yai yakalleta fuskarsa d'aukeda tsintsar b'acin rai yace "ke wace irin mahaukaciya ce mara hankali meyakawoki wannan dajin wato ku y'an gayunnan masu kud'i gani kuke komai kukayi dai dai ne toh shikenan ai dama nakyaleshi yacinyeki watakil yazama EZNAH gasauran masu hali irin naku" shuru tai tana sauraronsa takasa cewa komai takafesa da dara daran idanuwanta tana kallonsa har yagama fad'an nasa,, sauran waenda yake taredasu ne suka iso gunsu sannan suka sakko daga kan dawakinsu suna dariya suna masa kirari "saikai Namijin zaki yayan Rasheed da Rumaisa sha lelen Ummi" murmushi yai saboda akodayaushe sukamasa wannan kirarin koda yanacikin damuwa nantake zaiji dikkanin damuwarsa takau,,, d'aya daga cikinsu ne wanda ake kira da Majeed yace "ai tinda mukaji shuru mukasan kana nan kana aikin naka ashe yauma babban aiki kai tabbas kacika JARUMI Namijin Zaki kuma Namijin duniya natabbata idan sarki yaji wannan abun dakai nakashe wannan tsohon mafitinin zakin daya dad'e yana addabar mutanen wannan yankin Zaiji da'di kuma zakasamu kyauta mai tsoka dakuma k'arin girma",,,,,

Murmushi yai batareda yace komaiba yakamo dokinsa yagyaramasa silkensa sannan yajuyo gareta yace "zakibiyomune kokuwa...?" yafad'a cikin sigar tambaya, d'aga masa kai tai alamar Eh saikuma tace "amma dan Allah kutayani neman 'yan uwana banikadai bace nazo mu uku ne firgici da tashin hankali yasa muka raba hanya dasu" tafad'a muryanta rawa kwallah nabin kuncenta,, wani irin kallo yamata sannan yace "wato rainin hankalin naku har haka yakaiku kukawo kanku da kanku inda za'arabaku da rayukanku lallai wallahi dama Zakinnan yacinyeku gobe naga wata wacca zatasake zowa" itadai tai tsitt tana kallonsa,, takowa yai yazo gunta yakai hannayensa yarik'o k'ugunta tareda juya fuskarsa a gefe saboda kayan dake jikinta bawasu masu rufe tsiraici bane wando ne Jean dark blue da t-shirt fara wacca idan tad'aga hannayenta sama to zaka hango cibiyarta kanta kuma ba mayafi sumarta dikta barbaje ta wawwatse ko'ina watakil wajen gudun ne mayafin ya fad'i shikuwa ba abunda yatsana kaman yaga tsiraicin mace,,, alokacinda yarik'a k'ugunta kuwa saida yaji wani shook ajikinsa sannan yaji wani abu na ratsashi, dakyar yadaure yad'auketa cakk yad'ora kan dokin sannan shima yahau,,, dik lungu da sak'o NA dajin saida suka shiga amma bako d'ayansu wanda suka gani danhaka tahak'ura suka fita dajin...


#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊

JAWAADWhere stories live. Discover now