_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Aslm masoyan JAWAAD ina mik'a d'inbin godiya agareku nagode nagode sosai Allah yabar k'auna inajin dad'in yanda kuke nuna k'aunarku ga wannan littafen kusani kuma kuk'ara sani ana kyawon tare*_😍
_*Wannan page d'in kyauta ne ga mom sayeed and noor, juwairiyya adam Mrs muvarak and sis Aysha matazu, JAWAAD FAN'S CLUB and PRINCE MALEEK FAN'S CLUB kusani ina yinku sosai one luv*_💋_*PAGE 45~46*_
🌷 *END*🌷
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Zuwairat takusa kai 1hour tana bacci sannan ta tashi koda ta tashi kuwa bobbs d'inta sun cicciko da ruwa har sunamata zafi nan taje gun momy tasanar da'ita sai akabata babyn tafara shayardaita, tana kafamata maman abaki dasauri tak'arba tafara tsotsa, zafi tadingaji amma haka tadaure har tasha tak'oshi nantake bacci yad'auketa zuwairat tasauke nannauyan numfashi na jin dad'i,,...
Tsabagen tashin hankali yasa JAWAAD yamanta da bullet d'indake cikin hanunsa saida zafinsa yacigaba da damunsa gakuma damuwa suka tattaru acikin zuciyarsa, yatashi zai Mike a tsaye sai kawai yafad'i koda aka daukesa hanun yafashe yana zubda jini dasauri aka wuce dashi hospital,,...
Suna isa kai tsaye akawuce dashi theater room cikin gaggawa akamasa operation aka cire bullet d'in sannan aka fito dashi d'akin hutu,,...
******
Haka zuwairat tacigaba da shayarda baby har akai kwana uku aka gama zaman makoki kowa yawatse yarage sai y'an gida kawai,,...
Sati d'aya darasuwar ZULAIHERT police sukazo daga Court aka turosu suka tafi da dady aranarda aka tafi dashi aranar aka saka k'ara y'an human right ne suka saka sunce dole sai ankwatarwa ZULAIHERT hak'k'inta,,...
Kwana uku da saka k'ara akafara Shari'a, saida akai zama uku ana ukun ne aka yanke hukuncin,, amatsayin dady na chief Justice kuma aka kamashi da wannan laifin wanda acikin kundin dokar k'asa ba inda akace dole dole sai y'a tayi karatun zamani mai zurfi sannan uba zai aurardaita ba sannan dik macenda takai shekara 18 to tamallaki hankalin kanta kuma zataiya zab'awa kanta mijinda takeso a aura mata danhaka kotu ta yankewa dady hukuncin zaman gidan kaso na shekara 18 da tarar naira dubu dari takwas sannan saiyabiya diyyar ZULAIHERT,,...
Asakamakonda kotu tai tagano cewa wannan ba shine karo na farko da y'an dabannan suka tab'ayin kisa ba kuma wanda ya harbi JAWAAD a hanu shine ya harbi ZULAIHERT harta mutu danhaka kotu ta yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya,,...
To reader's kunji karshen waennan y'an daban dakuma hukuncin dady Allah yak'ara shiryamana zuriyarmu baki d'ai ya karemu da sharrin bin zuciya ameen.
Bayan angama yanke hukunci mai shari'a yatashi yafita sannan kowa yatashi police sukazo suka rik'a dady izuwa gidan kaso nan yarok'i alfarmar abashi 10mnts ba'a masa musuba akabashi,,...
Gunsu momy yazo yafara rok'ansu yafiya da afuwa, daga momy harsu zuwairat kuka suke dikda yanda sukejin takaici da haushinsa amma saida sukaji tausayinsa acikin zuciyoyinsu, bayan yagama dasu yaje gun y'an uwansa suma yarok'esu gafara daganan akawuce dashi izuwa gidan kaso,,...
Bayan angama komai su momy suka dawo gida kowa jikinsa a mace a kasalance,,...
Kimanin watan JAWAAD d'aya a hospital yana jinya sannan yasamu sauk'i suka sallamesa domin yaje gida yacigaba da jinya,,...
Zaune yake acikin parlor akan 2seater yana rungume da baby momy da zuwairat suna a gefensa, momy ce takallesa tace "JAWAAD yakamata karad'awa baby suna kaga har yanzu munrasa wanne suna zamu kira kowa sai baby yake cewa" shuru yai nawasu y'an dak'ik'u can sannan yad'ago ahankali yace,,..