JAWAAD part 21-22

1.8K 134 0
                                    

_*JAWAAD*_🌷

_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

_*PAGE 21~22*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Haka rayuwa tacigaba da tafiyarmata cikin k'unci da zafin zuciya, zaune take acikin Library tana karatun wani littafe wanda daka ganta kasan ba karatunsa takeyiba kawai tadorashi ne,,...

Wata y'ar k'awartace wacca sukaje dajin DOSO atare tazo tadafata nan tamotsa a firgice dataga Amina ce k'awarta saita tai tsaki tareda sauke wani nannauyan numfashi,,..

Wani kallon mamaki Amina tamata tana murmushi tace "ohh..!!! sorry nakatsemaki jin dad'inki kina tinanin habibtyn ki nakatsemaki koh" tai maganar cikin tsokana, murmushi kawai tai azuciyarta tace "wallahi kamar kinsani kuwa" amma a fili sai tace "Amina yadai" umm dama wanine yazo yana nemanki tareda wata y'ar budurwa amma daga ganinsu larabawane dan gyai d'in yahad'u wallahi k'awata kuma yace ke suke nema dan harda full name naki suka fad'i...." ai batako k'arasa zancenba ta tashi dasauri tasaka takalmanta tad'auki jakarta da phone nata tafita da gudu,,,..

Tana fita kuwa tahangosu tsaye a bakin wata bishiya rumaisa sai kalle kalle take, ahankali tak'arasa kusa dasu taredayimasu sallama cikin wata iriyar murya mai taushi, ahankali yajuyo tareda amsa sallamarta saboda tin bai juyoba yagane zazzak'ar muryarta mai taushi rumaisa kuwa tana waigowa taganta tazo da sauri tarungumeta tana dariya itama d'in murmushi takeyi na mamaki dan bata tab'a zaton JAWAAD zaidawo izuwa garetaba,,,..

Har yafara mata magana ta ban hak'uri saitaga sam baidace suyi zancen anan cikin filin School d'inba danhaka tajasu sukaje gunda suke shak'atawa suke karatu, bayan sunje nan yabata hak'uri sosai akan abunda yamata tai murmushi tace bakomai ai dama bata rik'eshiba tasan rashin sanine yasa yaimata hakan,,...

Rumaisa kuwa cewa tai "wallahi ni dama can nasan bahaka bane sam bakida wannan halayyar" murmushi kawai tai batace komaiba,,,, kallonta JAWAAD yai sannan yace "ZULAIHERT inaso nasan cikakken labarinki saboda shak'uwarmu dake tai zurfi yakamata musan cikakken labarinki a wancan lokacin kin fadamana koke wacece amma bamusan sauran abubuwa akankiba waenda sune muhimmai" murmushi tai tace "naji dad'i dakanema dakanka kasan cikakken labarina yanzu kuma zaka sani",,..

"sunana ZULAIHERT SA'AD MAINASARA ni y'a ce ga chief Justice Sa'ad mainasara shugaban lauyoyin Nigeria da doctor Amina Umar fana likitar mata da k'ananun yara a federal medical centre dake k'asar kebbi, nice first born nasu inada k'anne biyu zuwairat da zayyan, mahaifinmu yakasance mutum mai tsattsauran raayi kuma mutum ne wanda yafiye san kansa dayawa, burinsa shine muyi karatu mai zirfi saidai mukuma bamuda wannan burin burinmu shine muyi aure, tin da muka kammala secondry mukaso yamana aure amma yak'i dikda kuwa munada masoya sosai, ni yace zai had'ani da d'an k'anensa aure amma sai bayan nakammala karatuna,, yakan kashe ko nawane indai akan karatunmune amma dazaran munmasa maganar yamana aure ko dukanmu zaiyi gashi nikuma Allah ya halicceni da matsananciyar sha'awa tinda girma yakamani nake fama da ita, inamatuk'ar shan wuya marana kaman ya fashe amma mahaifinmu yakafe yace bamu ba aure saimungama karatu" tana kawowa nan kuka yakwace mata tai shuru saida ta tsagaita sannan tacigaba,,,,...

"ina matuk'ar shan wahala amma har yanzu yak'i ya janye burinsa agaremu, lokacinda kaganni tareda sumy baby a k'ungiyarsu wallahi sam bansan can zatakainiba ta tab'a yiman tayin shiga k'ungiyar amma nak'i nacemata bazan shigaba shine takaini danufin ko zanji sha'awar harkan nashiga amma dikda haka nak'i, naso katsaya namaka cikakken bayani amma lokacin idonka yarufe kak'i saidai banga laifinkaba saboda dik d'an uwa nagari yanaso yaga d'an uwansa yayi kyakkyawar rayuwa" yak'ara maganar cikin murmushi tareda zubda kwallah sannan tace "to kaji cikakken labarina" hmm....!!! ya sauke nannauyan ajiyan zuciya yai shuru batareda yace komaiba yakuma duk'arda kansa,,,...

Shuru yaratsa wajen nawasu mintina can yad'ago a hankali cikin murya mai taushi yace mata "hak'ika nayi bahagon tinani akanki kuma ban kyauta makiba danakiraki da y'ar lesbian amma dan Allah ki yafeman rashin sanine" murmushi tai tace "ai nasani bakomai wallahi abunda kamun kafi k'arfin narikeka a zuciyana da wata manufa bakomai Allah i yafemana baki d'ai" yace ameen sannan yace "saikuma magana tabiyu" dikansu ita da rumaisa d'agowa sukayi suka zubamasa dara daran idanuwansu suna sauraranshi, murmushi yai sannan yace,,..

"ZULAIHERT shin zaki iya aure na.....??",,..

Un expected taji tambayar tasa nan takafesa da ido cikin tsintsar mamaki can kuma ta duk'arda kanta k'asa tareda cusashi a tsakanin k'afafunta tarufe fuskarta da cinyoyinta sannan tace "yes... I will" dagashi har rumaisa wani irin k'ayataccen murmushi sukai alokaci d'aya sai yace "to Alhmdllh naji dad'i sosai saidai ZULAIHERT inaso kisani ni talakane maraya wanda saiyaje yanemo sannan ake d'ora tukunya agidansa ban maki alk'awarin zan baki dad'i kamar yanda akemaki a gidan iyayenki ba saboda banida zarafin hakan amma dai namaki alkawarin cikakkiyar soyayya wacca take had'e da cikakkiyar kulawa kuma zan kula dake iya k'arfina inafatar zaki zauna dani adik halinda rayuwa takasance mana",,...

Ahankali tad'ago fuskarta sannan tace "insha Allah namaka alkawarin zama tareda kai har k'arshen rayuwata saidai inaso kayi hak'uri ka daure kayi juriya da halinda zamu shiga idan mahaifina yaji cewa nayi aure saboda nasan halinsa kuma dan Allah inaso ayi wannan auren acikin sirri ma'ana AUREN SIRRI kenan har izuwa lokacinda yadace ya bayyana kowa yasani" murmushi yai yace "insha Allah namaki alk'awarin ba wanda zai sani har sai lokacinda kike so yazo" nan dai suka tattauna yanda abun zai kasance sannan suka tafi,,,...

Suna isa gida kuwa yafadawa ummi dik yanda sukayi, ummi tanuna jin dad'inta sosai kuma tasaka masu albarka sosai,,, bayan kwana hud'u dafaruwar wannan abun ranar juma'ah bayan anyi sallar juma'ah aka d'aura auren MUHAMMAD JAWAAD MUBASHIR da ZULAIHERT SA'AD MAINASARA akan sadaki naira dubu talatin a kud'in mu na nan gida Nigeria, masha Allah ubangiji yasanya aurenku albarka ameen...

🤔 Hmm tbd jam wato AUREN SIRRI 2 kenan akwai cakwakiya lallai ZULAIHERT bakima tsoron dadyn ki yaji zakiyi aure batareda saninsa ba to ko Amir zaibar JAWAAD ahaka batareda yad'auki fansar abunda yamasa ba 🤔 oho alamar tambaya?? tafito kuma dole abada amsarta, to muje dai zuwa reader's 💃🤸‍♀ domin samun amsoshin waennan tambayoyin ammafa sainaji daga bakinku 🤕

👇


#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊

JAWAADWhere stories live. Discover now