JAWAAD part 11-12

1.8K 123 2
                                    

_*JAWAAD*_🌷

_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

  _*PAGE 11~12*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Kwantawa tai kan gadonta ta rintse idanuwanta tana zubda zafafan kwallah tarasa meke mata dad'i a duniya karatun dik yafitar mata a rai,,,..

Jin bud'ewar k'ofar shigowa datai yasa ta tashi domin ganin mai shigowar, ahankali tak'araso tana murmushi tazauna kusa da'ita sannan tace "k'awata lafiya dai wai meke damunki ne 2days dinnan naga bakya cikin nishad'i pleace tell me what's happened" tasowa tai daga kwancenda take sannan tashare kwallandake zubomata,.

Kallonta tai da dara daran idanuwanta dasuka kade suka sauya launi izuwa ja saboda kukanda tai tace,

"k'awata nakasa fad'amaki damuwata na b'oyemaki saboda tinanin zata kawar nan kusa saidai har yanzu nakasa kauda ita nakasa maganceta hakan yasa dole yanzu nafad'amaki ko zaki taimakaman na magance matsalar tawa" kallonta tai cikin rashin fahimta tace,.

K'awata meke damunki fad'aman naji dan Allah ko zuciyata zata samu nutsuwa. Shuru tai nawasu y'an mintina can sannan tanisa tajuyo tana fuskantarta sannan tafad'amata komai ba abunda ta b'oyemata,...

Dariya taga ta kyalkyale da'ita saida tai mai isarta sannan ta tsagaita tace "kai wallahi k'awata kin bani dariya dama akan wannan abunne kike damarda kanki harda saka kanki cikin damuwa dik kin rame kin lallace kinfita hayyacinki" kallon banganeba me kike nufi kenan tamata ganin haka yasa tasake dafa kafad'arta sannan tace,,,,,,,,.

Indai akan wannan abunne kike damarda kanki to kidaina dan inada maganin matsalar taki. Sam bata fahimci abunda take nufiba hakan yasa tace "Sumayya sam ban fahimci abunda kike nufiba pleace kifitardani duhu" murmushi tai sannan tamatso ta duk'o da kanta dai dai fuskarta sannan tace,.

"munada wata k'ungiya ta maza da mata inda ake magance irin wannan matsalar taki ana kiran k'ungiyar da FETIR KO GAS ma'ana maza ko mata dik wanda kike buk'atar yamagance maki matsalarki acikinsu nan take cikin y'an mintina k'alilan zai magance maki ita batareda kin biya ko sisiba" matsawa tai da sauri daga kusa da'ita cikin tsintsar b'acin rai tace,,.

"subhanallah,  waiyazubillah,  innalillahi wainna ilaihi raji'un Sumayya kardai kiceman ke y'ar lesbians ce" tai maganar cikin tuhuma, shan kunu tai tace "eh to kusan hakan ne kinga ZULAIHERT wallahi zakiji dad'in k'ungiyar sosai ai yanzu yanda iyaye sukazama y'an BOKO nasara suka bud'e masu ido da rayuwa sukace lallai dole sai munyi ilimin zamani sannan zasumana aure shiyasa muma muka daina wahalarda kanmu muka had'u muka bud'a k'ungiyar saboda mudaina shan wuya da wahalar sha'awa tsohuwar k'ungiya ce kishiga zakiji dad'in ta sosai wallahi" wata iriyar tsawa tadaka mata tareda dakatar da'ita sannan tanunamata k'ofar fita alamar tafita,,..

Wani irin kallo tamata sannan tamik'e tsaye saboda tasan halin ZULAIHERT takama hanyar fita, har takai k'ofar zata fita saikuma ta juyo tace "akodayaushe a shirye nake domin karb'an bak'untarki izuwa cikin k'ungiyar mu" tasowa ZULAIHERT tai danufin tarufeta da duka aikwa batasan lokacinda tafita dagudu ba tabar dak'in nan tai tsaye tana mayarda numfashi cikin masifa,,..

Dawowa tai tazauna kan gadonta taduk'arda kanta k'asa tana tir da halin sumayya ashe dama wannan bakar d'abiar ce takeyi shiyasa take ganin tana fita School tayi har kwana hud'u bata dawoba hmm Allah yakiyaye nikam sam bazan karb'i gayyatarkuba ubangiji yamin maganin matsalata,.

Haka taita tinanin zantukan sumayya dake mata zarya a kunnayenta wata zuciyar nace mata kawai taje tashiga k'ungiyar ai bakomai bane zataji dad'i kuma matsalarta zata kau, wata zuciyar kuma gargad'inta takeyi akan tai gaggawar kawarda wannan zancen tayi watsi da wannan zancen, haka tawuni ranar jikinta ba kwari har dare, da dare tashirya taje restaurant taci abinci saboda bazata iyayin girkiba,,..

         *******

Washe gari tin 10:00am k'anwarta zuwairat ta'iso koda ta'iso tana kwance sanye da kayan bacci ko wanka bataiba, dasauri tarungumeta tafashe da sabon kuka dakyar tasamu ta rarrasheta tatsaigata da kukan sannan tagyara zamanta suna fuskantar juna tace,.

"yayata yakamata muyi maganin wannan matsalar tin da wuri kar tai nisa mukasa maganinta" cikin muryar kuka tace "to zuwairat miye mafita yanzu" shuru tai tareda sauke nannauyan numfashi sannan tace "dady yadawo yana gida muje mutinkareshi mucire kunya da tsoro mumasa magana akan yayi hak'uri muyi aurenmu bayan munyi sannan mucigaba da karatunmu idan akai haka zamufi samun nutsuwar yin karatun cikin kwanciyar hankali",.

Hmm....!!! tanumfasa sannan tace "kekinfi kowa sanin halin dady baya magana biyu d'aya yakeyi kozatai dad'i ko bazatai dad'i ba dik wannan ba damuwarsa bace amma tinda kice haka shikenan muje d'in Allah yasa mudace ya'amince" tai murmushi tace "yawwa yaya haka nakeso naji kince oya to tashi kishirya muwuce zuwa jibi sai mu dawo saboda inada lecture kema kuma nasan haka" murmushi kawai tai ta tashi tafara shiri,.

Cikin sauri tashirya tai wanka tasauya kaya sannan suka fita, kai tsaye airport suka nufa cikin sa'a kuwa suka masu jirgi d'aya yarage nan akamasu komai 3:00pm dot jirginsu yad'aga izuwa Nigeria.


#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''
  *I.W.A*🖊

JAWAADWhere stories live. Discover now