_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 15~16*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Bayan wasu y'an kwanaki taji sauk'in abunda ke damunta saboda addu'oinda takeyi safe da yamma idanma batada lecture har rana tanayi hakan yasa tad'an rage yawan tinani kuma sha'awar tadaina jinta kamar da, karatunta yacigaba da tafiya dai dai inda take mayarda hankali sosai saidai har yanzu batajin dad'insa yinsa kawai take kamar a tilas,,,,...
***** *****
Zaune yake acikin wani daji yana gasa b'era daya kama abokanansa kuma suna daga gefe suna a kwance sunashan iska, bayan yagama yace "majeed zo kad'auka kuci idan mungama kuma zamu tafi dajin Kalkawi domin yin farautar naman gidan sarki" to Jarumi bara muyi sauri mugama sai mutafi. Nan suka ci naman bayan sungama sannan sukahau dawakinsu suka wuce,,,...
Bayan sungama farautar sai suka wuce fada suka kai naman a hanyarsu ta fitowa sukai kicib'is da Amir zai shigo tareda hadimansa, wani irin kallo yawatsawa JAWAAD sannan yai tsaye tareda dakatarda JAWAAD nan ya tsaya cakk yasha kunu yamurtuke fuska kamar baitab'a dariya ba yana kallonsa,,,..
Dik irin wulak'ancinda yatattaro domin yamasa yana had'a ido dashi saiyaji JAWAAD yamasa wani irin kwarjini a fuska, ganin yanda yatsuke fuska yasa nan take yasha jinin jikinsa dakyar yace "kai nizakayiwa k'arya koh kai wai me kake d'aukan kankane kaida kake talakana bawana wanda idan naga dama zan iya mayardashi hadimine amma saboda tsabar raini zaka dubeni kaman k'arya",..
Ahankali JAWAAD yad'ago da idanuwansa yawatsa masa wani irin kallo wanda saida hantar cikin Amir ta motsa sannan yace "wace irin k'arya namaka...?" matsawa yai daga kusa dashi saboda tsaro hhhh Lol, yakallesa sannan yace "wannan yarinyar data taka dokata naje zan hukuntata kaman k'arya kace matarka ce to nayi bincike nagano k'arya kake y'ar makaranta ce saboda haka dolene ka kawoman ita kokuma nanda gobe nasaka akawoman ita ko na aureta kokuma nayi...." sai yai shuru ya kyalkyale da dariya yana kallon hadimansa nan suma suka kyalkyale da dariyar, shidai JAWAAD sauraronsa kawai yake baice dashi k'ala ba su majeed kuwa dik sunsha kunu ji suke kamar sukasheshi,,,..
Sake juyowa yai yace "dole ayi abunda nace idan bahaka ba kuma wallahi naje har gidanku nacimmata nayi abunda nakeso da'ita sannan nafito inafatar kafahimci zancena talakan banza d'an shan miya" yana gama fadar haka yai saurin wucewa hadimansa suka bi bayansa,,,,,..
Naushi majeed yakaiwa iska cikin b'acin rai yace "haba JAWAAD meyasa wai kake hanamu d'aukan mataki akan wannan sha sha shan wanda baifi nasaka takobina ba nafille masa kai" wani irin murmushi JAWAAD yai sannan yace "kushare dashi kubarni dashi kawai ni zanyi maganinsa dakaina kuma wallahi dik abunda yayiwa yarinyar nan saina mugun sab'amasa saidai mubar k'auyen nan dan nasan dole akoremu idan nakasheshi" yana gamar fad'a haka yawuce suma sukabi bayansa suka fita,,,...
***** *****
Ganin tayi kwana biyu bataje gidansu JAWAAD ba karatu yahana yasa yau dai tashirya domin taje kasancewar yau weekend ne, wani wando da riga ne tasaka masu kyau wandon light blue sai riga fara mai k'aramin hanu tasaka ribom ta tufke sumarta sannan tad'akko wasu takalma hills masu tsini sosai tasaka sannan tafeshe jikinta da tirare mai sanyin k'amshi, bayan tagama tad'akko mayafi ta yafa sannan tad'auke wayarta tafita,,,..
Kai tsaye hanyar gidansu JAWAAD takama ita kad'ai tana tafiya ahankali, wani lungu tabi wanda zai sadata da layin gidansu JAWAAD tana cikin tafiya sai kawai taga mutun yafad'o daga kan gini ta gabanta, dasauri tafad'i kalmar a'uzubillah tareda ja da baya nan shikuma yafara kyalkyala dariya yana matsowa cikinta,,,...