_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 19~20*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Cikin sa'akuwa tana fita tasamu a dai daita sahu tahau saboda yanzu tsoro takeji bazata iya tafiya a k'asa ba kar Amir yasake tareta a lungu,,,...
Basuyi wata doguwar tafiya ba suka isa k'ofar gidan nan tasakko tabiya mai a dai daita sahu sannan takama hanyar shiga gidan,, cikin sallama tashiga tana murmushi kamar yanda tasaba, Ummi nadaga gefe tana d'ibo ruwa acikin rijiya tana ganin ZULAIHERT tai murmushi sannan tace "a,a y'ata ZULAIHERT kece a gidan namu yau" itama cikin murmushi tace "Eh ummi nice ina su Rumaisa da Rasheed zasu barki ki d'ibi ruwa dakanki" tai maganar tana karb'an gugar daga hanunta, dikda bata iya d'iban ruwa a rijiyaba amma haka ta k'ok'arta tad'ibarmata ruwan har tagama aikwa taita nishi kamar wacca tai tsere,,,...
Bayan tagama sukaje suka zauna nan ta tambayi ummi Rumaisa tacemata tana ciki, abun yafara bama ZULAIHERT mamaki yanda ummi tasaba mata idan tazo tana sakemata fuska tana mata fara'ah yau dik taga sab'anin hakan sannan Rumaisa nagidan kuma ba bacci takeyiba taji shigowarta amma batazo da gudu ta rungumetaba tanamata oyoyo kai tabbas akwai wani dayake faruwa wanda batasaniba,,,...
Tashi tai tashiga dak'in koda tashiga ta taddata kwance akan gado tana kuka, dasauri taje ta tadota tana tambayarta abunda yake faruwa, rungumeta Rumaisa tai tana kuka sannan tafad'amata abunda JAWAAD yace kuma yace yaraba alak'ardake tsakaninsu bayasan yasake ganinta tareda ita ko gidan kar ZULAIHERT tasake zuwa,, tsintsar tsoro da fargaba ne suka bayyana a fuskar ZULAIHERT nantake tatino da samarinda suka gani lokacinda zasu shiga cikin wajen fuskokinsu a rufe da wani abu bak'i to kenan hadda JAWAAD yana cikinsu wayyo Allah tashiga uku ashe kowa yaganta to yanzu yazatayi ta wanke kanta,,..
Kallon rumaisa tai cikin tashin hankali tace "rumaisa ina JAWAAD yake inaso namasa bayani ko zai fahimceni wallahi wallahi ni ba y'ar lesbian bace banida alak'ar komai da wannan k'ungiyar" janyo hanunta rumaisa tai cikin zubda kwallah tace "wallahi nasani k'awata na yarda dake wannan sam baiyi kama da halayyarkiba amma bara yaya yazo sai kimashi bayani",..
Hankalin ZULAIHERT yamatuk'ar tashi ba kadan ba gani take kamar kowama yaganta,, tashi sukai suka fito waje nan rumaisa tayiwa ummi bayanin komai itama ummin abunda rumaisa tafad'a shi tafad'a tace "wallahi nima y'ar nan ban yarda da hakanba shine dai JAWAAD kuma nacemashi yai bincike tukun..." batako rufe bakintaba saiga JAWAAD d'in yashigo tareda abokanansa, yana ganin ZULAIHERT nan take yab'ata fuska yasha kunu tamkar baitab'a dariya ba aikuwa ZULAIHERT naganin yanayinda fuskarsa ta sauya tsoronsa yamamaye zuciyarta tashiga fargaba da tashin hankali,,..
K'arasowa yai cikin b'acin rai idanuwansa suka kad'a suka sauya launi izuwa ja dak'arfi yanuna rumaisa da yatsa yace cikin d'agawar murya "ke mena fad'amaki eh nace mena fad'a maki ne" b'oyewa rumaisa tai a bayan ummi saboda sanin halin yayan nata idan yanacikin b'acin rai komai yana iya aikatawa sai daga baya yadawo cizan yatsa,, juyowa yai ga ZULAIHERT yanuna da yatsa sannan yacemata "ke daga yau daga yau karna k'ara ganinki tareda k'anwata karna k'ara ganinki a gidannan kije can kinemi irinki lalatacci amma anan kam bazaki tab'a cin nasaraba idan kuma kikak'i ji to bazaki k'i ganiba wallahi zan iya aikatamaki dik abunda zuciyata ta ayyana man saboda haka kifita daga gidannan yanzinnan",,,..
Hankalin ZULAIHERT yatashi matuk'a ita bama fad'anda yakemata ke damuntaba sharrinda yake mata a gaban mutane ne yake b'ata mata rai kuma har wai yana nisanta k'anwarsa da ita,, cikin b'acin rai idanuwanta na zubda kwallah tace "JAWAAD ka saurareni namaka bayani wallahi abunda kake tinani sam bahaka bane ni bana d'aya daga cikin y'an wannan k'ungiyar wallahi k'awatace ke ciki kuma sam bansan ita y'ar lesbian bace da bazan tab'a yarda nai abotaka da'ita ba kuma a ranar bansan can ne zata kainiba da ban yarda nabita ba dan Allah karka koreni daga gidanku wallahi banida burin na cutardak...." bata k'arasa abunda zata fad'a ba yajanyo hanunta yakama hanyar waje da'ita, rok'onsa take tana masa magiya tana fad'amasa ita bata d'aya daga cikin y'an wannan k'ungiyar amma ina zuciyarsa ta bushe ransa a bace yake haka yajata saida yakaita waje yai wurgi da'ita tafad'i k'asa yajanyo k'ofar gidan yarufe,,,...
Jefota da yai kanta yabugi wani dutse yafashe sai jini yadinga zuba, haka tasaka veal d'inta tadafe wajen sannan ta tashi tad'auki kayanta tawuce,,..
Yana dawowa gida yawuce d'akinsa yajanyo k'ofa yarufe, rumaisa kuka tadingayi tashige d'aki tafad'a kan gado tana rusa kuka hakama ummi ranta ya baci sosai amma saboda tasan halin d'an nata idan ransa ya baci bayajin rarrashi kuma basuda abunda zasuce akan wannan al'amarin saboda shi yanada tabbas yaganta kuma itama ta yarda da hakan saidai basuda tabbacin itadin bata cikin k'ungiyar, haka taita wannan tinanin cikin b'acin rai nandai itama tacigaba da aikin gaban amma badan tanajin dad'i ba,,,...
***** *****
Tinda wannan abun yafaru ZULAIHERT tak'ara shiga damuwa karatun yinsa kawai take amma badan tanajin dad'in rayuwartaba komai yacakud'emata wani lokacinma saitaji dama tamutu tahuta da wannan rayuwar datakeyi idan ta tina da JAWAAD sai taita kuka tana rokon ubangiji daya shiga lamarinta dan tinda tahad'u da JAWAAD taji sonsa yashiga acikin birnin zuciyarta amma yanzu gashi tarasashi shi da kansa yakoreta daga gareshi,, haka taketa zama cikin k'unci yanzu daga class Library sai hostel idan tagaji da zama kuma sai tafita waje tad'an mik'a kafa,,,..
Yauma kamar kullum kwance take akan gadonta tana juyi tana hard'e k'afafuwanta gu d'aya kamar maijin sanyi, addu'oi takeyi tana neman kariya daga ubangiji tana so tafi k'arfin shaid'an takoreshi daga zuciyarta,, dakyar tasamu tad'an rage jin masifaffiyar sha'awardake tasomata ta kwanta a rigingine idanuwanta na a rufe tana zubda kwallah,,,...
Wani tinanine yashigomata a zuciya, tindadai itama sumayya taurin kan mahaifintane yakaita ga shiga wannan halin to ai itama mahaifintane yahanata tai auri kuma gashi ana zarginta alhalin kuma ita batayi toshin meyasa bazata shigaba da zarginta da akeyi ai gwanda a zargeta da dalili, da wannan shan wuyar datakeyi na fama da wahalar sha'awa gwanda kawai tashiga kartaje tajiwa kanta ciwo mararta ta fashe,,, haka zuciyarta taita rayamata kawai tashiga k'ungiyar tinda dai mahaifinta bazai tab'a aurarda itaba har saitagama karatunta,,,...
Da wannan tinanin tagama yanke shawara saidai kuma takasa zuwa tasanarda sumayya ta amince da tayin shiga k'ungiyarsu da tai, to ko meyasa hakan oho,,'..
********
Kwance yake akan wata ya gaggiyar katifarsa yarufe idanuwansa amma ba bacci yakeba, tinda yakori ZULAIHERT yakasa samun nutsuwa da sukuna kullum cikin tinaninta yake yakasa fitardaita a ransa yanzu har yakaiga yana mafarkinta saidai abunda yabashi tsoro shine, a dik lokacinda yai mafarkinta yakan gantane acikin k'unci tana rek'onsa dayazo ya taimaketa wasu sunzo zasu jefata acikin wuta kokuma wasu halittu sun biyota zasu kamata, irin wannan mafarkin yaketayi saidai a yanzu kam yafara gasgata abunda zuciyarsa take fad'amasa tabbas son ZULAIHERT ne yakamsa hakan ne yasa yakasa cireta daga zuciuarsa kuma yakejin d'aci da zafin korarda yamata hakan ne kuma yasa yaketa mafarkinta watakil ma abunda yake zarginta dashi bahaka bane,,..Haka kusan kullum yaketa keb'e kansa yaita faman tinani farautanda ma yake zuwa yanzu yarage, tin ummi nakyalesa hartafa masa magana takasa gane kansa amma kuma data tambayeshi sai yacemata ba komai....
#/Vote
#/Share
#/Comment'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊