_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 33~34*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Kimanin kwananta biyar da dawowa tafara laulayi zazzafi mai tsanani ga amai ga zafin jiki gashi bata iya had'iye yawu saidai taita zubarwa saida momy tasaka aka d'ibo mata k'asa acikin wani mazubi sai tadinga zuba yawun aciki,,,...
Tak'ara fari sosai dukiyar fulaninta sun cicciko hips d'inta sun k'ara fitowa sosai, tanashan wuya saidai momy nakula da'ita sosai wani lokacin idan tai amai tawahala saitamata k'arin drip abinci kuma bakowanne takeci ba daga d'an malele sai kunun gyad'a kona aya kokuma lemo da ayba, haka take fama wani lokacin taita kuka saboda bata saba da shiga irin wannan yanayinba su zuwairat suita dariyanta sai momy takoresu,,..
Kwance take akan gado dak'in momy tana shan lemo tana waya da habibinta sai dariya take tana washe fararan hak'oranta, zuwairat ce tashigo tazauna gefenta,,,..
Tajima sosai tana waya dashi har zuwairat tafara gajiya saida tace "yaya kefa nake jira dan Allah wannan wayar taisa haka" wata iriyar harara tajefo mata sannan tajuya tacigaba da abunda take,,..
Zuwairat gajiya tai da jiranta ta tashi tana tsaki tawuce abunta,.
Yau koda ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzab'i ta tashi tin tana hak'uri harta kasa abun yafi k'arfin momy ga amai ga zafin jiki,.
Dadyn sune yashigo d'akinsu yana neman momy kwatsam ya tadda ZULAIHERT tana amai ashe momy tea taje hadomata na citta da Lipton,,..
Halinda take ciki yasa batama damu da dady yasan halinda take cikiba,,, cikin sauri yazo yad'agota yana fad'in "subhanallah baby dama bakida lafiya kuma ba'asanar daniba" itadai batace dashi komaiba har saida tagama aman yazubamata ruwa ta kuskure bakinta sannan yataimaka mata suka fito daga toilet d'in,..
Kan gado ta kwanta tarufe idanuwanta tana mayarda numfashi,,...
Momy ce tashigo tana sauri saboda tasan halinda tabarta,,, kamar a mafarki sai kawai taga dady a tsaye ya hard'e hannayensa yana zarya acikin d'akin, azahirin gaskiya tsoro ne da fargaba fal acikin zuciyarta amma a zahiri saita b'oye fargaban tace,,..
"a,a dadyn ZULAIHERT kaine aciki" juyowa yai sannan yace "eh nine wallahi nazo ina nemanki saina tadda baby na amai ashe batada lafiya shine baku fad'amanba kuma kinsan banasan hakan b'oye damuwa ko ciwo batareda an sanardaniba" Murmushi tai sannan tace "to dadyn ZULAIHERT naga bawani ciwo bane shiyasa ban sanardakaiba zazzab'i ne kawai kuma yanzu nakeson nahad'a injection namata idan tasha tea nabata magani tasha",,..
haryaso kaman yak'i yarda da hakan amma saitai yanda zatai da dabarunmu na mata takauda zancen saboda tasan zai iya cewa sai sunje hospital idan sukaje hospital kuma tabbas asirinsu zai iya tonuwa,,...
Saida yaga tamata injection d'in tabata magani tasha sannan yafita,, yana fita kuwa momy tasauke nannauyan numfashi sannan tazo ta zauna dai dai kanta tasaka hanunta tana shafa goshin ZULAIHERT,,..
Da marance ma bayan yadawo saida yashigo yaduba lafiyar ZULAIHERT cikin ikon Allah kuwa taji sauk'i sosai harma tana cin abinci nan yaita tsokanarta mai raki ta gaji raki agun gyatumarta nan sukaita dariya momy tace agun gyatuminta dai ta gada yana dariya yafita,,...
Alhmdllh cikin ZULAIHERT yafara kwari yanzu yacika wata biyu cif hakan yasa tad'an ji sauk'in wahalar laulayi saidai har yanzu dady yana kula da'ita kusan kullum saiya tambayi lafiyarta koda batajin dad'i nan take saita saki jikinta kamar bawani abunda ke damunta tacemasa ai ta tawarke,,..
Kimanin satinsu uku da dawowa suka fara shirin komawa School saboda momy tsoro take yanda dady yasakawa ZULAIHERT ido karsuje asirinsu ya tonu dan haka suka karb'i kud'i agunsa yakuma cikamasu account d'insu sannan sukaje sukayo shopping,,..
Zaune take acikin parlor suna kallon tashar zeeworld ita dasu zuwairat saiga zayyad yashigo suna ganinshi su zuwairat suka buga kuwa suna dariya zayyan yaje suka rungume juna suna farinciki da ganin d'an uwansu, k'arasowa yai yazuna suka gaidashi sunamasa barka da dawowa ya amsa cikin murmushi,,..
ZULAIHERT ce tace cikin murmushi "gaskiya yaya zayyad ka shammacemu wannan tafiyar bazata haka bako sanarwa bare muyi shirin tarban manya manyan bak'i" zuwairat ce tai saurin fad'in "kaji yaya kamar bakisan halin ya zayyad ba shi dama idan zaiyi tafiya bayasan kowa yasani hakama idan zai dawo saidai kawai agansa",,...
Dariya yai yace "am sorry my lovely sister's amun afuwa hakan bazata sake faruwa ba" murmushi kawai tai batasake cewa komaiba zuwairat ta tashi tashiga ciki tahad'o masa drink's takawo masa, yana cikin sha momy da dady suka sakko k'asa nan ya durk'usa yagaidasu momy tace,,..
"wato dai zayyad bazaka daina wannan tafiyar ta dare ba ko any time ina fad'a akan tafiyar dare amma bazaka dainaba kasani banasan irin wannan tafiyar wallahi amma bazaka dainaba" sosa kansa yafara kamar mak'aryaci yace "amun afuwa momy tuba nake insha Allah baza'a sakeba" hmm kudai kuka sani, dady ne yace "Son sannu da zuwa ya hanya" yace "Alhmdllh dady" daga nan suka wuce dinning area domin yin dinner,,...
Bayan sungama ZULAIHERT tawuce d'akinta domin ta kwanta saboda wani irin masifaffen bacci takeji, zayyad na ganintawuce shima yabi bayanta dady nakallonsa yai murmushi,,...
Kusan atare suka isa dak'in tana shiga ta zauna shima yak'araso ya zauna yana mata murmushi,,..
Hartai kamar zata sake masa fuska saikuma tatino da tanada fa auren wani akanta harma da cikinsa a jikinta nantake tasauya yanayin fuskarta tasha kunu, ganin haka yasa zayyad ransa ya baci amma saiya dake yai kamar baidamuba yace,,...
"My lovely sis ina muka kwana da zancenmu ina fatar dai har yanzu bawanda ya'isa yamaye gurbinda nake dashi acikin birnin zuciyarki" k'ara shan kunu tai sannan tace "kaga yaya ni yanzu wallahi bacci nakeji pleace kabar wannan zancen har gobe inaga zakafi samun cikakkiyar amsarka amma yanzu abunda zan fad'a maka zai iya b'ata maka rai yakuma sakaka acikin damuwa" tana gama fad'ar hakan tajuya takwanta abunta tareda janyo blanket ta lullub'e,,,...
Hakan data masa bak'aramin b'ata masa rai yaiba bakuma k'aramin bashi mamaki yaiyaba saboda a iya saninsa shi da ZULAIHERT suna son junansu to miye dalilinda yasa tamasa haka yanzu, bawanda zai iya bashi wannan amsar,.
Ganin tai kwanciyarta kuma batada niyyar tashi yasa dole yatashi yafita, yana fita tai tsaki tacigaba da baccinta,,...
Washe gari tin 5:00am suka shirya jira kawai driver's suzo domin sukaisu airport, koda zayyad ya tashi saiyaga suna shirin barin gida mamaki ne yacikashi saidai yakasayin magana yana kallo har driver's sukazo d'aukansu,,...
Ataredashi akai masu rakiya airport suka shiga jirgi suka wuce suna d'aga masu hanu har suka shige jirgi zuciyarsa namasa kuna tareda zigasa akan dole yagano abunda ke faruwa saboda wallahi yariga ya tsunduma kogin k'aunar ZULAIHERT dolene kuma ya aure ta,,..
Da tinanin abunda zaiyi kuma taina zai fara har jirginsu ZULAIHERT yad'aga yawuce izuwa k'asar Niger sukuma suka juya izuwa gida.....
Hmm 💃🤸♀wasa farin aiki lallai zayyad kana da babban aiki a gabanka dandai JAWAAD yamaka fintinkau tinda har ya mallaki gangar jikin ZULAIHERT dakuma zuciyarta 😜🏃♀to muje dai zuwa reader's
#/Vote
#/Share
#/Comment'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊