_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 43~44*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Zaro dara daran idanuwansa yai cikin tsananin mamaki dakuma tashin hankali, jinine yagani yana zuba a k'asa saidai baigane jinin waye ba,...
Dasauri yad'ago baby yaduba yaga banata bane yana d'ago ZULAIHERT saiyaga ashe jinintane ita suka harba, cikin tsananin firgici da tashin hankali yajuya gefe d'aya ya ajiye baby sannan yad'ago ZULAIHERT yana duba inda suka harbeta,,...
Hankalinsane yamugun tashi ganin inda suka harbeta mugun warine bakowa ake harba nanba yayi rayuwa a zuciyarta ne suka harbeta kuma bullet har yafito ta bayanta saboda bindigar shegiya ce AK ce mai tarwatsa brain,, cikin tsintsar tashin hankali yafara bubbugata yana fad'in "hubby na hubby na dama ke suka harba dan Allah kitashi kitashi ZULAIHERT karki mutu bara nakaiki asibiti" saiya d'aga da nufin yad'auketa wai yakaita asibiti saitai saurin rik'emasa hanu jini yana zuba a bakinta da hancinta dakuma kunnayenta,,...
Rik'e masa hanu tai ta dakatardashi tana shak'uwa jini yana zubarmata acikin zuciyarta dakuma bakinta da hancinta, kwallah yake zubarwa yarungumeta yana fad'in "ba abunda zai sameki hubby na bazaki mutuba bazaki tafi ki barmuba munanan atare har abada" yana cikin surutunsa sai yaji tana fad'ar kalimatusshahada,..
Dasauri ya d'agota yazubamata idanunsa yana kallonta zafafan kwallah nazuba daga idanuwansa yana kallonta dak'arfi tarik'o masa hanu tana maimaitawa tana fad'a, takai dai dai "wa'ash hadu annamuhammadarrasulull......" sai yaji tai shuru idanuwanta suka kafe tana kallon sama kwallahn k'arshe suka zubo mata a gefen ido d'aya, shine ya k'arasamata "rasululluh",,...
A razane a tsorace yad'ago hanunta yasake saiyaga yafad'i k'asa, rungumota yai da k'arfi tareda kiran sunanta cikin murya mai k'arfi "zulaihaaaatttt....!!!" saikuma ya fashe da kuka mai k'arfi abunda yakwashe shekaru masu yawa baiyiba kuka tin rasuwar Abban sa rabonsa daya zubda kwallah harya bud'e muryarsa yana irin wannan matsanancin kukan,,...
Matsanancin kuka yake yana zubda kwallah masu zafin gaske yana fad'in "ZULAIHERT karki tafi ki barni hubby na bazan iya rayuwa acikin wannan duniyar batareda ke ba duba kiga babyn mu sai kallonki take dan Allah karki barmu ZULAIHERT" haka yadingayi abun gwanin ban tausayi, ni kaina Ummi jawahir saida na zubda kwallah saboda tsananin tausayi.
Police d'inne sukazo d'aya ya d'auki baby biyu kuma suka kama domin su tada JAWAAD cikin tsananin tausayinsa sai yafizge yace "kubarni bazan iya tafiya ko'ina nabar hubby na ba" ogan sune yazo yadafa shoulder d'insa cikin tausayi yace,,,...
Yaro kasani dik abunda Allah yabamu nasane kuma badan baya sansaneba yabamu haka zalika dik abunda ya karb'a nasane ba namuba yafimu sonsa shiyasa dan haka ina mai baka hak'uri dakuma tayaka jimamin rashin matarka kayi hak'uri ka daure namiji dik inda yake ansanshi da dauriya ai ita mutuwarta abar alfaharice saboda tarasu tana anbaton kalimar shahada kaga kuwa ita saidai muyimata murna Allah yasa muma musamu irin nata rabon" dik abunda yake fad'a JAWAAD yai shuru yana saurarensa nan yakai hanunsa yataimakasa yatashi tsaye saboda dik jikinsa yamutu ba kwari,,...
Nan take ogan yakira acan headquarter tasu aka turo motoci aka d'auki y'an daban akasaka sannan aka d'auki gawar ZULAIHERT aka saka a mota d'aya tareda JAWAAD yana rungume da babyn,,,...
Suna isa dasauri momy tafito tareda y'an uwanta waenda sukazo a tare domin tarban su JAWAAD saitaga JAWAAD yafito jiki a mace yana rungume da baby, yana ganin momy wasu sababbin kwallah suka zubomasa momy naganin haka tafara tambayarsa cikin damuwa,,...