_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 39~40*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Cikin sauri suke tafiya yana rik'e da hanunta sai kwallah take tana jero addu'oi a bakinta, can suna cikin tafiya saitaji maranta yawani irin murd'awa nan tai k'ara tareda dafe maran tata,,..
Cikin sauri yarik'ota tareda fad'in "hubby na menene...?" batace komaiba tadai dafe maran nan yarik'ota suka zauna arikice cikin tashin hankali saboda ganin yanda takeyi,,..
Cikin tsoro yasake tambayarta "hubby na meke faruwa ne meke damunki meke maki ciwo...?" bata iya amsa masa ba saboda matsanancin ciwonda takeji a maranta dakuma bayanta da'alamu dai nak'uda ce,, ganin kan hanya suke yasa yakamata sukad'an b'uya a k'ark'ashin wata bishiya wacca ciyayi suka kusa rufeta sukai mata rumfa nan yazauna sannan yad'ora kanta a jikinsa yana tofa mata addu'oi sai juyi take hanunta d'aya kuma ta dafe k'asan maranta,,...
*******
Tini y'an dabanda dady yaturo suka iso School d'insu suka fara zuwa suna nemanta nan aka had'asu da Amina, tana ganinsu ta ganesu saboda dik yanda mugu yai shigar mutanen kirki indai har kanada hankali dakuma tinani zaka iya gane cewa shi ba mutumin kirki bane saboda sam shigar bata dace dashiba,...
Cikin sakin jiki dik tsoronda takeji ta b'oye shi tace masu "ZULAIHERT tayi tafiya ta tafi England gun k'anwarta zuwairat an kira ance batada lafiya shine ta tafi" harzasu sake mata wata tambayar nan tadinga addu'ah Allah yasa sutafi karsu sake tambayarta cikin ikon Allah kuwa sukace mata to bakomai sun gode sannan suka wuce, suna wucewa tai sauke nannauyan numfashi taredayin godiya ga ubangiji sannan tawuce,,...
Sam basu yarda da abunda Amina ta fad'a masuba danhaka suka sake tambayar k'awayemta nantake aka fad'a masu sumayya,, cikin sa'a kuwa suka taddata a gidanta nan suka fad'a mata abunda yakawosu gunta,..
Kamar dama jira take kuwa nantake tafad'a masu komai sannan tamasu rakiya har gidan ZULAIHERT inda tasan suna a zaune yanzu,, koda sukaje sai suka tararda gidan a rufe nan tasake rakasu gidan su JAWAAD a canma koda sukaje a rufe yake tofa nan suka fara musayar yawu su da ita sukace tinda dai ita k'awartace lallai ba shakka tasan inda sukaje, nanfa sumayya tafara rantse rantse tana cemasu "wallahi wallahi Allah bansan inda sukajeba" tatsorata sosai ganin sunfidda bindiga sun nunata da ita,,...
Sunacikin wannan rikicin saiga Amir ya'iso tareda abokanansa yana ganin sumayya ya ganeta saboda yana yawan ganinta tareda ZULAIHERT,, dikda yaga bindiga shima tsoro yakeji amma haka yadaure yatambayesu laifinda tamasu,,....
Cikin sauri sumayya tafad'amasa tace "dan Allah kokasan inda JAWAAD da ZULAIHERT sukaje ne" murmushin mugunta yai nan take yace "d'azunnan nagansu sunbi hanyar babban daji su biyu nayi mamaki sosai saboda bakowa ke shiga dajin ba sai mafarauta kawai" sunajin yafad'i haka ogansu yace "d'an samari ba kwatance zaka manaba nunamana hanya zakai muje kawai" yana maganarne kamar mai maye ganin yanda suke yasa ba musu dole Amir yashiga gaba shi da abokanansa sukuma sukabiyo bayansu,,...
Saida yanunamasu hanyar suka wuce sannan shikuma suka wuce itama sumayya tawuce tana sauke numfashi, kai tsaye dajin suka shiga suka fara tafiya suna neman inda zasu hango JAWAAD da ZULAIHERT,,,...
**** ****
Kai tsaye momy police station tawuce tana zuwa tamasu bayanin komai kasancewar momy shahararriyar doctor ce wacca kowa yasanta mai taimakon al'umma ce gakuma tausayi da san mutane nantake aka kaita gun Commissioner tamasa bayanin komai, cikin sauri kuwa aka had'a komai tabada kud'i yace bazasu karb'a ba ai girmanta yakai komai zasu iya mata batareda sun karb'i ko sisinta ba,,,...