_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Congratulation Sister Maryam Mamu gee for completing of ur amazing and educating novel DAWOOD, may God bless u and protect u with ur enemies, and may God help u to achieve anything wht u do ameen*_👏 ❤🌷
_*PAGE 31~32*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Acikin mota zuwairat tace "yaya nafa fad'awa momy komai amma wallahi tanuna b'acin ranta sosai yanzu haka jira take ki iso" da sauri takalleta tace "zuwairat ince dai dady baijiba koh" baijiba yanzu dai zaiji dan ni zan gayamasa da kaina. Cewar zayyan,,..
Wani kallo tamasa mai had'e da harara yai dariya yace "banda ni da momy ba wanda yaji maganar amma fa yaya wannan lamarin nada tsintsar hatsari wallahi tsoron zuwan ranarda dady zaiji nake dan nasan harmu sai laifin yashafa" murmushi tai tace "karku damu y'an k'annena insha Allah komai zaizo da sauk'i ai Allah baya barin bayinsa acikin k'unci batareda yasamarmasu mafita ba alkhairi na aikata ba sharriba saboda haka inada tabbacin ubangiji bazai tab'a barina na wulak'anta ba mudai cigaba da addu'ah Allah yasa komai yazo da sauk'i" suka amsa da ameeen,,,..
Suna isa bayan driver yai parking suka fito atare suka wuce izuwa cikin gida masu aiki sukazo suka kwashi kayanta suka shiga dasu ciki,,..
Suna isa parlor sukai kicib'is da baba nan ta wangare baki tana dariya da bakinta marar hak'ora tace "kai lale lale da zulai na y'ar gidana sannu da zuwa" ZULAIHERT tai dariya tace "baba sannu dai ya aiki" tace lafiya k'alau ya hanya ZULAIHERT tace "Alhmdllh" daga nan suka wuce ciki,,,...
D'akinsu tawuce tai wanka tasauya kaya kasancewar momy bata dawo daga aikiba sai tafito parlor,, koda tafito baba harta shiryamata launche tagirkamata irin abincinda tafi so tafi sha'awar ci saidai tana ganinsa ta b'ata fuska tarufe hancinta, mamaki baba taji itada ke zumud'i tana tsalle idan aka mata tuwon shinkafa d'anya da miyar kub'ewa bushasshe amma yau gashi anmata batai murnaba batakuma nuna farincikintaba harma da rufen hanci,,,...
Baba ce tace "a,a zulai ya haka kuma best food d'inkinefa na girkamaki" dayake baba tsohuwar y'ar boko ce sosai, yatsine fuska tai tace "kawai baba ni yau bana sha'awar cinsa d'an malele nakeso da mai da yaji kuma yajin yaji tafarnuwa sosai sai kuma kunun gyad'a ko kunun aya su nake sha'awar ci yanzu" tana gama fad'ar haka takoma parlor tazauna tareda kunna TV tafara kallo,,,...
Itadai baba tabarta da mamaki batace komaiba takwashe kayan tawuce kitchen sannan tayiwa sauran ma'aikatan umarni dasu girkawa ZULAIHERT d'an malele yanzu itakuma zata had'a mata kunun gyad'a,,..
Batafi 15mnts da zama ba bacci ya d'auketa anan kan kujera koda su zuwairat suka fito saisuka taddata tana bacci, rigimarsuce ta tadata saiga baba tashigo ta ajiyemata d'an malelen da kunun gyad'a tawuce,, mamakine yakama zuwairat ganin ZULAIHERT tanacin d'an malele ita da ko d'an wake bata damu dashiba bare d'an malele amma yau itace ke cinsa kamar zata had'iye plate d'in,..
Signal tayiwa zayyan da ido aikwa nan sukaita kwasan dariya itakuwa ko ajikinta ta sharesu dan yunwarda takeji bazama tabarta ta'iya yin masifa ba yanzu sai taji cikinta ya d'auka tukuna,, cinsa tai tacinye tass harda sud'an plate takuma shanye kunun dika tai gyatsa tai hamdala ga ubangiji sannan takira asabe mai aiki tazo takwashe kayan tawuce dasu itakuma tai kwanciyarta,,,...
Fira suke ahankali gobe zasuje gidan Auntyn su mamu ta haihu har anyi biki saboda suna School basujeba yanzu tinda sun dawo dole suje, maryam y'ar k'anen dadyn suce yayar Zayyad wanda yace zai had'a ZULAIHERT aure dashi,,,...
Around 6:00pm momy tadawo cikin zumud'i sukaje suka taryota sunamata oyoyo sannu da dawowa, cikin sakin fuska ta amsa masu amma tana ganin ZULAIHERT ta b'ata fuska takuma shareta tayi kamar bata gantaba zuwairat takula da hakan amma saita share suka wuce cikin gida,,..