_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 3~4*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Bayan sunfita daga dajin sai yaimasu umarni dasuwuce gida nan suka wuce shikuma yawuce da'ita,,, wani gida naga yashiga k'arami mara girma mai d'auke da d'aki biyu da ban d'aki d'aya sai filin gida mara fad'i sosai, da shigarsa kuwa sainaga wata 'yar dattijuwa kyakkawa zatakai kaman shekara 50 zuwa 51 ta taso daga gunda take a zaune tayo gunsa tana fad'in "JAWAAD meyasameka haka naga dik jikinka tsago da jini kuma ina kasamu wannan yarinyar...?" dik alokaci d'aya tajeromasa waennan tambayoyin,, murmushi yai sannan yakai hannayensa biyu ya rike kuncenta yana murmushi tareda sumbatarta a goshi sannan yace "ummi na kwantarda hankalinki munje dajine shine naga wannan yarinyar tana gudu ashe Zaki ne yabiyota shine nataimaka mata harma kuma nai nasarar kashe zakin" zaro idanunta tai cikin mamaki tace "JAWAAD kana nufin ka kashe wannan mugun zakin daya hanawa mutane shiga dajin suyi yanda sukeso" murmushi yasakeyi yace "Eh ummi na nakasheshi" wata runguma ummin tamasa tareda kaimasa sumbunta tana shafashi tana fad'in "akodayaushe ina alfahari dakai amatsayi d'a na tabbas KAI KAFI CANCANTA da akira ASSAD wato namijin zaki Allah ya albarkaci rayukarka yarona" yace "ameen ummi na",,,,,
Juyowa yai gunta yakai hannunsa yasakko da ita a k'asa, yana sauketa tai wata k'ara mai d'an sauti tareda fad'in "wayyo kafana" cikin sauri yajanyota ta fado jikinsa sannan yace "menene kuma" b'ata fuska tai kwallah nabin kuncenta tace "lokacinda nake gudu ne k'aya tashigeman a k'afa kuma wallahi zafi takeman bazan iya tafiya ba dan Allah kutaimakeni" tafad'a cikin yanayin damuwa,,, wacca yakira da ummi ce tace "JAWAAD taimaka mata kashigar da'ita ciki" ba musu kuwa yad'auketa cakk yawuce, a ransa kuwa mamakine fall yacikasa jin rashin nauyinta da yai idan kaganta a ido zaka rantse wani nauyine da'ita,,,,, acikin wani d'aki yakaita yasauketa sannan yafito abunsa itakuma matar tashiga.
******* ******
*WANENE SHI....?*
MUHAMMAD JAWAAD MUBASHIR shine cikakken sunansa, cikakken buzu jinin larabawa, JAWAAD kyakkawa ne nagaske tindaga kan sexy eye's nashi hancinsa lips nashi tsayinsa dakuma cikakkiyar sumarsa ta buzaye mai kama da ta larabawa, komai nashi is accurate from his skin colour to his foot,,gashin kansa a kwance yake lublub daka gansa kasan cikakken buzu ne jinin larabawa bcoz he looks axactly like his Father that's why mahaifiyarsa kematukar k'aunarsa saboda kamanninsa da mahaifinsa yakan tinamata dashi adik lokacinda tagansa,,,,, lips nashi is pink colour and yanada thick eye lashes and brown eye da beautiful set of teeth nashi, eye bolls nashi is something eyes bcoz idan yazarosu ko yanayiwa Rumaisa fad'a kaman fitowa zasuyi a waje don kaman paper's suke,, zazzak'ar muryansa kaman kanari mai zakin sauti and he's the first born agun mahaifiyarshi da mahaifinshi Rasheed da Rumaisa dik kannensa ne, mahaifinsu ya rasu Rumaisa nada shekara biyu alokacin kuma yana ss2 dakyar yasamu yakammala secondry School bayan yagama kuma baicigaba ba saboda shine ke nemowa yakawo gida aci danhaka ba lokacin karatu harkuma yaje yanemo yakawo haka yahak'ura dole badan yasoba amma kannensa kam dik yasakasu sunayi,, Fatima wato Ummi mahaifiyarsu mace ce mai hak'uri da tawakkali cikakkiyar balaraba ce shuwa'arab wannan dalilin ne yasa kyan JAWAAD yai yawa sosai saboda shi ruwa biyu ne mahaifinsa buzu mahaifiyarsa Shuwa'arab,, takanje yakarb'i haihuwa kuma tai wankan jego abiyata hakkinta kuma tana bada maganin gargajiya wanda tagada ga mahaifiyarta,,,,,..
JAWAAD mutum ne mai sauk'in KAI mai sanyi hali dan everything nashi is like his father kyawawan halayen mahaifinsa yasa kowa kesanshi haka daya rasu mutane da dama na k'auyen sunyi bak'in ciki wasuma harda kuka, wannan farin jinin ne na mahaifinsa yadawo kansa,, JAWAAD namijine nagaske cikakken jarumi mai tsananin kwarjini a idanun mutane harma da dabbobi dandik dabbarda ta gagari kowa shi akekira yakamata ko yakasheta wannan jarumtar tashice tasaka mahaifiyarsa kekiransa da ASSAD wato namijin zaki,, dik dajindake cikin wannan k'auyen dama wasu kauyukan ba wanda baya shiga yayo farauta yafito, shike kaiwa masarauta nama idan bashi yakawoba toh ba namanda zaaci dole sai anjira yakawo sannan adafa aci,, yasamu girma da matsayi acikin garin ba kad'an ba danma tashi hartafi ta mahaifinsa,,,,".
Wannan kenan****** ******
Ummi nashiga tahad'a wasu ruwa masu kala nan tazauna tana murmushi tace "'yata ya sunanki ne...?" kallonta tai sannan tace "ZULAIHERT" masha Allah suna mai da'di ZULAIHERT ta maimaita sunan sannan takamo k'afarta tad'ibo ruwan datashigo dasu tazuba a k'afar tawanketa sannan yasaka wani abu mai tsini tafara ciro k'ayar,, wani azababben zafi taji yafara ratsata alokacinda akaciro wata k'atuwar k'aya acikin k'afar aikwa nan tai wata k'ara mai sauti wacca tasaka har JAWAAD saida shigo da sauri saiyaga abunda ummi kemata danhaka yajuya yawuce,,, khalas.. khalas....khalas abunda ummin kefada kenan sannan tad'akko wasu ruwan daban tasake wanke k'afar sannan tazuba wani gari da'alamu maganine,, bayan tazuba sannan tasaka kyalle fari tass tad'aure k'afar,,,.
Bayan tagama mata dressing and k'afar sannan ta tashi tafita, ruwan wanka tahad'a mata masu d'umi saboda kayanjikinta diksin baci su kallace kumadai shigar sam bata mata shiyasa takeso tai wanka tacanjasu,, d'akin takoma ta taimakamata takaita band'aki sannan tafito,,,, bayan tagama wankan ma saida ummi takoma ta taimakamata tafito,kayan Rumaisa ummi tabata riga da sket na atamfa masu kyau d'inkin 'yan ghana tasaka kuma saisukamata ciff ciff kasancewar Rumaisa ma ba baya ba tanada girma gakuma girman halitta, bayan tagama sannan ummi takawomata abinci mai kyau tuwan garin masara wanda akai talge da marasa sannan aka zuba garin semovita akai yai laushi sosai da miyar kub'ewa d'anya wacca taji nama, dafarko ZULAIHERT kyankyami tafara amma lokacinda tafaraci hmm saitabani kunya dan cinsa tadingayi bako kunya har saida takusa cinyewa sannan tabari hakanan,,,,..
Bayan tagama ummi takawomata ruwa tawanke hanunta kuma tasha sai ummi tace takwanta akan gado tahuta nan ta kwanta kuwa bacci yai awon gaba da'ita...
#/Vote
#/Share
#/Comment'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊