page 3to4

139 4 0
                                    

♣ *DANGANTAKAR* *MU* ♣



                *NA*
       *Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
      
      ~SADAUKARWA~
  Ya umar ɗalha
   Aunty Beelat
   Fatima Mazadu

Wattpad @fatimaumarmoddibo

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN  PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*

page3to4

Da sallama Hafsa ta shigo d'akin hannun ta ɗauke da kwanan abinci, sai da tazo gaban ta sanan ta aje mata, ta ce

"Yaya gashi in kin gama Inna na kiranki

Da sauri ta ci abincin ta fito, a tsakar Gida ta tadda Inna ita da Baba sai da gaban ta ya ɗan fadi amma ta dake ta dushe inda suke

Tsugun nawa tayi har kasa, kanta a kasa tace

"Sannu da zuwa Baba"

Cikin annuri ya ce mata
"Lafiya Khadija"

Inna ta kalle shi ta ce

"To gata nan dai, ka fahimtar da ita ko zata fahimta dan ni na kasa fahimtar da ita

Kallon Khadija yayi idanuwan ta duk sunyi ja ƙiris ya rage hawaye su fito, tausayi da mamaki ya kama Baba, bai taɓa ganin Khadija ta damu akan wani abu ba, da har zata zubda hawaye akanshi ba, cikin sanyin murya ya ce

"Khadija"

Da gyar muryar ta ke fita ta ce

"na'am

"Khadija ba dan naga ɓacin ran ki zan hana ki zuwa ba, sai dan ina jin tsoran wani abu da bansa komeye shi ba, kinaji na?

Bai jira jin amsarta ba ya cigaba da magana

"'Baki taba ɓata min ba, kuma nima bazan ɓata miki ba  Khadija zan barki ki je, amma ina san ki natsu Khadija, karki ɓaran min da mutunci da zuri'ar mu baki ɗaya, wllh ban da niyyar barin ki zuwa bikin nan, dan naga kin shiga damuwa ne, ki natsu Khadija,  na yarda kuma na gamsu da tarbiyar da na baki, amma zuciyata ta kasa samun natsuwa ne, Khadija ba dan ni ba dan allah da annabinshi  ki natsu karki zubar mana da mutuncin ahali da kimar mu a idanan duniya


Hawaye ne, yafa bin kykkyawar fuskarta wai yau ita babanta ke ro'ka

"Ya isa bance kiyi kuka ba, dan karki yi kukan zan barki zuwa bikin nan, ya isa haka tashi ki jeki shirya allah ya tsare ya kareki ya kaiku lafiya yadawo da ku lafiya, tashi kinji

Da gyar ta iya tashi, gaba daya jikinta ya mutu ta rasa abin da ke mata dadi,zumidin da take tunanin zata yi in aka barta, duk bata ji sai ma wani irin yanayi da ta tsinci kanta a ciki.

Ko da ta koma d'aki kasa hada kayan tayi dan ilahirin jikinta ya mutu,ta dau lokaci mai tsawo bata ko mutsa ba, sai da inna ta shigo  d'akin tace mata

"wai ba zaki shirya ba ne, ance fa motar daukar amaryar ta isu, kiyi ki shirya mu tafe tare.

Ahaka jiki ba gwari ta shirya tare da inna suka fito, baba baya gidan ya fita.

wani dan madaidaicin gida na hanga ga  mutane  da yawa kusan duk yan kauyen ne, su kansu suna mamakin iyayen farida su a cewar su saidata zasu yi, dan makudan kudin da ya dan'ka musu, shiyasa kowa ya garzayo ya ba idanshi abinci kar ayi basu.

wata tangamemiyar motace a kofar gidansu farida wacce zata iya daukar ilahirin yan kauyen har anfara shiga motar

gab da gidan suka matso wasu yan mata suka tasu gurin su, suka gaida  inna,inna ta shige gidan ta barsu

wata yar madaidaiciyar buduwar kai da ganin ta kasan kunya bata isheta ba  ,tana yatsina tana kallo khadija tace

"uhm su babbar kawa sai yanzu ,ai na dauka ba zaki zu ba, da kuwa kin ba, farida kunya

wata daga cikinsu ce tace "ya isa haka fulaira yanzu dai ta zo ko, yan bakin ciki saidai su mutu

na ri'ko khadija suka shiga cikin gidan

suna shiga kai tsaye d'akin farida suka shiga.

da gudu naga ta tasu ta rungume khadija

"waiyo har naji dadi khadija, da ba'arki ba da bazan je ba, wllh tun d'azun nake ta addu'ar allah yasa mlam ya barki, sunan da suke kiran baban khadija malam dan shine babban malami a garin

wani guntun murmushi wanda bai samu gurbi a zuci ba, khadija tayi

"allah ya amsar addu'arki farida ya barni

wata tsuhowa ta le'ko dakin tana fad'a tace musu

"wai wainar me kuke toyawa ne tun dazun mota ta isu, kuma na shigo na gayamusu, kunsan gari ba nan kusa ba amma ku tsaya iskanci, to me tukin yace ku fito haba,  mu tun dazun muka shiga motar muna jiranku, ku kuna nan kuna tsiya to wallahi maza ku fito

faridar ce tai mata magana"yi hakuri goggo khadija muka tsaya jira amma duk mun shirya, kuma gata ta zu

"to ku fito

fitowa suka yi, daga gdan khadija sai raba  ido take yi ko zata ga inna amma ina bata ganta ba, har suka shiga motar

oh su khadija andau hanyar avuja to ku biyoni dan jin yadda abubwa zasu wakana💃💃

to bari dai muje waye khadija?

malam yusuf shine ainihin sunan mahaifin khadija, haifaffan da katsina ne, duk zuri'arsu malamai ne, musu fada aji, ga basira amma saidai basu da kudi saidai 'kana'a wadatar zuci.

fatima shine ainihin sunan inna mahaifiyar khadija, ita ma haifaffiyar yar katsina ce, mlam yusuf malaminta ne, ganin natsuwarta yasa malam yusuf naiman auran fatima, iyayenta sunyi maraba da haka, aka daura musu aure, shekara  biyu da auransu suka haife khadija  saida khadija takai shekara bakwai sannan suka kara haiwuwar hafsa, khadija yarinyace mai natsuwa da rashin son hayaniya, ga zurfin ciki, shine ma yasa su yin mamaki gnin yadda ta nuna rashin hakurinta a kan zywa bikin farida.





wannan kenan

ku biyoni abuja muji yadda abin yake



*like*
*comment*
*shire*
and vote me on wattpad
@fatimaumarmoddibo


keep  flowing  🚴‍♀🚴‍♀🚴‍♀🚴‍♀🚴‍♀🚴‍♀


~bhartoolerty~

DANGANTAKAR MUWhere stories live. Discover now