page 32 to 33

88 8 3
                                    

♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣



                *NA*
       *Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
      
      ~SADAUKARWA~
  Ya umar ɗalha
   Aunty Beelat
   Fatima Mazadu

Wattpad @fatimaumarmoddibo

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

'''Ya Allah remove  all arrogance in my  heart, Ya allah dukkan wani abunda zan mallaka wanda zai sa ni girman kai ya Allah ka hana ni shi, da dukkan wani ilimi ko basira wacce zata sani girman kai  Ya Allah ka tushe min basira daga iya abinda zaisa naji girman ka, Ya Allah na roƙe ka da saunanniyar murya da zuciya ka raba ni da dukkan abinda zai  sani girman kai.'''

____________________

💃💃Lale maraba da ke  *Madubiyar* *golden* *pen* *writers* *Asso.Marubuciyar* hamshaƙin littafin nan *BANFI* *ƘARFIN* *TA* *BA* ,omme deedat na tayaki murna allah ya baki ikon riko.


Page *32* to *33*

Zaune suke akan manyan kujerun dake cikin ƙaton falon wanda girman falon isa a gidana manyan  ɗaku na biyar a cikin sa.


Ba abinda ke tashi daga cikin falon banda sautin kuka.

Sun kai minti talatin a haka cikin kuka ba wanda ya kalli wani balle ya bashi hakuri.

Wani kyakykyawan rayo ne ɗan ki manin shekara bakwai ya shigo ɗakin da gudu da shigarshi ta kayan makaranta,sai da ya iso har tsakiyar su sanan ya ce"Oyoyoo   Grandy ,da gudu ya faɗa jikin wanda ya kira da Grandy ɗin"

Lokaci ɗaya ya tsaida kukan shi ,wata fara'a ta baiyana a fuskar shi ya ce "Ka dawo  *Muhsin* ya makarantar?

"Lafiya grandy yau baka zo ɗauka ta ba ,lafiya kuwa?

Yana gama faɗa bai jira cewar shi ba,ya tafi gurin wacce ke zaune a gefen kujerar wanda ya ki grandy ɗin,kan jikin ta ya faɗa ya ce"Hubbi kema yau kin manta da ni ko"

Murmushi tayi kamar wacce bata taɓa kuka ba bayan yanzu ta gama kukan amma zuwan muhsin ya kawar musu da dukkan damuwar su.

"One (sunan da take kiran shi  shikenan) ya zan manta da kai , bugun zuciyata ɗan lele ban isa na manta da kai ba"

"Yes i know it,ya buka tsalle ya rungumeta,sanan ya janye jikin shi,ya tafi gurin wanan kyakykywan matashin wanda shi ma yana zaune a falon.

"Dady ya faɗa kan jikin shi.

"Son ya kike "

"Lafiya lau dady grandy da hubbi yau basu zo gani na ba,kai ma haka"

"Sorry son"

Abinda ya ban mamaki da waɗan nan bayin Allah wato wata irin kama naga suna yi wacce shekaru ne kawai zai banbanta su da juna hadda muhsin ɗin.

Hubbi(Abudulmannan Waris Abudul ahad) shine ainihin sunan shi,shi ne wanda yawa Khadija fyaɗe.

Haifaffun yan garin misra ne ,shi da ƙanwarshi Hubbi(Jazra  Wasri Abudul Ahad,Saboda so da kaunar da suke wa juna yasa suke kiran Junan su da Hubbi.

DANGANTAKAR MUWhere stories live. Discover now