♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣
*NA*
*Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
~SADAUKARWA~
Ya umar ɗalha
Aunty Beelat
Fatima MazaduWattpad @fatimaumarmoddibo
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
Gare ki jamila da mutanan ki aradu bani mantawa da ku har gaban abada, na gode na gode👏👏allah yabar kauna.
page 20 to 21
Zaune take akan tebur ita kadai ta yi tagumi tana kallon abincin da ke gaban ta, a zuciyarta ta ce "Ya allah ka taimake mu da kai muka dogara da kuma abincin nan"
Bata fi minti biyar da gama maganar ba, ta fara ganin mutane suna fitowa daga ƙasan layin su,kuma da alama ma'aika ta ne dan kayan jikin su iri daya ne.
Tana ganin sun nufo inda take tayi sauri ta miƙe tsaye "me za'a baku ? ta fada cikin sanyin murya.
Wani bahaushe daga cikin su ya kalle ta ya ce "Me da me kike da shi?
"Shinkafa da taliya da wake da doya ,tana maganar tana fuɗe kulolin
"Akwai nama da ruwa?
"Eh akwai ta nuna musu
"To bari ogan mu ya zo,muna aikin wani Gida ne a can ƙasa ,to zaki dunga kawo mana kullum?
"Eh kullum ina yi, ta faɗa wani farin cike ya mamaye ta
Wanan motar da ta watsu mata ruwa ta gani ta nufo su har yanzu sautin waƙar kiss daniel ne yake tashi daga cikin motar ,kamar ɗazun dai yanzu ma haka da gudu ta nufo su.
Gaba da ita kaɗan motar ta tsaya tai minti biyar ta zuwa gurin Amma ba wanda ya fito,sai chan aka buɗe motar aka sako ƙafa, kafar kawai ta kalla ta gani macce ce dan ɗamammen wandon jikin ta da dugon takalminta ,hannu ta ziro waje ƙunbunan ta zara-zara kamar mai cin kare sun sha bluen cotes kamar na arniya.
daga ɗayan ɓarin na motar kuwa wani kyakkyawan guy ne ya fito kai tsaye ya fito dan ganin shi kawai tayi ,kai masha allah tunda kan shi ta fara kallon shi fari ne sosai irin hasken larabawa ga gashi ya bari akan shi kamar mace shi kanshi gashin abin kallo ne dan yadda yake ƙyalle da sheƙi gashi baƙi ƙirin sexy eyes gare shi ga su manya-manya ya yalwar gashin ido its kuwa girar shi ko macce albarka dan kamar zan mishi kabin ɗin ta ita ma baƙi ƙirin da ita dugo kuma sirin hanci ya ƙara fito da kyaun fuskar shi ,shafe ɗin fuskar shi irin na larabawa ne ɗan karamin bakin shi jajir kamar an saka jan baki ga bakin ƙarami shi ya ƙara ainihin fito da kyaun fuskar shi,ba wani dugo ba ne tsaka-tsaki sanan kuma bashi da qiba daidai wanda ba zamu kira da sirri ba kuma ba zamu ce lukuti ba.