♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣
*NA*
*Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
~SADAUKARWA~
Ya umar ɗalha
Aunty Beelat
Fatima MazaduWattpad @fatimaumarmoddibo
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
*Bloody* *Bugun* *zuciyata* ku sani ni Fatima Umar Moddibo ina matuƙar ƙaunar ku kuma ina alfahari da ku ❤.
page 5 to 6
"Khadija wai lafiyar ki kuwa tunda mu ka fito naga kamar wani abu yana damun ki"
Kallon Farida tayi ta ce " Farida wallahi ban jin daɗi jiki na ya mutu ga shi gaba na sai faɗuwa yake yi"
"Subhanallah baki da lafiya ne ?ta kai hannu ta taɓa jikin ta
"A'a lafiya ta qalau ban san abinda ke damu na ba "
Riƙo hannuwan ta Farida ta yi ta ce"Addu'a zaki yi khadija ba abinda zai faru da yardar
Allah ki kwantar da hankalin ki ,muna tare "Duk yadda Farida ta so ta kwantar w
ma Ƙhadija hankali abin ya gagara ,tun suna ƙara nufo Abuja gabanta yana ƙara faɗuwa, na damar zuwa ta fara yi ,Allah sarki Khadija sai da ƙaddarar mutun bin shi take yi ,shi ma kuma yana bin ta.Gaba ɗayan su barci ya ɗauke su tun kafin su kawo zaria.
>>>>>>>>>>>>>>>>
..Zaune take akan wata ƴar ƙaramar kujera a tsakar gidan ,tagumi tayi tana tunanin Akan Khadija.
"Inna ki kawo kuɗin na siyo miki iccen ko yau ba za'a yi girkin ba ne?
Maganar Hafsa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa.
"Kina tunanin Yaya Khadija ne ? Hafsat ta tambaye Inna
Kasa bata amsa Inna tayi,kuɗi ta kwanto daga habar zanin ta ,ta miƙawa Hafsat
"Gashi kiyi sauri ki dawo ,kar muyi dare
Amsar kuɗin tayi ta ,ta fito ,Hafsat yarinya ce bats fahimtar abubuwa da yawa ,suna Kama da Khadiji sosai saida Khadija fara ce ita kuma Hafsat wankan tarwatse ce,kykkyawa ne su ,kamar fulani , suna da tsawo fuskar da cikar fuska ɗan jikin daidai a gashi ba laifi za'a kira su masu gashi.
*Garin* *Abuja*
Hayaniya da karar mota ya farkar da su.
buɗe idanuwan su suka yi ,suna kallan babban birnin tarayya ,a haske ta ko ina shi ya ƙara basu sha'awa ,duk da rana ta faɗi har an kira sallah amma hasken garin ka ce me,manya manya gidaje masu matuƙar kyau da girma abin kamar ba'a 9ja ba ,ni kaina saida na bada aron idanuwa na ga kallon hamshaƙan gidaje waɗan da a tivi na ke ganin su lolx yes ba ƙarya ba ne ranar da na fara zuwa can na baro eyes ɗn ne hhhhhh
,balle su ƴan kauye ko tivin ba su kallo ,ya kuke ganin zasu nuna ƙauyanci.Wani katafaran dankareran makeken Gida su ka ga direban ya kunno kai yana ma me gadin horn.
Ba tsofaffun ba hatta su ƴan matan saida suka tsorata ko gidan ƴan yankan kai ne.
Kafin su ankare sai gasu A harabar giɗan mai haske ɗa kyau ,har direban ya sauko basu sauko ba ganin ba su da alamar saukowa yasa direban ya matso ya buɗe kofar ,ihu suka yi gaba ɗayan su dariya suka bashi yayi dariya har ya gaji.
"Dan Allah ku fito wallahi ba abinda za'a mu ku da ni ba'a min ba ku fito ɗan allah.
Allah sarki Khadijs daman tunda suka shigo jikin ya mutu hatta bakin ta matuwa yayi Farida ta riƙo hannunta suka fito da gyar ta ke iya iya tafiya.
Wani hamshaƙin hadaɗɗen falo suka tsinta kan su a ciki ,shirko -shirko suka yi a tsaye suna kallan haɗuwar falon da girmanci hatta khdija sai da hankalinta ya karkata gurin kallon falon.
Da sallama direban ya shigo ɗakin wanda shi yai sanadin barin kallon falon da suke
Cikin sanyin murya ya ce" Haba dan allah ku zauna mana tunda kuka ga har kun ido ba'a yi muku komai ba to ba za'a mu ku ,ɗan allah ku zauna yanzu muka gama waya da angayen suna nan zuwa kar zu su ,su raina ku dan allah.
Zama akan kujerun suka yi ,su fulaira kuwa su a dole ba su san raini ko alamar tsoro ɗa fargaba babu a tare da su .
A kan kafaɗar Farida ta kwanta ta rufe idon ta zuciyarta na bugawa ɗa ƙarfe.
Basu ƙara minti ashirin ba sai ga wani kykkyawan matashi dugo fari sul fuska ɗauke da annuri ya sha manya kaya , da Sallama ya iso ɗakin
"Dan allah kuyi hakuri mun barku haka,ya kuka iso garin na mu ina fatan ɗai kun iso lafiya ya kuma gajiyar hanya ,yana maganar yana fara'a da murmushi da
shi yasa ma rsofafin suka saƙe Suka amsa mishi"Lafiya ƙalau yaro sai da garin na ku da nisa "
"Haka ne gaskiya amma tunda kun kawo lafiya mun godewa Allah "
Wasu matasan yara su uku suka shigo daure da ledoji A hanuwan su,su ma manya kaya suka saka kuma kowannen su fuskar da annuri ,a gaban su suka ajiye ledojin kallan su yayi ya ce" yawwa to ku shiga kicin ku dauko musu plate da kofuna da chukali "
Yana kama faɗa ya suka bi wata hanyar ɗa zata kai su kicin ɗin.
Da kwanuka suka fito ,bai ce musu komai ba suka fara buɗe ledojin nan kaji ne manya manya sai drinks kala -kala .
Kallan su wannan kykkyawan matashin yayi ya ce "Dan allah ku ci,zan je na dawo mun shirya faty ku shirya kafin na dawo ,da sai gobe da rana zamu yi to sai naga yaushe za'a gama da har zaku tafi ,to shiyasa na ce ayi yanzun..
✍~Bhartoolerty~