♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣
*NA*
*Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
~SADAUKARWA~
Ya umar ɗalha
Aunty Beelat
Fatima MazaduWattpad @fatimaumarmoddibo
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
I can't imagine my life without u my shadow i don't know how to tnx you my bestie am very proud of you 😍one in the town.
page 18 to 19
*BAYAN* *SHEKARA* *ASHIRIN* *DA* *BAKWAI*Ranar Monday ƙarfe 2:56pm watan August.
..kykkyawar yarinya ce ƴar kemanin shekara goma sha takwas duguwace ita ba fara ba ita ba baƙa ba wankan tarwatsa kenan cikin shigar uniform ɗin ta farare ƙal take tafiya kamar zata tashi sama dan tsabar sauri , duk da kasan cewar yanayin garin na ruwa ko ina ya chabe amma haka take jefa ƙarfarta ta ko ina ,duk kayanta sun ɓace da jar ƙasa, kallo ɗaya zaka mata ka gane tana cikin damuwa.
A hankali ta fuɗe ɗan karamin bakinta ta ce "Waiyo allah yanzu ya za muyi,kai wallhi uncle sagir mugu ne duk kai zaka ja mana komai yau idan ban saida abincin nan ba ya za muyi"
A hankali ta faɗa yadda idan har ba kana kusa da ita sosai ba baza ka ji abinda ta faɗa ba.
Daidai kan layin da zata shiga ,sai ga wata katowar bakar mota ta tawo da mugun gudu wakar kiss daniel yana tashi daga cikin motar,ta watsu mata ruwan chaɓalɓalin daya kwanta kasan cewar jiya an yi ruwan sama, har fuskarta da dukkan jikinta gaba ɗaya fararen kyanta sun koma ja.
Ko kaɗan motar bata tsaya ba shigewa layin tayi da gudu kamar layin na uban ta ne.
Cikin ɓarin rai tasa hannu ta goge fuskarta har zata fara tafiya wasu bayin allah suka tsayar da ita suka bata ruwa fuskarta kawai ta wanke ta musu godiya ta tafi tana mugun sauri.
Wani ɗan karami gida madaidaici naga ta shiga da sallamar ta.
Wata ƴar madaidaiciyar mata ita ba tsoho ba ita ba yarinya ba,shanyar kaya take iya a tsakar gida, da saurin ta ɗago kai cikin tsoro da ruɗiyar ganin yadda taga ta shigo gidan ta ce " *Anum* lafiya kuwa wa yai miki haka ?
tambayar da ta mata ba ita ce a gaban ta "Waiyo umma wallhi uncle sagir ne ya tsayar da mu dan mugun ta,gashi yanzu uku saura ina *ummama* ta fara fitar min da kayan ka fin na cire kaya ,tana maganar ne haɗe ta cire hijjabin jikinta ,hakan ne ya bani damar gane yadda surar jikin ta yake,dugun wuyanta na fara arba da shi sai ƴan brest ɗinta a tsaye chikk suke madaidaita daidai jikin ta bata da dumbi ko kaɗan ɗan ƙaramin kugunta sai hips manya-manya wanda hijjab baya hana a gansu ,tafiyar da ta fara ji zuwa cikin wani ɗaki ya bani damar ganin ɗuwawu kanta manya-manya irin musu yawan nan.
Ɗaga cikin ɗakin naji tana kira " Ummama umma ki mata magana ta fara fitar min da kaysn "
Ɗakin umma ta shigo tana faɗin "Anum ki bari ki huta ki ci abinci kinyi sallah kuwa?
"Eh nayi bana jin yunwa umma
"to kiyi wanka"
"A'a sai na dawo"
Da gudu wacce aka kira da ummama ta shigo ɗakin "Na'am yaya Anum kin dawo "
"Eh ummama yi sauri ki fitar min da kolar abincin da kayan ki gyara min bencin ki mai shin fiɗa ki fara aje kayan yi sauri kin ji"
"to aunty Anum tabar ɗakin da gudu "
duk maganar da Anum ke yi tana duba kayan sawa ne a cikin durowar ta ,a gaban umma ta cire kayan ta sa wata doguwar rigar atamfa ta ɗan kama jikinta kalar pink sun haska ta sosai.
Umma ta kwashe kayan ta fito tsakar gida ta zuba su a cikin ruwan kumfa.
Cikin sauri ta fito daga ɗakin ,ta taɗa kicin ya ɗauko kula ta fito tsakar gidan bata tsaya ba ta ce ma Umma "Umma zan tafi sai na dawo"
"To Anum allah ya tsare ya bada sa'a "
"Amin ta faɗa"
gaskiya zai dai kuji na dauke wuta dan baku yin comment bai fi mutane biyar ba,haba abinda da kunya ko ba dadi ne saina daina.
like
shire
comment
✅ote me on wattpad @fatimaumarmoddibo✍ *~bhartoolerty~*