♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣
*NA*
*Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
~SADAUKARWA~
Ya umar ɗalha
Aunty Beelat
Fatima MazaduWattpad @fatimaumarmoddibo
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
🤸♀🤸♀page ɗin ki ne my batula kiyi yadda kike so da shi bhartoolety ta mallaka mi ki 😍
page 12 to 13Da sauri Inna ta ƙaraso gurin ta a ruɗe ta ce " Lafiya Khadija meke damun ki? baki ta lafiya ne
"Inna...maganar ta maƙale a maƙogaron ta .
A ruɗe Inna ta fara kin "Khadija Khadija ,Hafsat ta kwala ma Hafsa kira.
Da sauri Hafsa ta fito daga ɗaki ,tana ganin Khadija a jikin Inna ta ruɗe ta fara kuka
"Hafsat yi gudu ki kira Baban ku ya zo da machin da sauri
Tun kafin ta rufe baki Hafsa ta fita da gudu.
~~~~~~~~~~~~~
A kwance ya ke akan ƙaton gadan shi ,kallo daya zaka mishi ka fahimce yana cikin damuwar da bai saba yinta ba,kykkywa ne ajin farko ko kaɗan baya kama da yan nigeria yafi kama da larabawa,tun daga yanayin kyaun ɗakin da yadda fatar jikin shi ta ke na gane cewa yana cikin jin daɗin rayuwa.
A hankali ya buɗe ɗan karamin bakin shi ya ce " *Waye* *ita* ? ya sauke wata irin ajiyar zuciya ,haɗe da runtse ido,kunnuwan shi suna jiyo mishi kukan ta.
Tunda yake a rayuwar shi bai taɓa jin kukan macen da abin ya kasa fita daga kunnan shi ba,yana matuƙar son kukan mace a lokacin da yake saduwa da ita wanan ne dalilin da yasa baya naiman karuwa sai da wacce bata san komai ba.
Zumbur ya miƙe zaune kamar an tsikare shi tushe kunnun shi yayi saboda kukan Khadija da ke yawo a cikin kunnuwan shi ,da ƙarfi ya ce "Waye ke ,plss ki barni haka akan ki na fara jin wani abu akan mace plss ya isa haka.
~~~~~~~~~~~~~
Dushe-dushe ta fara gani , sama sama take jin muryar Inna na faɗin "sannu Khadija ya jikin ?
Gurin ta ƙarewa kallo a hankali ta ce "Asibiti"
Inna wacce take zaune kusa da ita ta dafa ta tace" Eh Khadija Asibiti kina Asibiti"
Hannunta ta Kalla drip ne ,sanan ta dawo da kallon ta gurin Inna tana san cewa wani abu amma ta kasa
"Sannu yaya Khadija ya jikin?
ɗaga mata kai tayi Alamar da sauki.
Da sallam Baba ya shigo yana kallon inda Khadija ta ke ,har ya ƙarasu kusa da ita sanan ya ce" Khadija sannu ya jikin ?
da ƙyar ta buɗe baki ta ce "Da sauki Baba "
"masha Allah allah ya baki lafiya kin ji,ya dawo da kallon shi gurin Inna ya ce " taci abinci?
"A'a ba ta daɗe da tashin ba.Kallon ta Baba yayi ya ce "Khadija tashi ki ci abinci kin ji "
Ko kaɗan bata son cin wani Abu amma ta ɗaukar wa kanta alƙawarin duk abinda Baba ya ce mata ba zata musa mishi ba.
Da ƙyar ta taimakon Inna ta tashi ta ci abincin kaɗan tasha ruwa.
Sun dau lokaci mai tsawo suna fira kaɗan kaɗan ,zuwan likita ne ta tsayar da su.
Kallon Khadija likitan yayi ya ce " Ya jikin ?
" da sauki ta faɗa a hankali
"Baba ka same ni a office yanzu "
"to likita Baba ya faɗa
likitan ya juya ya tafi office ɗin shi.
Inna da Khadija suka tsinci kansu ciken muguwar faɗuwar gaba,musamman Inna ta take tunanin wani abu.
Da sallam Baba ya shiga office ɗin.
"Yawwa Baba ga guri ka zauna ya nuna mishi kujerar dake fuskantar shi.Zama baban yayi,ya tattara dukkan natsuwar yana kalon Doctor ɗin .
"Yawwa Baba ,naga kamar mijinta bai zo ba ne shi yasa na ƙira ka,ya kamata ace mijinta ne zai fara jin wanan albishir ɗin amma tunda baya nan zan gaya maka yarinyar ka tana da juna biyu na wata huddu.
Tunda baba yaji ya ambashi miji gaban shi ya mummunan faɗuwa jimmm kan shi ya ɗau nauyi yayi nisa cikin tunani
"Barka na tayaka murna allah ya sauke ta lafiya likintan ya faɗa haɗe da miƙa ma Baba hannu.
Jiki ba ƙwari baba ya miƙa mishi hannu da kyar Baba yake iya ɗaga ƙafar shi .
Tunda Inna ta hango Baba gaban ta yai wani irin mugun faɗuwa
Tun kafin ya ƙarasu gurin su Inna ta miƙe tsaye Ahankali ta ce " Lafiya ?
Har ya ƙarasu gurin su bai iya cewa komai ba kuma ya kasa zama ,ƙafar shi ta fara rawa sanan ya tsugunna.
runtse idanuwanta tayi wasu irin zafafan hawaye suna fitowa kamar famfo.
Ganin ɓarin ran shi na ƙara yawa yasa ,shi ya tashi yabar Asibitin Inna tana ta kiran shi tana tambayar lafiya amma ya kasa magana.
Kusa da Khadija Inna ta matso ita kanta Innar hawaye take yi ,a hankali ta ce "Khadija yaushe rabonki da yin wanku(period )?
Kuka mai ƙarfin Gaske ya kubce wa Khadija.
Ganin haka ya tabbatar ma Inna abinda take zargi haka ne .
Kuka mai cin rai Khadija take yi a zuciyarta ta ce" *Waye* *kai*? na tsane ka kasa nayi nadamar zuwa na duniya iyaye na sun shiga kunshi na kafa musu mugun tarihi waiyo allah na ka cuce ni ba zan taɓa tafe maka ba,ko da kuwa hakki na ne ya rake ma shiga aljanna ba zan yafe ba ,Tun a duniya zaka fara ganin sakamokon ka tsinanne allah ya tsine ma albarka kai da zuri'ar ka kamar yadda kasa mu cikin kunshi rayuwa"
Allah sarki khadija to ko waye shi?
~~~~~~~~~~~~~
"Karki ƙara min wata magana ɗan na rantse kuma bari ki ji na ƙara rantsewa Wallahi tallahi ba zanyi kisan kai ba,kuma wallahi ba za'a haifar min shege a gida ba,ba kuma zan raine shege ba,wallahi tun wuri kisan yadda zaku yi kinji dai na gama magana,taje chan ta haife shi,idan ta haife asan yadda za'ayi da shi ,daga nan sai ta dawo gare ni ita kadai ,cikin matsanaicin fushi baba yake maganar da ƙarfin shi yana gamawa ya fita a fusace....tofah gashi ni yanzu zan fara😅
ba zan ƙara typing ba gaskiya sai na ji comment in kuna son na cigaba to naji ruwan comment.
Comment
shire
✅ote me on wattpad @fatimaumarmoddibo✍ *~bhartoolerty~*