♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣
*NA*
*Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
~SADAUKARWA~
Ya umar ɗalha
Aunty Beelat
Fatima MazaduWattpad @fatimaumarmoddibo
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Ƴan* *Wattpad* shadow tana miƙa gaisuwarta
Dangantakar mu fans 1 to 2
Jamila's novel
Zahra novel
Rumaisat novel
Duniyar makaranta
Hausa novel 1 to 3
Cool novel and makeup
Golden pen fans
Kundin littafan hausa
Aushy novel
safna novel
ƴan uwan juna
Ruɗani fans
Fatima batulah fans
🙆waiyo yawa gare ku.kai duk wanda yake karantawa *Shadow* tana miƙa gaisuwa kuma ta ce tana yinku wujiga wujiga.
page *30* to *31*
Ko kaɗan Anum bata lura da Daniel ba,zuciyarta sai bugawa ta ke yi da ƙarfi amma duk da hakan bata ɗago kai ba.
"Little Girl"
Daniel ya faɗa yana kallon ta.Cikk ta tsaya gaban ta na faɗuwa a tsorace ta ɗago kai suka haɗa ido.
Wani lafiyayyan murmushi ya sakar mata,wanda yasa ta sauke kanta ƙasa da sauri.
Durkowa yayi daga kan motar ya fara tawowa inda ta ke.
Ji tayi kamar ta ruga da gudu dan tsabar tsoro,gashi sai ƙara matsota yake yi, tsayawa yayi yana murmushi ganin halin da take shi na tsoro.
"Sorry ba cutar da ke zanyi ba"
Ya faɗa yana kallon ta.
Zare idanuwa take yi,tana ajiyar zuci.
"Ya sunanki? kina jin tsoro na ne,ba abinda zan miki,ko dan ni cristan ne?
Da sauri ta girgisa kai ,da wata irin murya wacce bata yi tunanin zai ji ba ta"Anum suna na Anum"
"Anum nice name"
ya rasa dalili da yasa duk wani abu daya danganci musulmai yana jin daɗin shi musamman sunayen su.
Jin yayi shiru ya bata damar fara tafiya,a ruɗe take tafiyar sai harɗewa take yi.
Kallo ya bita da shi yana jin wani irin baƙon yanayi yana kai wa zuciyar shi ziyara,komawa yayi ya zauna.
Ko sallama Anum bata yiba ta faɗa Cikin gidan,Umma tana zaune a tsakar gidan ita da Ummama suna fira.
"Anum lafiya kike kuwa ko sallama baki yi ba"
Bata ɗago kai ba ta ce"Umma ba komai"
"Ba komai zan ganki haka"
"Eb ba wani abu ba ne,yau aiki aKa samu a makaranta na gaji jiki na duk ya mutu"
Ƙura mata ido Umman tayi tana son fahimtar ta.
Jin Umma tayi shiru yasa ta wuce ɗakin ta,bata yarda ta kwanta ba ,dan tasan sai umman ta shigo..
"Anum fito na kai miki ruwa bayi kiyi wanka ko zaki ji daɗin jikin ki"
"To Umma bari na cire kayan"