page 9 to 10

36 2 0
                                    

♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣



                *NA*
       *Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
      
      ~SADAUKARWA~
  Ya umar ɗalha
   Aunty Beelat
   Fatima Mazadu

Wattpad @fatimaumarmoddibo

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN  PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*


*NA TAYAKI MURNAR KAMMALA LITTAFIN KI MY MOM(FATIMA ZAHRA MAZADU)ALLAH YA BAKI IKON FARA WANI A SA'A.*

my  bloody( *Deejar* *one* *lv* ) ina matuƙar yinki Allah yabar ƙauna maƙiya nan kallo nan bari dumin ni da *bloody* har abada.

Kina ina ƴar sokotawa ? my bugun zuciya ( *lipton* *girl* ) ke ma aradu ina yinki  irin totally ɗin nan 😊

wanga page ɗin naki ne *Khadija* ƴar abuja 😅kinga yadda abujar take

page 9 to 10

Ihun kukan su Farida ya farkar da ita,da kyar ta iya buɗe idanuwanta kasa kallon jikin ta tayi ,wasu zafafan hawaye ta fara yi,zuciyar ta na bugawa da ƙarfin gaske.

"Waiyo mun shiga uku yanzu shikenan sun ɓarar mana da mutucin mu yanzu da wani ido iyayen mu zasu kalle mu "

Cewar fulaira kenan cikin matsanaicin kuka

Dumm-dumm zuciyar Khadija ta buga haɗe da wasu zafafan hawaye ,tuno maganar babanta tayi da ya ce " Khadija karki ɓarar mana da mutuncin zuri'ar mu,ki kula Khadija kin san yadda ake ganin mutunci na a Garin nan "

Luuu ta ƙara zubewa  kasa,da gudu Farida wacce ita ma taji jiki tayo kan Khadija tana kuka ,ihu take yi tana girgiza Khadija "Khadija waiyo Allah na nashi uku ni Farida da me zanji dan Allah ki tashi ki rufa min asiri"

Khadija tayi nisa bata jinki Farida

kaca-kaca su ke cikin jini ,sun keta musu haddi ta ƙarfin gaske dan ko wacce saida mutane uku suka fyaɗe ta.

Kuka da ihun su yasa masu gaɗin gurin tashi suka zo faɗa suka rufe su da shi 

"Wai wani irin hauka ne wanan ku daman baku san inda kuka kawo kanku ba,,to bari na gaya muku dan naga alamar baku sani ba..

Da  sauri wani wanda suka tawo tare shi ma mai gadin ne ,ya tare numfashin shi  "ya isa da alama basu sani ba ,dan tsawon shekaru bamu taɓa samun waɗan da suka yi irin haka ba ,ya dawo da kallan shi gurin goggon Farida ya ɗuka har ƙasa yaa fuskance ta  ya ce"Inna ba abinda zan ce muku ,sai dai na baku hakuri ku ɗauka kaddarar ku ce dole ku karɓe ta ,su kansu sun san basu kyauta mu ba,duk irin haka su kan bamu kuɗi mu ba waɗan da abin ya faru da su,amma ku harda motar ɗa zata maida ku gida ,da makuɗan kuɗi a baku,me motar da zai maida ku ya iso sai ku shirya akwai ban ɗaki yana nuna mats ku shiga ku gyara jikinku,har kaya akwai zai ku chanja "


Saboda tsananin yadda Farida ke jijjiga Khadija ya sa ta farko a tsorace

"Khadija Khadija Abinda Farida ke faɗa kenan  tana hawayen ban tausayi.

Cikin wata irin murya Khadija ta ce "Farida dan allah karki maida ni gida me zan cewa baba farida da gyar ta iya ƙarashe maganar.

Goggon Farida ce ta matso kusa da su ta ce "Khadija in baki je gida ba ina zaki?bata tsaya jin amsar ta ba ta ɗaura da faɗin"Dole mu je gida yanzu nan koma meye mune sila  da kuma kaddarar take bin mu ,ita kanta an mata fyaɗen amma dayake ita ta kwana  biyu shiyasa bata ji jiki ba.

Zuma Khadija ta ƙara Farida ta fara ihu Goggo jimai ta tsayar da ita.

Ita tai ta musu wanka ta chanja musu kaya.

Sai a  gurin wankan Khadija ta farka ,bata iya cewa Goggo komai kuma bata jin zafin wanka  dan ruwan zafi ne sosai ,amma ko kaɗan bata ji.

"Waye shi? ban taɓa sanin kiyayya ba yai a kanka ,ka cutar da ni ka shayar da ni guba ,ba zan taɓa yafe maka ,wllhi da zan ga wani dabba  da ya fito daga zuri'arka da shi zai zama babban maƙiya zan wanzu ina maƙa bakar
addu'a ban yafe ba ,na tsane ka na tsani duk wani abu daya shafe ka,a zuciyarta take wannan maganr hawaye na zuba a fuskarta.

Shiruu kamar ruwa ya ci su,shi kuwa direba gudu yake yi abinshi.

"Na shiga ukku ni Khadija me nayi sai da aka hana ni zuwa amma naki,ba zan iya yafe ma kaina ba ,baba sai ya tsii...

  Tun kafin ta ƙarasar maganar da take yi a zuciyarta ta faɗo daga kan kujerar a sume.

Da sauri suka yi kanta suna uhun kiran sunan duk sun tausawa kan su amma sunfi tausaya Khadija dan ita fulaira iyayenta suka matsa sai ta zo ita ma ta samu mai kuɗi.

Khadija saida tayi zuma feye da ashirin dan suna yayyafa mata ruwa ta farka dga taji su a motar zasu ka gida zata ƙara suman.


~~~~~~~~~~~~~

"Inna baki da lafiya ne?

Hafsat ta tambaye Inna.

Wata ragowar ajiyar zuciya ta yi ta kalli Hafsat   ta ce "Hafsat wani mafarki nayi akan yayar Khadija "

"Addu'a zaki mata Inna "

Kallan hafsat inna tayi ta ɗan aro ma fuskarta murmushi  ta ce "To Hafsat tashi kiyi shara jiki na ya mutu bazan iya yi ba "

"To inna ki ɗinga Addu'a ba abinda zai faru "

Murmushi Innar tayi  ta ce "To Hafat Allah ya .....


comment
shire
✅ote me on wattpad @fatimaumarmoddibo.


✍ ~bhartoolerty~

DANGANTAKAR MUWhere stories live. Discover now