BABI NA 'DAYA

1.8K 41 1
                                    

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA,MAI JIN KAI...

JAWABIN MARUBUCIYA

JAWABIN MARUBUCIYA

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


Assallamu Alaykum

Da farko zan fara nuna godiya ta ga duk wanda ya ke karanta littafin nan mai suna JINI D'AYA,

GARGAD'I

Sannan ina so nayi gargad'i ko jan kunne,cewa littafin nan jigon sa ya ginu ne a kan SOYAYYA wanda babu yadda a yi soyayya ta tafi ba tare da an yi tarayya na aure tsakanin mata da miji ba,

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Sannan ina so nayi gargad'i ko jan kunne,cewa littafin nan jigon sa ya ginu ne a kan SOYAYYA wanda babu yadda a yi soyayya ta tafi ba tare da an yi tarayya na aure tsakanin mata da miji ba,

Da haka nake cewa duk wanda zai karanta littafinan ya san cewa akwai ABUSE,some DRUGS and also  MATURE CONTENTS,wanda bazan boye komai a ciki ba tunda na san dukkanin mu ba yara bane,dan Allah wanda ya san shekararunsa ba su kai na karanta irin wadannan abubuwan ba,toh ina roko da kar a  karanta

Ba na so daga baya a dawo ana blaming dina

Ko ganin rashin dacewar haka,wanda tun da farko sai da na nayi kashedi.

Read at your own risks

Na gode ...

                      ****FARKO****                             
                             KADUNA

Kwance take tayi matashi da cinyar momyn ta ranan wata lahadi misalin karfe uku na yamma,a falon su mai matukar girma da daukar ido.A gefe daya kuma wani tafkeken talbijin ne ke ta faman aiki kamar mutanen ciki za su fito waje tsabar girman sa.

Kara lafewa tayi jikin hajiya nafisa wacce ke ta kokarin gyara mata gashin kan ta mai tsawo da cika,a lokaci guda kuma ta na mata mitar yadda take barin gashin babu kitso..

 Maryam dake kwance dan murmushi ne kan fuskar ta jin yadda momyn na ta ta dage sai famar mita take yi na rashin kitson da bata yi wanda in da sabo,ta riga ta saba,don kuwa momyn ta na sha'awar ganin kitso a kan ta saboda a cewar ta kitso na kara fiddo da kyawun mace,wanda ita kuma hakan baya ra'ayin ta sam.

A hankali ta dago da kan ta,kafin ta ce

"Kai!momy ni fah ba na son yin kitso ,na fison na bar gashi
na haka,saboda in nayi ,sai na yini ciwon kai ,sannan kitson baya dadewa sai ya kunce"

K'ADDARA TA Where stories live. Discover now