_27_28...._
Tafiyar kusan 35mnts sukai kamin su iso garin kangiwa, bayan sun iso kuma suka d'auki hanyar gidansu Saif, dakyar da tambaya yagane gidan bcoz komai yasauya yanxu, ansamu cigaba ssi bakamar da ba, wosu gidajen na ginin k'asa dik an sauyadu, gidansu Saif ma ancanja masa gini daga na k'asa ixowa na sement, bayan sun iso yai parking sannan suka fito,
....Suna fitowa Kai tsaye suka shiga cikin gidansu Saif cikin sallama, mahaifiyar sa suka fara cin karo da'ita zata shiga palorn ta, tanajin sallama saita dakata tareda amsa sallamar cikin tsintsar mamaki, bawoi zowan DEEDART agidan bane yafi bata mamaki ba, aa kayanda ke jikinsa ne dakuma yanayinda tagansa aciki wonda baitab'a zowa da irinsaba gidan,
Ahankali suka k'ariso gunta sannan yadurk'usa cikin fara'a da sakin fuska yace "Umma barka da kwana...yah gida..yah aiki?" cike da mamakin yau DEEDART ne yadurk'usa yana gaidata tace "hmm...! barka dai AHMARD, gida Alhmdllh, yh can d'in yakuma iyayenka da k'annenka" yace "dik suna lfy suncema agaidaku" saitace "to Masha Allah, kushigo ciki mana".
Nan suka shiga cikin parlon takawo masu ruwa da fura da kindirmo kasancewor su fulanine ssi, aikwa DEEDART ansamu abunda ake so nanfa yazage yasha abarsa Saida ya koshi, hakama Abbas yasha amma ba ssi ba, sbd shi fura bata acikin tsarinsa,
Bayan sungama sannan DEEDART yace mata "am... Umma, nace Saif fa, ko yana nan" cikin fara'a tacemasa "Ehh...yana can sabuwar plaza d'insa daya buda a bakin titi, bara nasaka akaiku" yace to sannan tafita,
Batafi 15mnts dafitaba saigata tadawo tareda woni yaro wonda bazaifi 14yrs ba, saitace "AHMARD...gashinan, shizai kaiku gun Saif" cikin fara'a DEEDART suka mike a tsaye sannan sukamata gdy sannan sukai sallama suka fice,
Suna fita kai tsaye suka fice izowa gun Saif, yaron yadinga nunamasu hanya har suka iso a bakin plaza d'in sannan yai parking suka fito, yaron ne yaje yafadawa Saif yayi baki, bayan yafad'a masa sannan yadawo DEEDART yabashi y'an kud'i ya karb'a yai gdy sannan yafice.Saif nafitowa yahango su a jingine kan mota, dasauri yaje cikin fara'a da tsintsar farinciki yana murmushi, DEEDART ma yana ganinsa yafara fara'a nantake kewar aminin nasa tadawo masa sabuwa, dasauri Saif yazo yarungume DEEDART cikin tsintsar fara'a haryana zubda kwollan farinciki.
Nandai yajasa suka shiga cikin mota sannan suka shiga gaisawa, Saif yace "Sir. bakada lfy ne hala, naga kayi wota iriyar muguwar rama kamar wonda yai jinya" murmushi yai sannan yace "lafiyana k'alau Saif, saidai wlh inacikin wani hali wonda nakasa fahimtarsa, nakasa gane abunda ke shirin faruwa dani, nasani Saif kafi kowa sanin waye ni, kuma kafi kowa sanin halayyata, Saif kasani tinda nake bantab'a saka wota y'a mace a rainaba, sannan macema Sam bata a gabana, bata acikin abunda zansaka agabana harya dameni, amma wonnan karon tasauya zani,
Saif nakasa mantawa da wonnan yarinyar a raina, nakasa cireta a raina, a kullum itace take tayani fira, itace abunda nake tinawa najini acikin farinciki, sannan a zuciyata inajin woni abu akanta wonda nakasa fahimtar menene, nakasa gane meke Shirin faruwa dani" yana kawo nan saiyai shuru tareda sauke numfashi,
"Hmm....!, shine nazo gunka Saif domin kasamaman mafita sbd Kai kanka kasan banida woni aboki ko amini wonda nake fadawa damuwata sai Kai, Kaine babban yarona kuma aminina" dariya Abbas ya kyalkyale daita saif kuma yai d'an murmushi Abbas yace,
"Malama, kawoi kace kashigo hanu kawoi, amma kawoni tsaya kana mana woni kwana kwana" hararansa yai sannan yace "dalla malama kama mutane shuru dan Allah, nashigo hanu kuma kamarya?".
Saif yadafa shoulder d'insa sannan yace "Sir. inagafa abunda abbas yafad'a yayi gsky, tabbas ka kamu da son wonnan yarinyar ne batareda kasaniba" dasauri yawaro idonsa cikin tsintsar mamaki tareda fad'in "what....!!!, me kake fad'a haka Saif, are you mad, yarinyar da tatozartani a gaban idon duniya, tanemi taga bayan rayuwata, itace zakace woi zuciyata takamu da sonta, haba...haba Saif think before you talk mana" murmushi saif yai Abbas kowa har yanzu dariya yake kyalkyalawa.
Saif yacigaba da fad'in "Sir. dik woennan alamomin daka fad'a kanaji gameda wonnan yarinyar sune alamomin so woenda mace ko namiji keji idan takamu da son woni ko yamaku da son wota, yawon tinani musamman irin na soyayya yafi komai saka mutum yadinga ramewa tamkar wonda yai jinya, wonda kuma ga alamun hakan nan sun bayyana a tattare dakai, sannan yawon tinaninta dakake ya nuna cewa tabbas ka kamu da sonta ne, Sir kada ka k'aryata hakan, kamar yanda kafada nafi kowa sanin waye Kai, sanin hakan yasa nafahimci tabbas ka kamu da son wonnan yarinyar tabbas".
Shuruu DEEDART yai nawosu y'an dak'iku, Saif yadafasa tareda fad'in "kawoi muje ka bayyana mata soyayyarka agareta, kaga saikuyi aurenku kucigaba da tarbiyyar yarku dakuma sauran yay'an da zaku haifa, wlh Sir kunyi matukar dacewa da juna, had'in ku zaiyi kyau kuma tabbas mutane zasuyi farinciki da wonnan had'in naku" yakarisa cikin fara'a,
Abbas yace "perfect match kenan, dikda dai bansan wonnan pretty d'in ba, ammadai natabbata itama kyakkyawace kamar broz dina" shidai har yanzu yakasa furta komai, al'ajabi yacikasa, a zuciyarsa kowa fad'ar yake "Kai...Kai...Kai, ina haba zuciyata idan kikaman haka kowa bakimin adalci ba, baki kyautaman ba wlh, kirasa wocca zaki kamu da sonta sai wonnan yarinyar wocca tanemi taga bayan rayuwata, wocca ta tozartani a idon duniya, haba...haba" yana cikin tinani Abbas yadafashi tareda fad'in,
"Yadai broz..." numfashi yasauke nannauya sannan yace "ina tinanine dakuma mamakin kasancewor wonnan al'amarin" Abbas yace "uhm...ai al'amarin ubangiji ba abun mamaki bane, Allah yana aikata abunda yaga dama kuma a lkcnda yaga dama, danhaka wonnan ba abun mamaki bane, sannan kuma idan zai aikata baya neman shawarar kowa" sai yai murmushi wonda har ya bayyanarda fararan hakoransa.
Saif yace "Sir. kawoi kabari muje kabayyana mata soyayyarka, sbd abari ya huce shike kawo rabon woni, kada Kai sanya kaje lkc yakure maka" Abbas yace "lallai kam, gwonda kacire girmankai dadik woni abunda kakeji sbd karkaje kuma daga baya kadawo dana sani, inafatar kagane abunda muke nufi".
Nannauyan numfashi yasauke "hmm.....!" tareda gyara zamansa sannan yace "shikenan, zanyi shawara akai" sukai murmushi kawoi.
Sunjima ssi anan suna fira kamin daga bisani sukama Saif sallama suka fice.
.....Koda suka isa gida anata shirye shiryen tafiyar kamu danhaka suka fice izowa gun abokanan ango, dik yanda Abbas DEEDART yashirya sutafi kamun atare baiyiwuba, dan DEEDART cemasa yai kansa ke ciwo yana bukatar yahuta, suje kawoi gobe yaje dinner, badan yasoba dole yabarsa suka tafi,Bayan sunfice yarage saura shikad'ai acikin d'akin, nan yatsunduma acikin kogin tinanin mafita akan halinda zuciyarsa take ciki, yajima ssi yana tinani can daga karshe yasamo mafita.
Da dare bayan andawo daga kamu d'in yasami momy itakadai a d'akin hajiyarta yamata magana cikin fahimta,
"am....momy, dama inaso nafad'a maki wota magana" saita gyara zamanta kowa tareda fad'in "inajinka" saiya cigaba da fad'in "inasone naje naga yarinyar nan sbd inasone tasaba dani ahankali domin zan karb'otane daga hanun mahaifiyar ta namaidata gida" murmushi momy tai sannan tace "DEEDART kenan, bazan hanaka kaga yarka ba, ammadai kuma bazan baka goyon bayan karbe yarinyar nan ba karabata da mahaifiyarta sbd y'a mace ta uwa mace ce, sbd haka kabarta a hanunta inyaso dik abunda kasamu ka'iya kaje kakaimata, sannan kad'auki nauyin karatinta, ka karb'i nauyin daga hanun mahaifiyar tata kakuma dinga kula da'ita iya k'arfinka".Hakika maganar mahaifiyar sa gsky ce shikansa yasan hakan, amma yanaso yayi amfani da wonnan damarce ta karb'an yarinyar domin cimma wota manufa tasa agun mahaifiyar tata, d'agowa yai yace "ok momy, zanyi yanda kikace insha Allah" saitace,
"DEEDART, bawoifa nahanaka d'aukan yarka bane, aa shawarace nabaka" murmushi kawoi yai batareda yasake cewa komaiba yatashi yamata sallama yafice abunsa, batasake ce dashi komaiba tacigaba ca sabgarta dan idan dasabo tariga data saba da halin d'an nata.
.....Washe gari around 2pm bayan sundawo daga masjid yasake wonka yacanja kaya izowa wota tsadajjiyar shadda gizna mai tsadar gaske dakuma kyau, White color mai kyan gaske, saikuma hula da takalma suma masu kyau,
Nantake ainahin kyansa ya bayyana k'arara, tsintsar kyansa ya bayyana a fili sai haske yake yana kyalli tamkar hasken farin wata a sararin samaniya, bayan yagama shirinsa saiya feshe jikinsa da dad'add'an tirarukan sa masu sanyin k'amshi, bayan yagama sannan yatsaya a mirror yana kallon kansa, d'an murmushi yai sannan yashuri key car din abbas yafice..
Love u all my fam 💋❤
#/Vote
#/Share
#/Comment
#/Aufana for life.