_*CONEL AHMARD DEEDART*_
_29_30...._
Yana fita yaje parking lot yad'auki motar yafice, kai tsaye wota Central market yafice inda yafitarda kud'i yai tarin siyayya wa y'ar sa gudan jininsa, dik woni abu na bukatar yara Saida yasiyeshi, kamar kayan sakawa sitiru, abinci mak'u lashe, kayan wasa, takalma da dai sauran su.
Yakashi kud'i ssi dan idan kaga kayan kaikace shagone ma yad'akko gaba d'aya, sbd tarin yawonsu gakuma kyau da tsada, hatta Teddy's woenda yasiya sunfi a k'irga,
Bayan yagama siya aka sakamasa a mota yabiya kud'in sannan yashiga motarsa yafice,
Daganan Kai tsaye k'auyen Raha yadosa.Tafiyar 30mnts yai kamin ya'isa garin na Raha, tin a hanyar shiga garin yafara cika da mamaki, sbd ganin yanda komai yacanja, gine gine nazamani gakuma shaguna akan titi manya masu girman gaske, ciki hadda k'atuwar plaza mai kyan gaske wocca kuma tak'ayatarda shi ainun.
Can daga gefen titin kuma wota k'atuwar hospital ce mai suna "munawara general hospital" ganin tambarin sunan ne yasa yatino da abunda yafaru a baya, nantake abun yadawomasa a zuciya.
Cigaba yai datafiya ahankali yana tafiya acikin k'auyen wonda ya canjamasa gaba d'aya, ta tafiya yake amma yakasa gane ma inane yakebi kasancewor damacan baisan gidansu Madina ba,
Can yahango wota katafariyar makarantan boko wocce take had'e da islamiyya mai suna jab'bo international School da islamiya mai suna jab'bo malja'ussunah Raha dakuma masjid a gefensu, ko bai fad'a ba a baki tabbas a fuska school d'in guda biyu sun birgeshi dan sai kallonsu yake, ya kalli nan ya kalli can, yara y'an makarantar sunfito breakfast sai wasa suke wosunsu kuma sunashan ruwa agun pampo wosunsu kuma tsaye suke kawoi suna magana.Can yamatsa kusa da wosu tsofaffi dake zaune kan dakali yai parking sannan yafito, bayan yafito sannan yaje gunsu yamasu sallama suka amsa cikin sakin fuska sannan yacemasu "dan Allah ina tambayar gidan mallam ja'ey ne?" nan take suka kwatantamasa, amma saidai baigane kwatancen nasuba danhaka suka hadasa da woni yaro domin ya kaisa har gidan.
Nan yamasu gdy sannan yamasu alkhairin kud'i sannan yamasu sallama yafice, acikin y'an sakonni suka isa gidan, abun mamaki, katafaren gida ne DEEDART yaga yaron yatsayardashi alamar nanne gidan, wonda gidan yabashi mamaki matuka ace akwoi irinsa a wonnan k'auyen, bayan sun iso kuma yasaka yaron yaje yamasa sallama da Madina,
Yana zaune yaron yadawo yace ance woi waye Madina batanan, baifadi sunansaba saiyace da yaron "je kace zowa yaushe zata dawo?" nan yaron yasake komawa Jim kadan yadawo yacemasa "ance zatakai azahar".
D'an jimm yai nawosu y'an seconni can sannan yad'ago tareda saka hanunsa acikin aljihu yaciro kud'i yabama yaron sannan yamasa sallama da gdy shima yaron yamasa gdy sannan yafice.
Gyara parking d'in motarsa yai sannan yakwontarda sit yai kwonciyarsa tareda d'akko woyarsa yafara chart.
.......Madina kowa sunacan wojen lalle da saloon acan cikin garin bunza, ita dakuma su chuchu da shauran kawayensu dakuma jawahir,
Sunjima ssi acan dan saida akai sallar la'asar sannan aka gama masu itadai Madina komai angama mata kasancewor gobe ne za'a fara gudanarda shagalin, gobe zaai kamu, hmm reader's naso kuga yanda tauraruwor tamu tahaska, tasha jan lalle da bak'i gakuma gyaran Kai daaka mata, gakuma kalolin gyaran jiki daakamata na dilka da kurkur da halawa, gaba d'aya sai kyalli take tana woni shining tamkar tauraruwo zarah idan tafito tareda wota suna haske da kyalli.
Gakuma woni fitinannen k'amshi fatake na had'addun tirarukan tsuguno dana jiki irin na mutan kebbi da maiduguri woenda ake tsumata dasu, gakuma wota y'ar kiba datai sbd kularda ake bata acikin satin bikin dayashigo,
Gaba d'aya tafara canzawa sai kyalli take, dik inda ta gifta saitabar k'amshin dad'add'an tirarukan jiki.
Saida aka gamawa kowa kusan 4:30pm sannan dank'ara dank'aran motocin abokanan ango Dr ismail sukazo suka d'auke su izuwa gida.