CONEL AHMARD DEEDÀRT....41-42

2.1K 124 9
                                    

_*CONEL AHMARD DEEDÀRT*_

_Wattpad@Aufana8183_

   _41_42..._
Farinciki agun barrister Sadiq baaya misaltuwa, dakyar yabari aka wonke babyn aka bashi,
    Nantake gidan yacika da mutane, bayan anbama tsabtace komai chuchu yahuta, washe gari aka hada kayanta dana baby suka koma gida domin yin jego.

Acikin satin haka su Madina suka dinga zirga zirga domin shirin shagalin biki,

Ranar suna kowa yaro yaci suna Abdallah sunan kakansa mahaifin Abban sa amma suna kiransa da lamid'o, biki akai nagani nafad'a bikin manyan likitoci da barrister's, anko na musamman su Madina sukai na wota tsadajjiyar shadda galila Mai kyan gaske.

D'inkin gown sukai Mai kyau sannan sukasha make-up Mai kyau wonda teemah make over tamasu, mutanen yola adamawa wato family na mijin chuchu dik sunzo sai Shan shagalin biki ake,
  Hakama abokanan barrister Sadiq na nesa dana kusa dik sunzo, sun had'e dasu Madina sai farinciki ake ana shagalin biki atare.

K'asaitaccoyar liyafa abokanan Sadiq suka hadawa Sadiq d'in da chuchu dakuma kawayenta, 2pm dot aka fara gudanarda liyafar a katafaren holl d'innan Mai suna Royal event, a nan ne d'aya daga cikin aminan barrister Sadiq yamak'alewa Madina,

Tinda yakyalla idonsa yaganta yakasa d'aukewa, nantake yama Sadiq magana, shikuma Sadiq yama chuchu magan, itakoma chuchun tamata magana, dafarko bata mayarda hankaliba saida tagafa barrister Bashir dagaske yake sannan tad'an fara mayarda hankalinta gunsa.

Dik shagalinda akai na bikin itace best friend ta chuchu shima shine best friend na Sadiq, sbd haka abun yak'ara amarshi ssi, wojen liyafar ma haka yamak'ale mata dik inda take yana manne da'ita, gashi tabaro jawahir a gida gunsu maijiddah, sai abun yak'ara bada color.

Tin tana jajjaye masa harta fara bada gari bori yahau, sbd tafahimci abubuwa da dama a tattare dashi a d'an zamanda tayi dashi week dinnan.

Bayan angama liyafar suka d'aukesu suka maidasu gida,
    Bayan angama bikima bai bartaba, yacigaba da kiranta a woya suna magana, a sannu a sannu har shak'uwa tafara shiga a tsakanin su.

Kan kace me tini Bashir yafurtawa Madina kalmar so, dafarko kin karb'an tayin soyayyarsa tai Saida taja aji ssi harnatsawon wata biyu kamin ta amsa tayin soyayyarsa.

Nantake suka fara gudanarda soyayya wocca take cike da tsabta.

Bashir kyakkyawa ne black beauty Mai kyan gaske, yana d'anda tsayi amma ba ssiba sannan yanada cikar jiki kamar DEEDÀRT, haifaffen kasar jigawa state ne aikine yakawosa nan kebbi, kuma aikinsu iri d'aya da Sadiq wato lawyer kuma bashida aure yanzune yakeso yayi idan Madina tabashi dama.
   _______________________

Kamar kullum kwonce take akan makeken gadonta sanye da wando da riga kayan bacci, pillow ne acikin k'irjinta tarungume sa kyam, woya kuma tana manne a kunnenta da'alama dai woya takeyi.

Woni yolwataccen murmushi tai wonda ya bayyanarda fararan hakoranta dakuma dimple d'inda yake manne a kuncenta yalotsa,
    Ji nai tace "uhum...nidai a,a gsky bayanzuba, ka k'ara hak'uri har nanda d'an woni lkc, woima meye abun sauri aciki, nagadai ni takace kuma mallakinka insha Allah, nariga namallaka ma kaina, Kai nakeso nafad'a ma nakuma sake fad'a, so banga abun sauri aciki ba,

Abba na yatafi saudiya aikin hajji, so kayi hkr harya dawo sannan nasamesa namasa maganar" dagacan b'angaren yace "uhm...shikenan, ammadai gsky naso nanda sati uku nazama ango, woi bakisan nafara tsufaba, yakamata kiji k'aina kitaimakeni, kifiddani daga d'akin gwobrancinda nake" murmushi tai sannan tace,

"Ka k'ara hak'uri, komai yakusa zowa k'arshe insha Allah" gwobron numfashi yasauke sannan yace "shikenan, Allah I nunamana lkcn" tace ameen sannan yace "kije ki kwonta, dare yatsala nasan kuma gobe kinada aiki a office" d'an murmushi tai sannan tace "ohk...gud nyt" shina yace "nyt too my love, have a most sweetable and nice slp, Love u with all my heart, love you so so much".

CONEL AHMARD DEEDARTWhere stories live. Discover now