_*CONEL AHMARD DEEDÀRT*_
_Wattpad@Aufana8183_
_39_40...._
Kamar yanda DEEDÀRT yafad'a mata kowa hakan takasance, washe gari around 2:30pm deen da momy sukayowa su jawahir rakiya har gida, Madina taji d'adin hakan da momy saima tafarajin kunyar momyn.Liyafa tamusamman Madina tasa akamasu, atare dasu momyn sukaci suka sha sukai hani'an, 4pm bayan sunyi sallar la'asar sukamasu bankwana suka fice,
A d'an zamanda jawahir tai ataredasu kowa Alhmdllh tafara sanin su momy hartadan fara sabawa dasu, washe gari kuma suka koma school.
_______________________Sannu ahankali rayuwa tacigaba da tafiya, inda Madina takammala takabar mijinta Dr Ismail, bayan sungama takabar sai aka raba gadonsa akabaiwa magada, Madina tasamu mak'udan kud'i da mota d'aya dakuma wosu k'adarorin,
Bayan anbata nata saita biyawa kanta da jawahir dakuma abban ta umrah suka tafi atare.
........................Alhmdllh DEEDÀRT yaworke daga jinyarda yai, kuma Alhmdllh nasara tasamu dan ya murmure ssi yaworke sarai harda y'ar k'iba yai, Saida yai 1month cif sannan aka sallamesa daga hospital, bayan yakoma gida kuma akacigaba da kula dashi cikin kulawa.
Madina suna wojen gudanarda umrah DEEDÀRT yacike form d'in soja harya tafi shi dakuma Saif babban amininsa kuma yaronsa dan duniya bashida amininda yakai saif,
....Saif yasan komai nasa, yariga yasaba dashi danhaka yanzuma bazai iya tafiya wonnan aikinba batareda shi ba.Bayanda momy bataiba akan karya tafi wonnan aikin na sojohn tace "haba DEEDÀRT, dika dika yaushe ne kasakko daga kan gadon asibiti dahar zaka cike form d'in soja harka tafi, kokamanta likitoci sunce kana bukatar hutu kuma kadayi woni aiki na k'arfi ssi, sbd d'inkinda akamaka acikin jiki, haba DEEDÀRT kada soyayya tarufema ido kaje ka illata kanka".
Cikin fara'a yacemata "momy na, indai akan Madina ne, to Koda zan rasa rayuwata ne tinda tace tanasan wonnan soja d'in, to yazama dole kowa agareni naje nazama soja kodon nafaranta mata nakumayi k'okarin cusa soyayyata acikin zuciyarta, sbd haka ki kwontarda hankalinki, insha Allah ma babu abunda zai faru, zanje cikin aminci nakuma dawo cikin fara'a".
Bayanda taiya badan tasoba dole tabarsa sbd taga giyar soyayya nad'ibansa yakumayi nisa acikinta bayajin kira, haka tabarsa ya tattara kayansa ranar asabar da safe suka fice.
Yaso yakira Madina lkcnda zasu fice amma ina bashida contact dinta, haka yatafi batareda yagantaba kokuma sunyi woya,
Yatafi soja ne da zimmar daya dawo sai ayi bikinsu shi da Madina abar k'aunarsa.Bayan sati biyu da tafiyarsu su Madina suka dawo gida Nigeria, itakama tini tama manta da labarinsa sai sabgoginta takeyi da y'arta dan zowanda ma tayi can saudiya umrah harda kayan siyarwa tasiyo, gadaje dakuma kayan d'aki da bedsheets kala kala masu kyau,
Saidai momy kam dik kusan bayan kwana biyu ko uku takan Kira su gaisa sannan tayi woya da y'ar jikarta, sannan dik bayan d'an lkc takan aikowa da jawahir kud'i, dakuma kayan amfani na rayuwa, dakuma kayan wasa kala kala na yara mata, hakan kowa bak'aramin d'adi yakewa Madina ba,
Sbd dik Mai San jawahir to itama masoyinta ne, dan jawahir itace farincikin ta.
_______________________Ahankali rayuwa tacigaba da gudana cikin jin d'adi dakuma farinciki, Madina tini takoma bakin aiki, hakama jawahir takoma school, su maijiddah ma sunkoma school suna cigaba da karatinsu, danhaka yanxu rayuworsu suke cikin jin d'adi dakuma wolwola, Madina yanxu babu abunda ke damunta.
Bikin chuchu yazo danhaka suka zage dantse akasha buduri da chasu, mijinta barrister Sadiq d'an asalin garin jihar adamawa ne, aikine yakawo mahaifinsa garin kebbi har suka zama yan gari,