CONEL AHMARD DEEDART....9-10

2K 133 4
                                    

_*CONEL AHMARD DEEDART*_

_Wattpad@Aufana8183_

_9_10_
Acikin kwanakin kowa aka cigaba da aikin ginin companyn DEEDART wonda dik ma'aikatan companyn sane keyin aikin,
Shikowa tini yahaura yabar k'asar yakoma Cyprus dama shi baicika zama a Nigeria ba idan kagansa to woni muhimman aikine yazoyi daya gama kuma zai tattara yakoma can sbd acan babban office d'insa yake.
  ________________________

Cikin ikon ubangiji iyayensu MUNAWARAH had'e da y'ar uworta MADINAH kebata cikekkiyar kulawa domin ganin tarage damuwa akan abunda yafaru da'ita,

A b'angaren MADINAH kowa tini tafara shirya makaman yak'inta domin yak'ar DEEDART dama dik woni dayake da hanu acikin zalincinda yake aikatawa,

Kamanin wata d'aya cif MADINAH tad'auka suna hutu daga bisani kuma hutun nasu yakare danhaka ta shirya ita da MUNAWARAH suka koma school dansuma yanxu ne zasu fara karatun, cikinta kuma sai girma yake dan yanzu yashiga wata na biyar,

Aranarda suka iso birnin kebbi gidansu chuchu suka fara sauka dake shiyar sarakuna, washe gari suka fita inda sukaje kasuwa MADINAH tayowa MUNAWARAH siyayyar kayan sakawa sababbi, manyan hijab masu girma tasiyo mata da abayoyi dawosu rigunandai woenda Mai ciki zata iya sakawa batareda ta wohala ba, saikuma abinci kalar wonda takeso da abinsha, sannan tasiyo mata nik'ab, daganan bayan sungama suka fice gidansu susi inda suka wuni acan sai dare sannan suka koma gida.

Bayan kwana biyu anbude masu hostel sukaje suka biya kud'in hostel d'in dakomai sannan suka tattara suka koma school d'in,

Sannu ahankali MUNAWARAH tafara karatinta cikin nutsuwa da wolwala yayinda MADINAH dasu chuchu ke kula da'ita ssi, dik woni motsi nata suna kula dashi, dik sadda zataje class saita saka hijab har kasa sannan tasaka nik'ab daganan su MADINAH su raketa sannan sukuma sufice nasu class d'in,

Dik bayan kwana uku ko hud'u kuma saisun fita da'ita guraren shakatawa domin debe mata kewa da hanata yawon tinani sbd kar ya haifar mata da wota matsala kuma,

Karatinta kam Alhmdllh yana tafiya dai dai bawota matsala,
Izuwa yanxu kuma cikinta yakai wata takwos yafito hakan yasa MADINAH takara himma wojen cigaba da bata cikekkiyar kulawa.

    Kamar kullum yau takasance Sunday weekend suna hostel ba lecture yau,

Kwonce take akan bed d'in susi kanta na akan cinyar chuchu MADINAH kuma nadan mammatsa mata kafafuwonta sbd sunfara yin kaba nauyin cikin yafara sauka, danyen dabino ne a hanunta tanaci sunashan fira suna dariya,

Dikansu kayan bacci ne a jikinsu dan basu woni jimaba da tashi daga baccin,

Susi ce kemasu girki tana dafa masu indomie da kwoi, bayan tagama saita zubo akan faranti sannan tahada masu tea Mai kauri, bayan tagama saitace "to..dik wonda yatashi ci saiya sakko, wonda baitashiba kuma yajira harzowa anjima".

Uwor harara MADINAH tawurgo mata kamin tace "to su acici mala'ikun tamna, anki ajira d'in" chuchu ta kyalkyale da dariya ita da MUNAWARAH, itakam MUNAWARAH sakkowa tai ahankali susi ta taimaka mata tasakko sannan suma su MADINAH suka sakko suka fara ci,

Bayan sungama sannan sukai wonka kowa ta shirya acikin gown da k'aton hijab har kasa MUNAWARAH tasaka nik'ab sannan suka fita acikin motar susi,

Kai tsaye azbir center suka nufa inda sukasha ice-cream sukaci pizza da shawarma sukasha juice sannan sukai pictures,
Sund'an jima acan daga bisani suka fice gidansu susi, acan suka wuni sai dare sannan suka koma school.

Haka suka cigaba da rayuwa a school d'in inda suke bama MUNAWARAH kulawa ssi,
     Sannu ahankali cikinta yashiga wata na tara watan haihuwa yayinda kuma suka fara zana jarabawan zangon farko, su MADINAH kowa aka turasu IT a Sir. yahaya memorial hospital dake nan cikin garin birnin kebbi, danhaka suka tattara suka koma gidansu susi da zama kullum saisuna kawo MUNAWARAH sukuma saisu fice hospital.

CONEL AHMARD DEEDARTWhere stories live. Discover now