_*CONEL AHMARD DEEDART*_
_Wattpad@Aufana8183_
_37_38..._
Cikin gaugawa aka gama kammala komai domin yin aiki wa DEEDART,
Bayan ankammala komai sannan aka canja masa kaya domin shiga dashi operation.A kwonce yake sanye da oxygen a hancinsa wonda yake taimaka masa wojen numfashi acikin theater room dan tini aka shigo dashi yanxu isowar likitoci kawoi ake jira, ahankali yacire oxygen d'in jikinsa na makyarkyata yacewa yad'ago ahankali yacewa dady dake kusa dashi,
...."Dad..daddy in..inaso naga y'ata jawahir, domin nasan matukar bangantaba a yanzu to bazan sake ganinta ba, sbd nasan ni tawa tazo karshe, mutuwa zanyi dad..."Bai k'arisaba dasauri dady yarufe masa baki cikin tsintsar tausayin d'an nasa, kwollah nazuba a idanuwonsa yafara masa magana,
"AHMARD kadaina fad'ar haka, ciwo fa ba mutuwa bane, dik tsananin zafin ciwo akan warke daga baya, sbd haka kadaina fad'ar haka kaji, insha Allah zaka worke katashi harka raini yarka jawahir" d'an murmushi k'arfin hali yana cije leb'ensa na k'asa sannan yace "nasani dady mutuwa zanyi, Koda anman wonnan operation d'in zan mutu tinda Madina taki ta amince ta aureni, wonda yanzu kuma ita kadaice zata hana zuciyata cigaba da harbawa dak'arfi, sbd itace cikar burinta dik woni magani bazai tab'a mata aikiba matukar batasamu abunda takeso ba".
Yak'arisa yana dafe k'irjinsa sbd yanajin yanda zuciyarsa ke harbawa dak'arfi dak'arfi.
Kallonsa kawoi dady keyi, zuciyarsa cike da tsintsar tausayin sa, a zuciyarsa yake fad'ar "inama ana siyan soyayya, inama ana siyan k'auna daya siyawa d'an sa DEEDART soyayyar Madina, amma kash hakan bazata tab'a kasancewo ba, saidai a rok'eta kokuma anemota.
Dady woyarsa yaciro yakira layin Deen yace ashigo da jawahir ciki, nantake kowa saiga Deen d'in yashigo d'auke da jawahir, momy kam tinda aka shigo da DEEDART har yanzu kuks take takuma kasa shigowa tagansa kamin likitoci sushigo,
Deen naisowa yasauke jawahir sai DEEDART yacire oxygen d'inda ke hancinsa tareda miko da hanunsa alamar jawahir taje yana mata murmushi, ahankali kowa ta taka taje gunsa saiya riko hanunta tareda shafa fuskarta cikin so dakuma k'aunarta,
Hartace uncl... saitaki k'arisawa tasake cewa Dady tana kallonsa da daran daran fararen idanunta irin nasa, murmushi yasake yi ahankali yace,
"Dother me, yah kike" tace "am fine" saiya sake cewa "kina Sona ko?" saita gyada masa Kai alamar Eh, murmushi yai sannan yad'ago ahankali ya sumbaceta a goshi sannan yace adoramasa ita kan gadon, nankwa deen yadorata saiya sakada hanunsa acikin nata yana kallonta, itakam kallonsa kawoi take.Anan su dady suke a zaune har Saida doctor's suka shigo sannan deen yadauki jawahir suka fita,
Acikin y'an mintina aka fara gudanarda operation d'in,
Bayan anfara dady yacewa su momy "zan tafi kebbi garin Raha gun mahaifin wonnan yarinyar ko Allah zaisa yaji tausayin halinda yaron nan yake ciki ya aura masa ita" momy tace,"Shikenan, Allah yasa kasamu nasararsu" yace "ameen, zowa dare insha Allah nakeso naisa, zanbi flyt d'in dare" nan sukamasa fatan nasara dakuma addu'ar sauka lfy.
Cikin hanzari dady yakira anema masa Visa yanzu, sannan yakira acan kebbi yasanarda zowansa, cikin sauri kowa aka samu Visa card d'in, nan yashirya tareda driver dinshi da security's d'insa masu bashi tsaro suka fice izowa airport,
Dazuwansu bawoni b'ata lkc jirginsu yad'aga izowa kasar kebbi state.
Tafiyar kusan 3hrs suka isa kasar ta kebbi state, suna saukowa driver's na isowa, nan suka d'aukesu,
Kai tsaye garin Raha suka fice, inda sukai tafiyar kusan 30mnts kamin su isa garin na Raha.Lkcnda suka isa dai dai lkcn ana Kiran sallar magrib, danhaka suka fice masjid domin yin sallah.
Bayan angama sallar suka fito, sai dady yasami woni dattijo dai dai tsaransa dai wonda shima atare sukai dallar, bayan sunyi sallama sun gaisa sai dady yacemasa "am mallam, dan Allah woni bawan Allah nake tambaya Mai suna mallam ja'ey mahaifin Dr. Madina wocca take aiki a asibitin jawahir special hospital a garin birnin kebbi" murmushi mutumin yai sannan yacewa dady,