CONEL AHMARD DEEDÀRT...43-44

1.9K 117 8
                                    

_*CONEL AHMARD DEEDÀRT*_

_Wattpad@Aufana8183_

   _43_44....._
Sannu ahankali lkc sai karatowa yakeyi, gaba daya ahalin biyu dik sai shirye shiyen tarban hamshak'i kuma k'ayataccen bikin ake.

Tini umma meroje tafara gyaran y'arta da tsume kala kala dakuma kazar amare wocca akeyi, haka kuma wonkan lalle da dilka da kurkur shima ba'abarshi a baya ba, dik yimata takeyi,
      Har aka shigo satin bikin Madina bata bari tasake had'uwa da DEEDÀRT ba, dik yanda yaso suzauna domin yaji daga bakinta yanda takesan shagalin bikin yakasance amma tak'i, Koda yazo dakansa har kebbi bata yarda su had'u, haka yahak'ura yakyaleta.

A can b'angaren shi angon, komai sungama na Shirin biki damuka taryan amarya, daya daga cikin shahararrun gidajensa dake cikin garin habuja ne akaima sabon gyara, inda aka kyalkyale gidan yadawo tamkar yanzune aka ginasa, dikda bawoni dadewa yaiba da ginawa,

Gidan hawa biyu ne wato upstairs, a kasa ne babban parlor yake da toilet da babban kitchen da dakunan masu aiki guda uku, a sama kuma 3bedrooms ne da parlor daya wonda yake d'auke da k'aramin kitchen,
       Dik wonnan k'aton gidan DEEDÀRT yacewa abban Madina baya bukatar Koda tsinkensa acikin gidan sbd komai yagamayi, gaba daya kayan gidan ordering nasu yai daga kasar italy, kuma komai nacikin gidan Royal ne.

Main parlor gaba dayansa da abunda ke cikinsa milk and silver color ne, shikuma parlon sama purple and white color, hakama sauran d'akunan kowonne danasa kalan.

Saikuma batun event event d'inda zaayi, dika dika saif da Abbas suka yanke event daya kacal zaayi, shine dinner, yayinda sukuma kawayen amarya sukace a,a hud'u zaayi kamu, fulani's day, walima, dinner saikuma doctor's day wonda abokanan aikinta likitoci suka shirya, wonda zaayi da safen ranar d'aurin aure, da dare kuma ayi dinner.

Bayanda su saif suka iya dole suka kyalesu tinda sudai burinsu a d'aura aure akawo masu amaryarsu.
   .......................

Kamar yanda su cool Susi suka tsara haka kowa akayi, dan Koda aka bugo invitation card haka aka rubuta,
     Bayan ankawota su cool Susi ne sukaita faman rabawa mutane ita, dan ita gogar ko kallon IV din bataiba barema hartai zancen rabonta.

Su umma meroje kowa sai faman gyaran amaryarsu sukeyi, inda wosu had'in takesha, wosunsu kuma tazubar idan bakowa a kusa da'ita, sbd ita tace aurenda bana soyayya ba bakuma na so da k'auna ba miye nawoni wohalanda Kai dashaye shayen kayan mata, Koda ma taje gidansa dole d'akinta daban, nasa daban.

Hmm Madina kenan, woennan mazajen na wonnan zamanin ne zasu yarda dahakan, hmm to gamu gani idan aramma DEEDÀRT zai aminta da hakan,Lol.
    ________________________

Ranar laraba around 10am maiyin kunshi tazo tama amarya da k'awayenta dakuma sauran mutane sannan akama jawahir, Madina ja da baki akamata, yayinda itakuma jawahir akamata ja, suma su chuchu akamasu jan,
     12pm kuma sukaje gun saloon inda akamata gyaran Kai sannan akama jawahir kitso mai kyau, sukuma su cool Susi sukayi gyaran Kai suma.

A ranar laraban ne aka fara gudanarda kamu akatafaren gidan Madina, kawayen momyn DEEDÀRT dasu momyn Abbas ne sukaje kamun daga b'angaren ango, saikuma su hajiya farida da hajiya bilkisu da dai sauran mutane woenda suka fito da gidansu dadyn DEEDART wato goggonnin DEEDART kenan.

Ango da abokanansa basuzoba su hajiya farida ne suka wakilcesa, kamune akayi nagani na fad'a, ankashi naira agun kamun tamkar baasan zafinta ba, anantake hajiya bilkisu tabama Madina kyautan tsaleliyar mota sannan tamata lik'in naira dubu d'ari biyar na dollars, sannan hajiya kakarsu DEEDART ta aikomata da sak'on akwati daya wocca take a cike da kayan ado kala kala na mata da tiraruka irin na larabawa dakuma humrori kala kala, hakama wota gwoggonsa wocca bata samu zowaba ta aiko mata da key car sabo gal dakuma sarkan gold da awarwaro masu shegen kyau da tsada.

CONEL AHMARD DEEDARTWhere stories live. Discover now