*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*ATK ADMINS PALACE.**TRUE LIFE STORY.*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*Hhhhh Ban San yadda zanmuku bayanin zagin da Imamu yashaba tsinuwarku kad'ai ta Isa tayi wuji-wuji dashi, akwai* *wad'anda ma naji sunacewa sun tsani mai suna Imamu, to karfa kumanta Imamu bashine sunanshi nagaskiya ba, sannan bayi labarin Dan mata su* *tsani mazaba a'a nayine domin kufarka ku Kuma farga da halin samarin bana.*
*Ina gaisheku masoyam littafin KILALLU kuji dad'inku wannan page d'in nakune.*
*SHAFI NA 4📑*
*__________📖 To haka dai rayuwa ta dunga tafiya yayin dakomai ya dunga shud'ewa, inda abubuwa suketa canzawa sa'in da lok'aci ya dunga tsula gudu, yau da gobe tafi k'arfin wasa, Hausawa sukace yau da gobe kayan Allah, d'an adam ya tsula tsiyarshi ya manta yacigaba da cin duniyarsa, domin aganinshi dama tunaninshi kamar yadda ya manta haka Allah ma zaimanta, *WAMA KANA RABBUKA NASIYYA* haka abin yake Ubangijinmu bazai tab'a zama mai mantuwaba, abun ba hakabane Allah baya tab'a manta komai kazalika baya yafe laifin wani akan wani, lalle Allah shine sarkin adalci baya cuta Kuma baya barin meyin cutar batare daya biya wanda aka zalunta Hak'k'inshi ba, awajanka dai abin ya wuce Amma a wajan Allah kamar a lok'acin kake shiryawa...
*SHEKARU ASHIRIN* *DA* *FARUWAR ABIN*
.... " tun lok'acin har kawo yanzu bantab'a samin wata natsuwaba haka rayuwata ta dunga garaurawa, tashin hankali da kuka ko Babu kalar sa banyi ba, Allah ya Isa ko a k'alla arana Ina juyemai tirela million d'ari, amma duk da haka bazan tab'a barinshi yayi sukuniba zanshiga rayuwarshi na tarwatsa ta, sai yayi kuka kuma tabbas zaiga azaba tunkan barinshi duniya."...
Husnarh tafad'i wasu hawaye masu zafi na anbaliya afuskarta.
Haka ragowar y'an matan suma zubar hawaye suke, d'aya daga ciki ce tayi k'arfin halin fad'in.
" Karki damu Y'ar uwa Insha Allahu zamu baki duk wata gudun mawar da kike buk'ata a garemu."...
Hawaye ta share sannan tace.
" Nashirya ya k'arshi koni kad'ai ce, domin ba gudu Babu ja sabaya aduk Abin danasa gaba, ni Husnarh nayiwa kaina Alk'awarin tarwatsashi kamar tashin boom."...
********************************
Tafe muke mu biyu dukanmu Sanye muke cikin bak'ak'en a baya do gaye har k'asa yayi da kowacce tayi rolling da mayafinta fuskarmu d'aure da k'atwa ( nik'ab) , shigarmu kad'ai idan ka kalla kasan a d'aya daga cikin kasashen larabawa muke.
Motar wani matashin saurayice ta bayyana gabanmu, koda hakan tafaru sai mukayi k'ok'arin canza hanya amma kafin hakan yar yayi saurin fitowa daga motarshi.
Fari ne sosai kuma dogone me dogon hanci haka idaninshi mayan ne, gashin girarshi kamar na mace sabo da tsananin bak'inshi da cikarshi, k'wayar a daninshi kalar goldin coulor, gaskiya yana da wani kyau mai k'ayatarwa danko a cikin jeren larabawa kasashi to ba duk kaiba sai irin mai kyannan sosai shine zasu iya karawa.
Tsare Zubaida yayi da maka makan idanunshi, wanda hakan sukasa gabanta fad'uwa matuk'a, hannumu sark'ale dana juna jan hanunta nake alamin tataho mutafi amma saitake nok'ewa alamin bazata iya tafiyarba, bani da zab'in daya wuce natsaya nima tunda bazan iya tafiya na barta ba.
STAI LEGGENDO
KILALLU. {Completed 04/2020.}
AzioneTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.