*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*ATK ADMINS PALACE.**TRUE LIFE STORY.*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*Dedicate to this page to.*
*Rahmatullah Yusuf* *( ummon Afrah) Niger, & Khadija Muhammad Bukhar (Deejamah) k'anwata 😜*'''Comment d'inku nasani nishad'i nagode da yacce kuke nuna farin cikin ku akan novel d'ina, Ina yabawa da addu'o'inku masoyana Allah yayiwa rayuwa albarka, kusha sha'aninku wannan page d'in nakune idan kunga dama kubarsu sukaranta idan baku soba ku hanasu, coz Inayinku irin totally d'innan.''' 🤩🥰
'''Masoyan KILLAKLU Karku damu ana mugun tare Insha Allahu.''' 🤝🏼
*Inajin dad'in yacce kuke nuna kulawarku gareni, Amma Dan Allah idan banyi posting ba kukemin Uzuri .*
*SHAFI NA 9📑*
*__________📖* Rasa wajan zuwa Zubaidah tayi, yayin da Zuciyarta keyimata wani irin suya, yanzu duk tsawon lok'acin da tashafe Mubashshir Bai naime taba yanzu Kuma tazo gareshi Amma Babu labari, kenan Mubashshir baya zaijuya mata.
wani irin suya da ciwo takeji a ruhinta tarasa enda zatasa ranta taji dad'i.
gidan Yusrah tanufa Dan Bata tunanin iya komawa gida a wannan halin.Tayi sa'ar saminta domin yau Babu enda Yusrah taje, tana zaune gida Sanye da banzar Shiga tana kallon BF a wayar hannunta, wacce ake Kira da Android lafceciya k'irar Samsung.
gabad'aya idonta yacanza kala sabo da Abin da takeji atare da ita.Sosai Yusrah tayi mamakin ganin Zubaidah jiki a sanyaye take kallon Zubaidah wacce tashigo tanemi guri tazauna, itama waje tasamu tazauna tana kallonta mamaki fal ranta.
Zubaidah wacce zuciyarta take Mata Babu dad'i, Bata kawo wani Abu aranta ba game da shigar dake jikin Yusrah, ajiyar zuciya ta sauk'e tare da kallon Yusrah wacce itama kallonta take tace.
" Yusrah wani taimako nakeso kiyimin Zaki iya.?"...
Fuska d'auke da mamaki k'arara Yusrah tace," Fad'i inji inzan iya."... tafad'i a tak'aice.
Iska ta furzar tare da fad'in," Mubashshir nakeso kinai momin, ko Kuma kinai momin nombar shi."
Wani abu ne taji ya soki ranta marar dad'i, wanda bakomai bane face Zallar kishi.
murya a cunkushe tak'ara na-na ta sunan, fuska a yamutse tace," mekuma zaimaki.?"...
Zama Zubaidah tagyara kafin tace," abubuwa dayawa kedai ki taimaka kinai mominshi nasan Zaki iya ai."...
Shiru Yusrah tayi tana nazarin rashin zuciya Irin na Zubaidar, kallonta tayi tare da fad'in," sai kace Baki da zuciya Zaki naimeshi mutumin daya barki cikin mawu yacin hali yatafi ya barki, dafa ban zoba Zaki iya mutuwa, Amma Babu Abin daya mai zafi yabarki Kuma tun daga lok'acin nasan baiyi wani yunk'urin naiman kiba Amma sabo da rashin zuciya kidunga cewa innaimo miki shi, gaskiya bazan iyaba."...
Tafad'i tana had'e fuska dan zancan bak'aramin b'ata Mata rai yayiba.Shiru Zubaidah tayi tana nazarin kalaman Yusrah, tabbas ita kanta zuwa yanzu abubuwan da suke faruwa da ita jitake kamar ba itaba tarasa gane kanta Sam, gabad'aya k'wak'walwarta tacanza an birkitar Mata da tunaninta yabar jikinta, wani lok'acin ma jitake kamar an canzata wasu irin abubuwa kawai takeji atare da ita tabbas zatafi yarda Kuma zatafi amincewa idan taji maganar sihiri acikin lamarin nata.
VOCÊ ESTÁ LENDO
KILALLU. {Completed 04/2020.}
AçãoTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.