[4/19, 19:50] Dr Fayeex: *°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.
*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.
*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.
*TRUE LIFE STORY.*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 21📑*
*__________📖* Mubashshir ne zaune yana faman Jan carbi, tun da wowarshi daga masjid yake aiki d'aya.
enda jiran futuwar matarshi kawai yake dan yayi mata sallama Amma shiru kakeji gashi gari har yayi haske.Mik'ewa yayi tare da k'arasa shirinsa, kiching ya Shiga tare da samarwa cikinshi Abin da zaici duk da bawani dad'i abin ci yake mai ba a wannan time d'in.
Sai da yagama Abin da zaiyi tsab, Amma Zuhrah tak'i fitowa Sam.
D'aukar jakarshi yayi wacce ya zuba kaya kala uku a ciki sai abubuwan dayasan zai buk'ata.K'ofar d'akin ta yaje ya fara knocking, Babu bugun da baiyi ba Zuhrah tak'i bud'ewa.
Har zai tafi sai yaga rashin dacewar hakan Kuma yadda zuciyarshi ke mashi zafi balalle shi ya iya jure hakan ba.Wayarshi ya d'auka ya Shiga kiranta, namma tak'i d'agawa bayan tana ringing shi kanshi yana jin k'arar wayar Amma sai yaji tayi tsaki ta kashe kiran, kukane Mara sauti ya k'wacewa Mubashshir cike da taushin lafazi yake fad'in.
" Haba Habibtie na, ki daure ki bud'e k'ofar Sallama zanyi maki ba wani abuba Dan Allah ki bud'e."...Tana jinshi Amma tayi fuska.
Yana bud'e data ya ganta active in online tana kai k'yar dan ko sauk'a batayi.
Jiyayi zuciyarshi ta dad'a cin kushewa zafi yakeji har cikin k'ok'an kanshi , tabbas ko shakka Babu ya dad'e da gane Zuhrah ba sanshi take ba Amma tsananin son da yake Mata yakasa gane hakan.
Murmushi yayi Wanda kana gani kasan na bak'in cikine d'aukar a jakarshi yayi Dan barin gidan.
Kamar Wanda zai bar gidan na har abada yake Kuma k'are mashi kallo tare da jin wani Abu Wanda bai san ma'anar shiba.
Idonshi ne ya sauk'a kan k'aton hotansu na bikinsu daya cinye Rabin bangon parloun, gefa guda Kuma ga nashi ta d'aya gefan ma gana Zuhrah.Gani yayi tayi mai wani irin mugun kyau, batare daya saniba ya k'arasa tare da d'aukar hotan ya k'urawa ido Yana kuka Yana fad'in.
" Ina sonki ya Habibtie na, idan har Allah ya aramin rai zanyi iya yina wajan ganin kin aminta dani, sai dai ban saniba ko Ina da raban ganin lok'acin."....kamar Wanda aka tsikara Kuma ya maida hotan mazauninshi Yana fad'in.
"Astagfirillah ya Allah kaya femin, Ya Allah kaji k'aina.".... Yana kuka ahaka harya fita harabar gidan yasa jakar cikin motarshi, har zai Shiga sai ya sake komawa ko Allah zaisa ta bud'e Amma tak'i, haka ya dawo tare da Shiga motar Yana kuka Dan gabad'aya duniyar ta dad'e da siremai.Numbar Zubaidah ya dunga Kira sai da tayi ringing tara ta d'aga tana tsaki tana fad'in.
" Wai Kai wanne irin maye ne?, Tun jiya ka dage sai kirana kake bashi kake binane.!!?"... tak'arashe maganar cikin daka tsawa.

YOU ARE READING
KILALLU. {Completed 04/2020.}
ActionTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.