12

917 50 1
                                    

Check out Gaskiya Writers Association. (@GaskiyaWriters): https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09

*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
     *1441H/2020M.*
   
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼*


*SADAUKARWA GA:-*
*ATK ADMINS PALACE.*



*TRUE LIFE STORY.*


~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

*Dedicate this page to Fatimarh Muhmd Bukhar ( aunty Ameerah).*

'''Kin Shiga zuciya ta kin zauna Meerah, bani zuma taso da k'aunarki nai maki wak'a yanzu-yanzu.''' 😊😊😊

*My Ukuty Meeerah inayinki k'awa Kuma aminiya Allah ya barmu a tare, wannan page d'in nakine tawan Allah ya barmu a tare da juna Ameeen.*

*SHAFI NA 12📑*

*__________📖* Baccine mai mugun k'arfin gaske ya buge Mubashshir, sai kusan Magrib  ya farka .

Tana zaune akan 3 star hannunta rik'e da waya tana karanta wani BN (blue novel).

Domin Zuhrah a rayuwarta tana san batsa ita kallo zatayi tafison kallon batsa hakama karatu, dan a wajanta indai abu Babu batsa to bashi da amfani Kuma kallonshi ko saura rarshi duka b'ata lok'aci ne.

  Mubashshir ne yayi Sallama, hanunshi rik'e da a kwatin k'anwar shi wato Siyama.

Da fara'a Zuhrah tad'ago dan amsa sallamar shi, Amma ganin Siyama a bayanshi wacce sai a lok'acin ita take sallamar ta murtike fuska domin jin wani haushi tayi ya rufe Zuciyarta.

Mubashshir Wanda gabad'aya jikinshi yagama mutuwa lamarin duniya yagama jigatashi Zama yayi daga gefan Zuhrah tare da aje a kwatin dake hannun shi, cike da k'arfin hali ya nunawa Siyama d'akin da zatakai kayanta Wanda yake a matsayin nata d'akin.
     Haka ta d'auki a kwatin tashiga jiki Babu k'wari na yacce Zuhrah tanuna kamar ma Bata tab'a ganin mai irin zubin halittar taba.

Jinginar da kanshi yayi a jikin kujerar da suke zaune Yana mai da a jiyar zuciya, a sanda a bubuwan da yaji yau daga bakin mahaifanshi suke dad'a da womai sabbi.

Saurin danne damuwarshi yayi Dan Sam bayason Zuhrah tagane komai, kallonta yayi a sanda tadad'e damai da kanta kan wayarta tanaci gaba da karatunta fuskarta murtike Babu wani alamin rahama gareta, cikin taushin lafazi yace.
     " Habibtie na, my Madam ayimin uzurin dad'ewar da nayi wllhy hakan..."...wata harara da kallon banza Zuhrah ta jefamai had'i da daka mai tsawa ta mik'e tana fad'in.
     " Mubashshir ni zaka rainawa hankali mai kake nufi na kawo k'anwar ka gidannan.?"...

Cike da mamaki Mubashshir yake kallon Zuhrah na yacce take mai magana cikin kumfar Baki kamar zata dakeshi, shi dai a iya daninshi matarshi mai hak'uri ce a kan komai Amma ya suffarta ta janja.

Zuhrah wacce ke tsaye akanshi k'ugu ta rik'e tare da fad'in," da kaifa nake."...

Cikin sanyin murya yace," kiyi hak'uri da rashin sanar dake tun farko da banyi ba, Dan Siyam a tare damu zata zau."..." Kutumar Ubancan Kai yasa, idan ka Isa mai duka ya tsinemin."...

Mubashshir ganin yacce Zuhrah tajuye sak addaba yasashi kasa magana, hakan yasa cikin  shouting da hayayaga tace.

   " Kai ka isa, wllhy nabaka awa d'aya kafi tarmin da k'anwar ka a gida idan ba hakaba wllhy sai dai ka sakeni ehhee."...tafad'i tana shigewa d'aki cike da banbamin bala'i.

KILALLU.                           {Completed 04/2020.}Where stories live. Discover now