[4/19, 19:51] Dr Fayeex: *°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**TRUE LIFE STORY.*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*Happy birthday to you my daugther A'isha Abdallah (Ayyush).🎂🎂🎂🎂🎂🎂*
'''Wishing you my Ayyasha an awesome day, with good luck on your way.'''
'''Stay blessed and happy this day, my daughter on your birthday today.'''*Allah yak'aro wasu shekaru masu albarka My shushu Allah Kuma ya maki albarka Ameeen ya Rahman.*
*SHAFI NA 31📑*
*__________📖* Agigice a kuma d'imau ce suka k'arasa ga matar su duka suna kuka ganin yacce ta jigata.
Take jama'a ta cika wajen enda aka taimaka masu wajan sata a mota, Koda suka Shiga motar Umaimah kasa driving tayi bayan ita ce da take, jikinta Ina ban da rawa Babu Abin da yake ga wani kuka da take tana had'a zuffa, Babu shiri Amira ta karb'i driving en, Nan take suka bud'e wuta sai asbiti........suna tsaka da shiri Dan suna kan dining suna cin Abin cin Rana, Gateman ya shigo da Sallama cike da ladabi yace.
" Alhaji kunyi bak'i suna bakin gate na hanasu shigowa sabo da ban San suba."...
Tsaida cin Abin cinshi Daddy yayi tare da tattara hankalinshi gareshi yace.
" Su waye mazane ko mata?, Kuma wajan wa suka ce ma sun zo.?"...
Kan shi na k'asa batare daya d'ago ba yace.
" Tsohuwace daya sai wata Mata shiyar budurwa a tare da ita sai mai tuk'asu, kuma sunce gun Hajiya suka zo."...
Murmushi Daddy yayi mai cike da dattaku batare dayaji ta bakin Matar ta shiba yace.
" Ok kai masu iso da su shigo."...
Yana tashi Daddy ya kally Mommy wacce take kallonshi fuska had'e, bata jira yayi magana ba tace.
" Haba Baban yara ya zakace su shigo bayan kasan munyiwa Rabin raina Alk'awarin zuwa asbiti idan bamu tafi yanzu ba sai yaushe.?"...
Murmushi ya jefeta dashi Kan shima yace.
" Mommyn yara bak'in ki suna da matuk'ar mahimmanci agareni dake, idan suka tafi ba sai mu tafi ba."...
Muhammad Lawan Wanda duk maganar da suke baice komai ba shima rai a had'e yace.
" Gaskiya Daddy Ina Ina goyon bayan Mommy a nan, munyiwa Rabin ranmu Alk'awarin zuwa Kuma bana tunanin a kwai bak'in da zasu zo yanzu su tafi a kan lok'aci, biyu fah ta wuce Daddy."...yafad'i Yana kallon tsadaddan agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi.
Shima Daddy b'ata fuska yayi kad'an yace.
" Yanzu dai Kuna nufin bak'in nan mukoresu, amma Kun manta da cewa bak'onka annabinka, Kuma ko ba komai kwatsaya kuga suwaye ko, sannan Alk'awarin Umaimah ni na tabbata y'ata mai fahimtace zata Mana uziri idan har ya kasance bamu Sami damar zuwaba."...yafad'i Yana kallonsu su duka.
YOU ARE READING
KILALLU. {Completed 04/2020.}
ActionTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.