13-20

1.4K 66 0
                                    

[4/19, 19:49] Dr Fayeex: *°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
     *1441H/2020M.*
   
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*FACEBOOK:-* https://m.facebook.com/GaskiyaWritersAssociation.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.




*TRUE LIFE STORY.*


~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

'''Ina gaisheku masoyana tare da Baku hak'urin jina shiru da kukayi'''

*SHAFI NA 13📑*

*__________📖* " kwananta d'aya Amma har ta fara gasamin d'an uwa, jiyafa aka kawota Amma yau a parlour yake kwance, wama yasani ko jiyamma a wajan ya kwana."... tak'arashe maganar tana gyara zaman wayar a kunnanta.

K'asa da murya kawar tata  tayi tana dariyar shak'iyanci tace.
    " Gaskiya Sahbatie (k'awata)  na tausayawa Yaya Muby, Amma Allah ya k'ara alhakin mune, wanne kalar duka ne Yaya Muby bai manaba Amma da ike sha-sha-sha ne ya zauna mace na gasashi Allah ya k'ara wllhy."...rai Siyama ta had'e kamar tana kallonta cikin fushi tace.

   " Yayan nawane sha-sha-sha, sabo da Baki da mutun ci.?"... tafad'i cikin cikin jin haushi, Y'ar gajeriyar dariya kawarta tayi Kan tace," au sorry Sahbatie mantawa nayi, Allah Yaya Muby ya ban haushi kamar wani soko ya zauna mace kamar Zuhrah na juyashi."...ya isheki haka !!!."... Siyama tafad'i cikin shouting had'i da cewa.

" Dallah can gafara munafika kawai ba gwara Yaya naba, matarshice take juyashi keko Naga saurayinki yafi ubanki a wajanki ko kin mantane.?"...
   Tafad'i tana rik'e k'ugu kamar suna a tare Kan ta d'ora da cewa," ko kin manta sanda zamu tafi makaranta ki wuce wajan saurayi?, yasaki kashe waya ai takira wani lok'acin ma tana kunne Amma kik'i d'agawa ko duk kin mantane?, Shine Kan Yayana yayi haka Zaki cemai soku sabo dake jakace."...

Gaban k'awar tata in ban da rawa Babu Abin da yake sabo da tsananin furgici cikin rawar murya tace," haba sahbatie mai Kuma ya kawo wannan zan can, Naga ke Kika kawomin Zan can Yaya Muby Kuma wallhy bada wata munufa nayi maganar nan ba Amma kiyi hak'uri idan ta b'ata maki rai."... Tafad'i kamar  tana kallonta.

Cikin b'acin rai Siyama tace.
   " Eh Dana kawo maganar Yayana ai bacewa nayi ki zageshiba, ke Kareemah tsaya kiji nifa na dad'e da gano gidanku Babu tarbiyya fad'a makine kawai banba sabo da zaman tare, Amma sabo da Baki da mutunci shine Zaki cewa d'an uwana sha-sha-sha?, To wllhy a hir d'inki, kisawa bakinki lumzami nikuma in kame nawa bakin, idan ko ba hakaba wllhy nai maki d'iban albarka ehhee."... Khareema tasan halin Siyama tas Babu Abin daya dameta yanzu zata iya yaga Mata zani hakan yasa tace.

    " Dan Allah Sahbatie kiyi hak'uri kirufan Asiri kibar maganar nan kada ai rashin sa'a wani ya jiki kinji."... tak'arashe maganar kamar zatasa kuka.

    Baki Siyamar ta murgud'a Kan tace," kanki akeji banza kawai sakarya."...

" Eh naji Kuma maye, ni dai Dan Allah kiyi hak'uri, haba Mana Sahbatie."... tak'arashe da sigar rarrashi.
    K'it Siyama ta kashe wayarta, tana Dana sanin kiranta harma da gulmar da ta kaimata, Dan Siyama haka take kamar mai tsutsar Baki in dai taga Abu saita tofa yawu a kai.

KILALLU.                           {Completed 04/2020.}Where stories live. Discover now