*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**TRUE LIFE STORY.*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*Jumma'a the best day of week* _please don't forget read surah Al-khaf_ *🕋*
*Karkumanta gobe da jibi ba posting sairanar Monday karkujini shiru.*
~Follow me on Instagram.~ ~dr.fayeeeez_m_usman~
*SHAFI NA 7📑*
*__________📖* Haka dai dak'yar suka kwasa jiki suka dawo gida inda tsoro da fargaba had'i da tashin hankali suka cika ruhin Mus'ab, yakasa sukuni kamar yadda natsuwa tak'aura gareshi, yarasa wanne kallar kallo zaiwa lamarin wai Daman maganar mutane gaskiya ce?, Wai daman dagaske duk Abin dakayi sai Amma?, Wai dagaske abubuwan dayayi bashi ya d'auka saida aka fanshi akan Y'arshi k'waya d'aya tilo wacce bai da kamarta duk duniya ita kad'aifa Allah yabashi, amma saida akasamu la'ananne kuma matsiyacin daya tarwatsa mutuncin tashi Y'ar, Ashe tsaro da kulawar dayabata bazai hana faruwar hakanba?, Yanzu duk taka tsan-tsan dayayi da ita nahanata k'awa waya sakewa ilimin Boko Shiga mutane Ashe duk abanza?, Ina anfanin ilimin addinin daya d'uramata wai Ina kyan halin da Y'arshi take dashi ada?, Ina rik'o da addinin dayasanta dashi ko duka duk abanza?.
Y'arshi k'waya d'aya tallintal!!!, Ita aka lalatama rayuwa?,wayyo rayuwa Innalillahi wa'inna illaihiraji'un Ashe tunanin dayake gagarar dayayi yaci bulis ashe yaudarar kansa yayi?, Tabbas shidai yaga sakayya k'arara an lalatamai Y'arshi asanda baiyi zatoba anrugazamai gida asanda yagama Shan wahalar ginashi, Ashe duk shekarun daka b'ata wajan bawa y'arka tarbiyya a d'ank'ank'anin lok'aci wani shege zai rugazama?, Wai Daman haka ragowar iyaye sukeji asanda aka b'atamasu yara?.
Lalle shidai yaga sakayya mafi muni asanda sam bai shirya amsartaba, Y'ar dayake fahari da ita yake tak'ama yake ganin kamar yafi kowa iya tarbiyya sanadinta yau tahad'u da sharrin *KILALLU*.
Wad'annan tunane tunanen suke sake zautar da Mus'ab, yarasa natsuwarshi sam yarasata yakasa tsai da hankalinshi waje guda danganin yagyara abin, domin shi bashi da ido kowani k'arfin dazai iya kallon lamarin, shidai abin daya sani shine wanda yaja Y'arshi harya lalatamai ita yacuceshi yagama dashi...
... Zubaidah ce zube gaban Abbanta wanda ke ikirarin kasheta idan har Bata fad'amai yacce akai tasamu cikinba, danshi yana mamakin yadda a Kai hartasamu sakewar da zatayi ciki.
Hawaye ta share domin ta tsorata da yanayin da Abbanta yazo dashi kafin tace," Abba kayi hak'uri,tun ranar dana dawo amaye harkabini cikin dare kadakeni, wanda tundaga lok'acin Baku k'ara barina fitaba.
Abin da Baku saniba shine Saurayina a ranar yabani waya Kuma nashigo da ita gidannan batare da sanin kuba, duk dare idan natabbar kunyi bacci Yana zuwa gareni wanda sai gab da Asba yake barin gidannan."... tak'arashe tare da fashewa da kuka.
Gabad'ayansu mutuwar tsaye sukayi domin mamaki yagama cikasu, sudai a iya saninsu sunaba komai tsaro fiye da tunani to garin ya-ya wani yake shigomasu gida batare da saninsuba, gaskiya babuma ta yadda za'ayi ace hakan gaskene.
Rashida wacce ke gefe tana zubar hawaye tace," k'arya kike Y'ar mak'aryata kibud'e baki kifad'amana inda kikasamu cikinnan ko yakasheki muhuta."... tak'arashe maganar cikin sautin kuka.
YOU ARE READING
KILALLU. {Completed 04/2020.}
ActionTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.