*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**TRUE LIFE STORY*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 2📑*
*__________📖* Haka Al'amari yaci gaba da gudana tsakanin Umaima da Imam,ta biyemashi har yake koyar mata yadda komai zaiwakan cikin sauk'i,Kuma akai sa'a duksa ido da tsaron gidansu Babu Wanda ya tab'a gano hakan,tomin mostly Abin da bakai tunanin faruwarshi da kaiba Sam baka tada hankalinka kanshi, inda ya kwashi ganima marar adadi,bawai jindad'in Abin da yake Mata takeba, a'a tana biyemashi ne domin ta hasaso yacce rayuwa zata juyamata baya idan harya k'i auranta,Amma ko kusa takasa samin natsuwa da Abin da suke aikatawa.
Kafin kace me,Umaima tayi wata kalar muguwar rama a tsakanin satin biyun,tarasa Ina zatasa kanta taji dad'i jitake kamar tasa amatso da auran ayi kota samu tasami sauk'i,duk da tasan Imam yagama cutar da ita matuk'a to Amma ya zatayi,fatanta shine Allah ya tsayar Mata da sharrin Imam iya haka.
Satin bikinsu ya tsaya hakan yasa kowa nagidan murna fal cikinshi,Kuma ko Ina nagidan maganar yadda bikin zai kasance ake duk da bawai party za ayiba balle denna,Amma yadda suke tsara zasu had'a walima wacce ba atab'a yin taba wannan shine maganar su A'isha duk sanda suka zauna.
Duk Abin da suke Umaima kawai jinsu take domin kwana biyu kenan rabonta da Imam Dan ko kusa baine metaba,Wanda hakan ya d'aga hankalinta matuk'a,gashi bikinsu ya rage saura kwana biyar.
Allah sarki duk da d'unbin damuwar da tashin hankalin Da Umaima take ciki Amma Babu Wanda ya hasaso haka atare da ita sabo da tsananin zurfin ciki irin nata.
Abu wasa-wasa biki saura kwana d'aurin aure saura kwana biyu Amma Babu batun Imam gashi kullum sai an tambayeta maganarshi agida, Abin da yafi d'aga Mata hankali shine Abbansu da kanshi yace Yana Kiran nomber Abban Imam d'in Amma baya samu gashi ko sanar dasu inda yai gini baiba,gashi yagama sanar da batun auran Y'arshi toba asan inda za akai Amarya ba to ai kunga Babu aure kenan,Kuma tunkan faruwar hakan yadami mahaifin Imam d'in daya fad'awa Imam yabasu mukulli da address Dan zasu fara jere,gashi danginsu na nesa harsun fara zuwa Abin har magana yamaza biki saura kwana biyu Amma ko cokali ba akai gidan Amarya ba, gashi gida sai cika yake Dan hidima ake sosai.
Hakan yasa Umaima yanke shawarar zataje har inda yake tasameshi,Bata da hukuncin daya wuce hakan,aiko yau da sassafe misalin k'arfe Tara tace zataje gidansu Husna akwai shirye shiryen dazasuyi Aiko Babu wata matsala akabarta.Tana fita ti-ti direct ta tari d'an acab'a ta hau Babu wani b'ata lok'aci ya sauk'e ta a k'ofar gidan Imamun.
Tana Shiga tasameshi yana shan sigare da kwalbar shisha itama agabanshi Koda tamai sallam Bai amsaba hasalima baiko kalletaba,kusa dashi tad'an matsa tana fad'in.
" Imam ya kake hakane kagujewa ganina bayan kasan gobe ne d'aurin auranmu,gashi ko Abbanka ba'asamu awaya,Imam yakamata ku tashi tsayefa Dan maganar aure ba Abin wasabane."...tana dasa Aya ya shek'e da dariya kamar wani d'an iska,Koda ike d'an iskan nema.
Saida yayi dariya sosai sannan yace.
" Haba Umem na,nazata missing salona kikayi,aini duk atunanina zuwa kikayi mushana,Amma saiki wani zomin da batun banza ana zaune k'alau."... yak'arashe fad'i Yana had'e fuska.

YOU ARE READING
KILALLU. {Completed 04/2020.}
ActionTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.