*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*ATK ADMINS PALACE.**TRUE LIFE STORY.*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*Jumma'a the best day of week* _please don't forget read surah Al-khaf_ *🕋🕋*
~Fallow me on~ ~Instagram~
~dr.fayeeeez_m_Usman~*SHAFI NA 11📑*
*__________📖* B'angaren Mubashshir Yana Isa yayi parking d'in motarshi ko key bai tsaya samata ba ya Shiga gida da sauri Kuma a gaggauce dan ya matsu yaji dalilin kiranshi da safiyar nan.
Dawata kyakkyawar yarinya naga yayi karo tana fitowa daga parlour shikuma yana Shiga saura kad'an su bigi juna Wanda hakan yasa gabanta fad'uwa matuk'a wayar dake hannunta saida ta fad'i batare da tasaniba sabo da tsananin tsoro.
Sanye take cikin wando white da t-shirt Blue color Wanda kayan suka matseta sosai, kanta Babu d'an kwali tayi parkin ne kasan cewar tana da gashi kunnanta sark'ale da majiyar wak'a, hannunta Kuma wanda yasha jan lalle rik'e da wayarta mai tambarin Apple a bayanta.Harara Mubashshir ya doka mata cikin d'aga murya da fad'a yace," ke mahaukaciyar inace?, ko bakya kallon gaban kine eyyye.?"...Baki Siyama ta zunb'uro gaba Kan tace.
" Ina ganin gabana mana, Yaya kai Abu kad'an sai kace zakayiwa mutum fad'a."... Tayi maganar ne cikin tsiwa, ran Mubashshir ba k'aramin b'aci yayi ba kasan cewar irin mai San girman nanne sosai, cikin d'aure fuska yace." Wai Siyam meyasa Baki da kunya ne?, Kumama bana hanaki irin wannan shigar ba?, Koke kinfi gane mutum yaita maki ihu kamar wani mahaukaci.?"...
Kai ta rausayar tana k'un k'unai dan Siyama babu abin data tsana irin fad'an Mubashshir data kurar da yake mata kan kawai tana k'anwar shi.
" Magana nake maki.!!!."... to kayi hak'uri."... tafad'i cikin ladabi dan yacce taga yanayin shi ranshi a ɓace yake zai iya huce fushinshi a kanta." Kiyi sauri kisa Hijjab d'inki, ki had'a kayanki kafin nagama abun da zanyi dan tare zamu wuce."... yafad'i Yana shigewa batare daya jira amsar taba.
Siyama wacce ido warwaje take fad'in," in had'a kayana kuma.?"...banza yayi da ita yayi shigewarshi ciki.Siyam rannan nata Babu dad'i tawuce d'akin ta tare da fara had'a kayanta Dan dama yace Yana aure gidanshi zata koma, wani b'angaren tana murna kasan cewar tana bala'in san Zuhrah domin tana burgeta wani kuma b'angaren tana tausayawa kanta wahalar da takurar da zata k'ara riskar kanta.
Suna zaune akan kujerar mai cin mutum uku, kallo d'aya zakayiwa foskokinsu kaga tsantsar dadtijan taka da dadtaku shinfid'e saman fuskokinsu.
Tsugunnawa yayi tare da gaishesu amsawa sukayi cikin jin dad'i su duka biyun.
Waje yasamu shima ya zauna Zama mai cike da ladabi tare da Sunkuyar da kai.
Zama Sa'eed ya gyara tare da gyaran murya kan yace.
" Kaji Kiran Ummanku dasassafe haka ko.?"... ahankali Mubashshir yad'ago kanshi tare da furtar," eh Baba."...
" To Masha Allahu, da Allah ya nuna Mana wannan ranar da muka sauk'e nauyin ka akanmu, na baka ingantacciyar tarbiyya da mukayi da ilimi tare da kula tun zuwanka duniya har kawo yanzu to Masha Allahu."...
Yafad'i Yana sauk'e a jiyar zuciya da badun ya k'arashe maganar shiba da'alama yanajin nauyin maganar da zata biyu baya.
KAMU SEDANG MEMBACA
KILALLU. {Completed 04/2020.}
AksiTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.