5

988 95 5
                                    

*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
     *1441H/2020M.*
   
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼*


*SADAUKARWA GA:-*
*ATK ADMINS PALACE.*



*TRUE LIFE STORY.*


~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~


*SHAFI NA 5📑*

*__________📖* Tundaga nesa Mus'ab yake hango Y'arshi Zubaidah wacce ke tafe kanta sunkuye, murmushi yayi tare da kawar da kanshi gefe, Hummm tabbas shidai yagama cin ribar duniya kuma itama Lahirar adai jira yasan dole nema saiya cinye duka daga duniyar har lahirar, tunda shidai ya kula Yana da kyakkyawar sa'a a rayuwa, duk tsiyar daya shuka Amma Allah bai hana bashi y'a kamilalliya ba wacce natsuwarta da kamin kanta ke tafiya da imanin mutane, wacce kaf anguwar da suke babu shakka yasan zaiyi wahala asami wata y'a mai kwatankwacin halin Y'arshi.

   Ko da'ike shiyafi tunanin yacce ya tsaya akan Y'arshi yasa ido akanta dolenema tayi tarbiya ingantacciya, shiyasa  duk acikin tsayuwar tashice ya yanke shawarar aurar da Zubaidah.

Sallamar Zubaida ce takatse Abbanta tunanin dayake, tsugunnawa tayi tare da gaisheshi kai sunkuye, ansawa yayi kan ya numfasa yace.

   " Baby daman inaso muyi wata maganace dake, dafatan kin shirya.?"...

Kanta sunkuye tace, " eehh Abba nashirya."...

Zama ya gyara tare da fad'in," kinsan Ziyad ko.?"... Ya tambayeta yana kafeta da ido.

" Eh."... Tasake cewa kanta sunkuye.

   " Toshi zan aurawa ke, kuma minyi magana dashi harda iyayanshi kuma Alhamdulillah komai yatafi dai-dai, inda mungabatar da komai saura d'aurin aure kawai wanda za'ayi watanni biyu masu zuwa.". ..

Shiru Zaubaidah tayi kanta nak'asa tana nazarin irin takurar da mahaifinta kemata, sam itaba bata dawani sakewa tun tasowarta baya barinta mu'amala Koda k'awayen tane shiyasa duk da birge mutane da take bata dawasu k'awaye sabo da tsananin takurar iyayanta musamman Abbanta gabad'aya zata iya cewa rayuwarta a takure take.

   Yanzu kuma har auranma bazai bari tasamu wanda yadace da itaba dan rashin adalci kawai saidai yace yaba data, babu ruwanshi da ko akwai wanda takeso, lalle Abban ta yakai mak'ura wajan takurata harga Allah.

Abban tane ya katseta tahanyar fad'in," naji kinyi shiru lafiya.?"...

Idanunta tad'ago tare da makasu kan Abban nata cikin sanyin murya tace," Abba meyasa kakeson aurar dani dawurine ko akwai laifin danake makane wanda har kakeson rabuwa dani haka.?"... Tafad'i tana kafeshi da ido.

  Shiru ya d'anyi yana nazarin kalamin Y'ar tashi Kan yace," to laifine kana aurar dake dawuri naga Manzon tsira Nana Asiya tana shekara shida ya aureta ko kinmanta ne?, balle ke da ak'alla kinba shabakwai baya."...

    Baki bud'e Zubaidah tace," Abba Nana Asiya Kuma?, Kodai Nana A'isha uwar muminai."...

Cikin rawar baki wanda ke nuna jahilci k'arara yace," Au Nana Asiya ba itace ya aura tana k'arama ba."...

" A'a Abba Nana Asiya itace Matar Fir'auna wacce Allah saidaya anbaceta a littafinshi mai girma yacce tayi Imani, Nana A'isha kuwa itace d'aya daga cikin iyalan manzon Allah wacce ya aureta tana da shekara shida, ya tare da ita tana shekara tara yabar duniya tana shekara shatakwas itace Nana A'isha uwar muminai."...

KILALLU.                           {Completed 04/2020.}Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz