6

1K 65 1
                                    

*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
     *1441H/2020M.*
   
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼*


*SADAUKARWA GA:-*
*ATK ADMINS PALACE.*



*TRUE LIFE STORY.*


~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

_Daya Yanzu Har Zuwa Ƙarewar Wannan Labari Sadaukarwar sa Ta Ku Ce Gwarazan Jarumai Admins Dake ATK Palace, Kuji Daɗin Ku,Allah Ya Biya Ku Da Gidan Aljannah,Gaskiya Writers Na Godiya Da Ƙoƙarin Ku A Kanta A Koda Yaushe._

*SHAFI NA 6📑*

*__________📖* Zubaidah taci wahala sakamakon karb'ar budurcinta da Mubashshir yayi, sai dai zatace dad'in da taji yafi wahalar yawa.

Domin yashayar da ita wata irin zuma wacce badan shiba haka zaitai tazama a gafalanta.

Shiko Mubashshir Abin har tsoro yabashi yacce Zubaidah tabashi had'in kai kamar wacce ta tsufa abariki, ko bayan faruwar abin mai makon tayimai raki a'a godiya ce tashiga tsakani.

   Kuma dai gashi a zahiri budurcinta ya karb'a, Amma tana kuka tanamai godiya kamar wanda yaceto ranta daga ha'ula'i, danshi da farko yazatama idonta abud'e yakene, Amma yacce yaga komai sabo hatta yanayinta da zubinta da komai sunnunamai batasan komaiba cikin lamarin, domin shid'inne mafari.

  Hakadai sukaci karansu ba babbaka, domin Zubaidah ta manta dawata zancan Tahfeez, Dan gabad'aya ta manta kanta kwata-kwata.

To Rashida dai tsoro kamata yayi ganin har anyi sallar magrib Zubaidah Bata dawo gidaba, gashi Abin tsoran batasan inda tajeba, dan Babu wanda baisan Tahfeez d'in anguwar k'arfe hud'u da rabi ake tashiba," toko Ina Zubaidah taje.?"...

Ummanta ke tambayar kanta asanda tagama jigata da zurga-zurgar da takeyi a tsakar parlour, d'auro Alwala tayi dan sai yanzu ta tuna batai sallar magrib d'inba, ita gashi babban tsoranta kada Abbanta Mus'ab yadawo yace Ina Y'arshi.
    Hakadai tasamu ta k'ok'arta tayi sallar da rabinta tunanin halin da y'arta ke ciki take.

Tunkafin a shigo titin da zaisadaka da layin gidansu Zubaidah tayiwa Mubashshir umarni daya ajeta, gudun karsu Shiga layin mutanan babanta suganta, dan Yana da jama'a sosai.

Ziyad wanda ke Sanye cikin farar Jallabiyarshi fara tas, gabanshi ba k'aramin fad'uwa yayiba ganin Zubaidah tafito daga wata mota.

Baya ya d'anyi tare da lafewa jikin wata mota, k'uramata ido yayi danya tabbatar Zubaidan ce ko-ko kamace.
   Zubaidah ce dan kamarta da komai sun tabbata.

" To waye wannan.?... Ziyad ya tambayi kanshi afili, Dan sosai yacika da mamakin ganin Zubaidah tare da wani.

Kasaitaccan murmushi Mubashshir yayi tare da kallon Zubaidah wacce tagama kici-kicin sauk'a daga motar, ahankali yace," to sai yaushe.?"...

Dariya tad'anyi tare da kawar da kanta cikin rashin k'warin jiki tace," sai yaushe kakeson muk'ara had'uwa.?"...

Mik'a yayi wacce ke nuna tsantsar iskanci kan yace," indai tanine yanzuma kitaho mukoma Dan mud'ora daga inda muka tsaya."... yafad'i Yana kafeta da ido, murmushi tayi tare dayo waje da ido," kaiiii so kake ayankani agida, rufamin asiri kadai fad'i wani lok'acin Amma bayanzuba."... tak'arashe tare dayin k'asa da murya, danji tayi ajikinta kamar ana kallonsu.

KILALLU.                           {Completed 04/2020.}حيث تعيش القصص. اكتشف الآن