3

1.1K 75 6
                                    

*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
     *1441H/2020M.*
   
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼*


*TRUE LIFE STORY.*

~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

*Dedicated this page to my bestie na , Fatimarh Sulaiman ( Momy), inajin dad'in k'arfafamin gwiywar da kike sosai.*

*SHAFI NA 3📑*

*__________📖* Haka A'isha ta k'ank'ame jaririyar tanajin soyayyarta da mugun soyayyarta na d'awainiya da ruhinta.

Tabbas tayi kanta Alk'awarin kula da ita Koda zatayi yawo babu zanin d'aurawa, Amma Ina Koda A'isha ta iso gida kallon Ummansu tayi tasamu lafiya, batayi mamakiba domin Likita yace akoda yaushe zata iya dawowa yacce take, sabo da Daman firgicine ya kwantar da ita ba ainihin cutar bane.

Tana shiga d'akin taga Umman tasu zaune akan gado ta jinginar da kanta jikin fuskar gadon, yadda yanayinta ya nuna saika zata Bata fuskantar komai,ga Kuma babban wansu Ashir da Anas wanda shikebin Ashir d'in dagashi sai Umaimah sai ita A'ishar sai kuma k'annansu maza Mukarram da Mubarak sai twins mata wanda gab da faruwar lamarin Umman Asiya tahaifesu.

Kallon da suke aikawa A'isha dashi yasa tayi saurin Shiga taitayinta,Salma tayi masu Amma ga mamakinta sai taga Babu wanda ya amsa.

Ashir ne ya kalleta tare da fad'in.

" A'isha wato ke kinzama mai kunnan k'ashi ko?, Y'ar ragowar rayuwar tamu kike k'ok'arin ruguza mana ko.?"....

Kallonshi tayi cikin da sashiyar muryarta mai nuna tsanstar jigata tace.

" Kayi hak'uri Yaya bani da zab'in dayawuce haka."... Tafad'i tanayin k'asa da kanta yadda taga Umman tasu na aika mata wani kallon.

Anas ne ya k'wace da fad'in," kin shishigema wacce tazama sular rugujewar komai namu,yanzu kuma tahaife shigeyar kin rungumo kin shigomana da ita cikin gida."... fad'i kamar zai daketa.

Cikin shashek'ar kuka wanda kullum a cikinshi take tace.

    " Wallhy bawai nak'i  ta takubane a'a inajin tausayinta ne idan har muka juya Mata baya, kusani gina y'a mace aikine mai matuk'ar ladan gaske, ruguzata kuwa babban hatsarine ga AL'UMMA domin naga haka k'arara arayuwar Aunty Umaimah, Dan haka Dan  Allah koda bazaku tayani rik'on taba, kubini da addu'a domin wani zab'in dayarage tunda Allah yayi itad'in ta zuri'armu zata fito."... tak'arashe fad'in haka tanawani zubar hawaye maicin zuciya tare da jijjigata alok'acin da tafara kukan yinwa.

Zuba idonta tayi akan yarinyar taci gaba da fad'in

   " Karki damu Auntyna kuma y'ata zan sadaukar da komai akan naga rayuwarki tayi tsafta duk wata addu'a ta akanki zata k'are Auntyna , tuni nacire lissafin aure a rayuwata dama duk wani lissafina domin sonake rayuwar sabuwar Auntyna ta inganta, nashirya cud'anya da duk wata jarabawar da zanfuskanta muddin Ina raye da Kuma lafiya ta,  nidai Abin da nasani bazan bari ki kokaba idan har maiduka yabani iko, Zan kula dake kodan wasiyyae da Aunty na tabarmin, bazan tab'a barin kema kiyi kukaba fiye da wanda mukayi kinji Ya Umaimatah."... tafad'i tana dad'a k'ank'ame Husnar wacce zuwa yanzu da callare da kuka.

Umman Asiya wacce tayi shiru kamar bata fuskantar komai, Tari Ummansu tafara kamar ranta zaibar jikinta inda su Anas dama har ita A'ishar sukayi kanta suna aikin jera mata sannu.

KILALLU.                           {Completed 04/2020.}Место, где живут истории. Откройте их для себя