*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*ATK ADMINS PALACE.**TRUE LIFE STORY.*
~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 10📑*
*__________📖* Da ciwon kai mai tsanani Zubaidah ta tashi jitake kamar zaibar jikinta, sabo tsantsar azaba.
Tasan bakomai bane face raba daran da sukayi ita da Yusrah akan Abu d'aya, cike da dabara ta yunk'ura danyin sallar asbah.
Yusra wacce ke kwance Kan gado shame-shame babu komai jikinta ta motsa, tana kallon Zubaidah wacce yanayin ta kad'ai zai nuna tana cikin damuwa.
Kallonta tayi tace.
" Honey lafiya naganki haka.?"... tak'arashe maganar cikin sautin vacci.
Ahankali Zubaidah tace," wlhy kaina kemin ciwo, Kuma gashi sonake nayi sallah." ...tayi maganar cikin sautin dayake nuna damuwa.
" Sallah.?". ..Yusrah ta nanata cike da yamutsa fuska.
"Eh."... Tafad'i asanda kan Bata ke k'ara tsananta Mata da ciwo.
Shiru Yusrah ta d'anyi alok'acin da takejin wani ba dad'i wai sallah zatayi Abin dake yi mata yawo kenan arai Yana Mata zafi, domin Yusrah irin mugayen mutanece tunda dai ta b'ata Bata da burin da yawuce uban kowama ya kauce hanya.
Matsowa tayi kusa da ita tace," haba Honey yazaki takura akanki akan wata sallah bayan kanki ciwo yake, Kinga manta kawai idan Kika warke kyayi kinsan banasan wahalar ki ko.?"...
Baki Zubaidah ta bud'e danyin magana Amma tuni Yusrah ta had'e bakinsu waje guda taci gaba da aikamasu wani irin hott kiss wanda ciwon kan da Zubaidah ke fama dashi Bai hanata birkicewa ba...
.... Gab da Asba Mubashshir yasamu damar farkawa daga nannauyin baccin dayake, ahankali abubuwa na mamaki sukaci gaba da cikashi.
Mik'ewa yayi tare da kunna fitilar d'akin ganin Zuhrah kwance sheme yasashi sakin ajiyar zuciya, blanket d'in yaja yarufe mata jiki tare da gyara mata kwanciya, yashige toilet danyin wankan tsarki.Zuhrah najin motsin shi ta bud'e ido sai dai bata Bari ya gane idonta biyu ba.
Haka Mubashshir yayo wankanshi tare da d'auro Alwala Dan alok'acin har anfara kiraye-kirayen Sallah.
Tashin duniya Babu kalar da Mubashshir baiwa Zuhrah ba Amma tayi banza dashi yayi tashin har ya gaji Kuma idonta biyu.Haka ya kad'a kai yatafi Masjid Dan alok'acin har antayar da sallar, shima fa bawani k'aimi yayi ba wajan ibada yaune yafara kun san yace zai fara sabuwar rayuwa, shine tun yau akafara.😂
Zuhrah na tabbatar da Mubashshir yafita tamik'e tana fad'in," shige d'an iska takurawar da akamin agida kana nufin a kanta zaka d'ora?, Shege sai kace shima wani mutumin kirkine d'an bura uba kawai.".... jakar ta d'akko tare da k'ara b'allar k'wata dayawa ta zuba abaki ta kora da ruwan da sukasha ajiya da bai k'are ba.
Tana gamawa tafad'a bed bakinta Babu Abin dayake face zagin Mubashshir dawani kalar mugun haushinshi takeji, kafin bacci yayi awon gaba da ita...
YOU ARE READING
KILALLU. {Completed 04/2020.}
ActionTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.