Episode one

163 7 0
                                    

KAWANCEN MU
2017 version

*Mallaka*.....FAUMSYK FAMILY

SUMAYYA ce sanye cikin kayan islamia coffee color, kafarta Kuma sanye da safa (socks) baki tana tafiya sannu a hankali har Naga ta iso wani madaidaicin gida , ta tura gate din gidan ta shiga hade da sallama. Tura kanta keda wuya cikin palour ta hango SURRAYYA da Waya a hannunta tana dannawa, surayya ta dago kai tare da amsa sallama fuskanta yalwace da murmushi can Kuma sai tace ha'a (in a suprise tune )
blad Meye Haka Kuma na ganki da uniform? Yanxu fa nake son kiranki naji ko kin shirya ko mun fasa xua lallen ne ??hmmm sumayya tace tare da 'dofana a hannun kujera ta xauna. Wlh umma ce tace wai dole sai munje islamia yau ba ynda bnyi da ita ba fa....
Aiko baa inda xani saidai ki tafi ke kadai😒.
surayya tace tare da kwanciya Kan thrw pillow diin cushion din , ta dauki wayanta ta cgba da dannawa,
Ai wlh tunda kikaga na shirya kema sai kin shirya kinxo munje ina mummy take ... Rufe bakin sumayya keda wuya sai ga wata mata mai matsakaicin shekaru ta fito dga wanni er lungu (corridor) xua cikin parlorn. 
Mummy ina wuni,
Lfya lau sumayy ya ummanku?
Tana lfy klau ta ce wai gobe in Allah ya kaimu ki jirata Ku tafi dankin tare.
To ba damuwa.
Ke surayya baxaki tashi ki shirya ba ko sai kin ja muku latti ne?? 
Mummy nifa yau baxani ba....
Dallah tashi kona bibbigeki banasan raini da wasa da mkrnta, baxe yiwu ba ace yau laraba kuki xua sannan ran asabar ma baxaku ba .
Sanin cewa mummy bata da wasa yasa surayya tayi maxa ta mike ba shiri.
Idan kun shirya ga katin daura aure Nan Ku kaiwa headmastern Ku inji abban Ku, cewar mummy.

Bayan sun shirya ne suna tafe a hanya sumayya sai mita take wai surayya ta kusa ja musu latti. Surayya da haushi ya isheta ta waigo tace Dan Allah ni ki rabu da ni, ai duk ke kika janyo mana da kinyi wa umma bayani da yanxu muna can Ana mana lalli ai kin sani dai gobe we hav no plans for lalli a schedule din mu....
Eh ai we can create one kedai wlh blad kin cika mita inxaki dago kafa ki dago. Inji sumayya
To gudu knm kike son nayi ko me? Kuma ke kadai xaki kaiwa mallam auwal katinnan to Dan ni baxani baa banshirya shan waaxi baa a yau Kam. Inji surayya. 
Ai wlh baki isaba ai tare aka aikemu... Mgnn sumayya yayi daidai da isowarsu islamian uthman bn affan da ke u/kanawa kaduna.
Bayan an tashi dga islamian ne da misalin karfe shida saura minti goma ne sumayya da tasa surayya gaba xua office din headmaster domin kai sakon Abba . Tare suka rangada sallama tare da naiman ixinin shiga,
" a shigo"
aka basu amsa. suka cire flat shoe din da ke kafansu suka shga a tsanake fuska cike da ladabi..
Ba headmaster kadai bane cikin office din ashe , wani matashi ne xaune Kan daya dga cikin cushions din da ke office din kanshi a kasa yana duba wani littafi dak e hannunshi mai rubutun lrbci, a sace su surayya suka kalle shi kafin su maida hankalin su ga Malam auwal headmaster suka gaishe shi tare da mika mai sakon abba na gayyatan daurin aure wanda xaayi ranar asabar da yardar Allah. 
Bayan mallam auwal ya amsa ne tare da adduan sanya alkhairi daga bakinshi , ikon Allah goggonku faixa Kuma lokaci yayi kenan cikin hukuncin Allah?
Eh mallam..
To madallah inji mallam, daliban nawa hijabbin xaa sa ko gyalen ne ?? Mallam auwal ya tambaya cikin sigan tambaya Kuma ya dago kai yana Kare musu kallo..
Shiru ya biyo baya wanda acikin xuciyan surayya sai fadi take tana sallaallami tana shkn Kuma ni wlh banji dadin aiko mu da akayi ba... Ko sumayy abin da take sakawa knm suka kara jin tambayan mallam a karo na biu...
Malam duka biyun xamusa suka fada a tare hakan da suka fada shi yayi daidai da dago Kan matashin saurayin da ke xaune yana karatu, lkci daya idanuwan mutane uku suka sarke wanda yayi daidai da bugun xaciyan ko wannen su. Shikam saurayin maida kanshi yayi Kan littafin tare da hade gira ya cgba da abun da yake yi. 
SUBHANALLAHI!!! kayya kayya inji mallam auwal, Nan ko mallam abun nema ya samu ya fara kwararo nasiha akan Sam karsu yadda su bari shaidan yaci galaba akan su, Dan Allah karsu sake Susa gyale sbd ganin a gidan su ake biki.... Haka yayi tayi suko suna ta binshi da to har ya gama ya sallamesu suka fita matashin be kara dago kai ya kalle su ba...
A hanya ma dai su surayya sai mita suke wai ai mallam auwal badai sa ido ba surayya harda fadin dama in munsa gyalen ya gammu ya koremu damn na gaji da xua sai mu chanxa wata.
sumayya Kam na fadin wai kanwar mallam ma ai tana sa gyale mu duk yabi ya takura mu ( niko dai nace a'a emmata gaskya mallam ke fada muku kuji tsoron Allah a duk inda kuke mutuwa dai ci take kamn rana).
*** *** ***
Yau ta kama alhamis , enuwa da abokai sai bulbulowa suke ta koina. Lallai wannan biki ta er gata ce Kuma er dangi. Faixa itace amaryar da xa a aurar ran asabar tare da angonta Barr ibrahim mu'azzam.
Aunty faixa kanwar baban sumayya da surayya ne, itace auta a dakin su, Abdullah shine babba yanada yara shida abba, yusuf, mansoor, masuod, sai Surayya sannan ismail. 
Sai Kuma Adam na biu yanada yara biyar, akwai mahmud, sai naxeefi, sannan sumayya sai Kuma adeel da aseem (twins). 
Sai Kuma salihu wanda aka samu akasi akanshi, yaranshi guda biu ne kacal daga safiyya sai fadeel.
To daganan ne Kuma aka haifi auta faaeza. 
Abdullah da Adam da salihu da faixa dukansu yara ne ga Alh abba kyaudai. Wanda asalinshi daga wani kauye yake maisuna kyaudai karkashin hunkuyi karamar hukumar kudan kaduna state.
Chirani ya fito dashi dga kauyansu xua cikin garin kaduna tare da matanshi Hajya rabi inda suka yada xango a u/kanawa. Aikam Alh abba ya fito a saa to Dan yasamu budi sosai. yana da shaguna sosai acikin kasuwanni gashi Kuma Allah ya azurtashi da da yara kyawawa duk da matanshi rabi tana haihiwa kusa kusa ne to Dan tsakanin yaran befin shekara xuwa shekara da rabi. Daga Kan salihu ne Kuma Allah be kara bata haihuwa BA sai akan faixa wanda ita kadai ce mace Kuma akwai taxaran shekaru sha Tara xakaninta da salihu. Faixa nada shekara daya a dunia Allah Yama Alh abba rasuwa. Mutumi mai jamaa da zumunci to Dan dukda ya Tara iyali be bar xua kauyensu BA da yin zumunci da en Uwa da abokan arxiki. Duk cikin yranshi BA wanda Allah be nufa yafara ganin Kwan shi BA sai salihu da auta faixa. 
Bayan rasuwanshi BA yanda su Abdullah basuyi mahaifiyar su ta koma cikin su BA amma taki tace a barta gidan gado da diyar ta dayake musa da adamu suma duk cikin unguwan suke xaune da iyalansu. Salihu ne kadai me aikin gwamnati cikinsu inda yake xaune da iyalanshi a abj.
**** ***** ****** ** ** *

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now