episode 6

36 4 0
                                    

KAWANCEN MU.
2017

Wasa wasa dai karamar magana ta zama babba, ciwo reras ya kwantar da sumayya, hakanan ta hana kowa sukuni sai kuka. Daman ita indai tana ciwo za'a sha raki sosai ba kadan ba.
Bata ki ace duk en gidan su su taru kanta Ana mata sannu ya jiki ba, ita ko taita xuba raki da shagwaba.
Hajya kaka Kam duk ta gama rudewa, sbd ko surayya zama tayi gefen sumayya tana tayata kuka itama. Yana daya daga cikin abinda ke daga musu hankali sosai, wato ciwon daya daga cikin su. 
Ba shiri kaka ta danna kira ma adamu cewa yaxo ko yasan wanda xe turo yaxo ya kai yara asibiti. Haka abba adamu ya kira abba(jnr) da ya maxa ya je ya kaisu asibiti besan waye ba lafya cikin su ba.
Bayan abba ya iso ne surayya ta kama er uwanta har zuwa wajan mota, kafinnan suka wuce giwa hospital dake abakwa.
Bayan sun Isa ne suka tadda Dr Fatima, inda ta duba ta takuma tabbatar da malaria da typhoid ne ke damunta, inda ta hadasu da magani sai Kuma allurai da zaayi har na tsawon kwana uku. Ba sai an bata gado ba inshaallah zata warware da yardan Allah.
Gidan Hajya kaka dai suka ce amaida su anan ne xasuyi jinyan. Anan ne Kuma suka kara missing Aunty faixa cox da tana Nan ita xata dinga ma sumayya allura sbd nurse ce, amma hakanan su mahmoud xasu dinga jigilar kaisu har na kwana ukun.
Jamb matriculation bord tayi fixing ma yara masu jiran xana jamb lokaci in 2wks time,
Sumayya na cikin ciwon Nan ne taga message daga jamb office na cewa ta kara selecting state domin ganin center dinta, wanda tayi da ya samu matsala.(cld jamb b dat reckless?? Lol).
Bayan sun fadiwa abban su ne ya tura nazeefi akan yaje yayi duk abinda ya dace. Da zuwan naxeefi sai ya tadda centern kaduna state duk sun cika, sai dai ya zabi wani jahan. Sai kawai ya zabi jos Plattue state, dayake can ne garin mahaifiyarsu, daga can daddynsu ya aurota.
Ciwon kwana uku sumayya tayi, Allah ya aiko mata da shifaa(sauki) ta tashi ras kamn ba ita ba. ciwon ne Kuma yasa san basu leka islamian su ba Balle surayya ta hadu da abokin fadanta malm muhd, sumayya Kuma da mai kaunarta black......lol.
*** *** *** *** ***

Yau TA kama ranar talata, wanda ya kasance saura kwana uku ras dalibai su fara rubuta jarabawar jamb.
Da wurwuri su surayya suka shirya suka nufi islamian su. Kwana biu da suke zuwa mallam Muhammad bashi da aiki sai takalan surayya. Kiris yake jira tayi laifi yasamu hujja cewa ta mai rashin kunya. Ta Dan indai ba a islamia suka haduba, data ganshi a hanya xata fara hararanshi sanrai tana tabe baki, tadai gama rainashi. Hakan ba karamin kona mai rai yake yiba sosai. 
Saboda haka nema kullum sai yasa surayya a gaba, daya shigo aji abinda yake farawa shine canxa mata wajan xama yace ta koma can baya,idan Kuma ya musu Kari sai ya tasheta ta karanta. Duk naiman hanyan takalan fada sai yamata ita kuwa taita shanyewa. Dan dole yasa take xua islamia akan lokaci kar sbd kar yaci mata mutunci da tambayoyi.
Ta yau dinma mallam Muhammad garesu, shi Zai musu tajweed a darasin karshe(last period),
Yau mallam da kwarin gwiwa ya shigo ajin, yana shigowa ya hango surayya can a baya wato ta koma ta zauna kafin ya tasheta knm. Ya tabe baki. 
Daganan ne Kuma yace yau tambayoyi xaa yi, damn kun san na fada muku xan dinga ware ranaku na tambayoyi domin inga wa enda basa muraja'a yanxu su amsa query. Sbd haka duk wanda na Nuna ita zata amsa min tambayata.
Da haka mallam ya fara xabe , duk wanda ya Nuna shi xe amsa mai tambayan shi, in ka iya ka zauna in baka iyaba ka cgba da tsayuwa. Haka mallam ya dingayi, itakam surayya gabanta sai fadi yakeyi, hakama sumayya tasan zeyi wuya ace mallam be nuna er uwanta ba.
Har aka kusa tashi mallam ko kallan inda surayya take beyiba, haka yasa har hankalinsu ya Dan kwanta. Can suka ji yace surayya tashi! 
Ras kakeji gaban su ya fadi...
" ki fado min harfofin qalqala da muke da shi ki Kuma mun bayanin kowannen su..."
Innalillahi sumayya keta maimaitawa, tabbas ran da akayi wannan darasin basuzo islamia ba tasan blad dinta Sam bata san amsa na. Haka ta waiga tana kallanta fuska kmn tayi kuka.
Surayya tasan bata san amsan ba, Kuma ta san da gayya ya mata tmbayan Nan sbd kila ya gane basuxo ba ranan daya koyar. Hakanan ta hada giran Sama da kasa tayi shiru batada niyyan magana. 
" ke muke saurare ko baki iya bane?" mallm ya tambayaa?" 
' Eh". Surayya ta bada amsa a gajarce.
To madallah! Mallam ya fada, sai ki cigba da tsayuwa kema.
Ahaka surayya ta cigba da tsayuwa har aka tashi, to daganan ne yakira discipline master yace ya tarkatasu ya kaisu hall su share tas, duk wanda yaki sharewa shi ze wanke bayi. Inji mallam muhd. 
Ahaka aka tarkato su su biyar aka tafi dasu wajn shara. Dayake d.master shima baida mutunci, ba yanda sumayya batayi ya barta ta taya su ba amma yaki, saida suka gama share ajin Nan tas kafin yabarsu suka tafi, lkcn ma gab ake da afara kiran sallan magriba.

Surayya in ranta yayi dubu ya baci to Dan har kwalla saida tayi, a duniya ta tsani wannan malamin kamn ynda shima ya tsaneta.
" ai wlh blad nida malamin Nan mun riga munsa kafan wando daya, inda ya bata min rai tsab sai na Rama haba! Wannan cin mutuncin yayi yawa wlh" surayya ta ce.
Sumayya ma jikinta duk yayi sanyi, tanaso ta ba blad dinta hkr amma tana jin tsoro to Dan ba wannan bane lkcn daya dace. Itama dai abin da malamin Nan yayi yau ya fara isanta gskya ya kamata a taka mai burki....
Charap kakeji surayya ta rike hannun sumayya tana nuna musu black a inda ta hangoshi ya fito dga wani lungu yana nufosu fuska dauke da murmushi. Ba arxiki su sumayya suka rike hannun juna suka fara gudu kaman sun hango wani dodo, yo dodo mana tinda da wannan mangariban gari ya fara duhu black ya tare su ahanya aiko ba lafya!!
Shiko black tsaya yayi yana kallan inda suke gudu , dayake yasha ta kawo mai karo,
can dai yace 
"waini suka tserewa ne?" 
"jar uban can !!!"
***
Mallaka...
Faumsyk family
Ammin Eemaad

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now