episode 19

20 2 0
                                    

*KAWANCEN MU*
2017

MALLAKA.......FAUMSYK FAMILY.

Bayan su sumayya sun kammala lectures ne, a karshe harda shut gun test ya basu. "Dama Mr TAUFEEQ dan uwanki ne?? Maryam ahmad ta tambaya sumayya. Waye kuma taufeeq? Sumayya ta maida mata da tambayan tana mai yatsina fuska. Mutumin da ya sauke ki daxu mana. Inji maryam
Wlh maryam ban ma taba ganinshi ba sai yau. Dama taufeeq sunanshi? Wlh ya taimake rayuwa na yau ba kadan ba. Cewar sumayya.
Kinsan zayyad dan 300 level da muke gaisawa da shi? To brother dn mr taufeeq ne . Cewar maryam. Ta kuma daura da. Gabaki daya gidansu en iyayi ne sunada feeling sosai, family dnsu are well known, duk haka suke farare tas kuma kyawawa. Tundaga kan maxan har matan auran zamunci sukeyi a tsakaninsu. Dai dai kun wasun su ne kawai suke auran bare, suma sai an tabbata either masu kudi or other way famous. Tare mukayi computer scl da zayyad din ai...

"To ni maraym da kika tasa ni gaba kina mn wannan bayanin ce miki akayi akwai wani abu a tsakanin mu, yau fa na fara ganinshi a tarihin rayuwa na kuma taimako na ma yayi dats all. I doubt ko xamu kara haduwa again. Sumayya ta fada tana tabe baki cox bata san irin halin gulma da hassadan en ajin nan.

" Tab, aiko there's possibility dn haduwarku, anan fa yake aiki office dn Deen. I think shine secretary dn Deen. Halan baku hadu bane sanda kike registration?? Inji maryam.

Nooo ni ba shi nagani ba gaskya. Sumayya ta fada hade da mikewa. To maryam let me get going sai kuma Monday in Allah ya kaimu. Tana gama fada ta fito ta kara gaba ranta duk a bace, Yanxu da wuya in baa dasa gulmanta ba a ajin nan, worst thing data tsana sosai shiyasa ko kawa bata da a class din. Wannan shi ya hanata maida hankali a tunanin taufeeq or whatsoever har Allah ya kaita gida lafya.

*■*

Bayan fadeel ya dan kwana biu da dawowa kuma ya huta sosai, sai ya fara tunanin cewa da zafi zafi fa akan bigi karfe, tun wuri bari ya fadi ma iyayenshi bukatanshi, Allah dai yasa su amince.
Da daddare bayan sun kammala cin abinci, suna zaune suna kallan t.v. tare da iyayen nashi cikin raha sosai fadeeel yayi calling attention dinsu akan he wants to ask dem smth.
" daddy dan Allah alfarma nakeson kuyi min. University dinmu ne ganin cewa i'm part of d best student suka bani offer to b a medical doctor at d university teaching hospital.kuma at d same time i want to expand my studies inyi PhD program dina acan." Fadeel ya dire yana mai faduwar gaba ganin yanda mahaifinshi ya hade rai, mum dnshi kuma na aika mai da harara iri iri.

" zancen banza ma knm, to ban amince ba. A nan gida Nigeria na tsara zakayi aiki. Kuma bana son na kara jin ka tayar min da wannan maganan. "Dad ya dire yana mai hade rai sosai da alama ba wasa a bayaninshi. Ras gaban fadeel ya fadi, ya riga yasan halin mahaifinshi nd his dogmatic behaviour. Shi yanxu ya xe yi??? Kwata kwata he has no plans of coming back to stay in Nigeria.  Fuska kamn xe kuka ya maida kallanshi wajan mum dinshi, dakata fadeel kar ka bata ma kanka lokaci, kasan tunda i'm against tafiyanka abroad balle yanxu. Mum dinshi ta fada. Nan take Mum da dad suka maida hankalinsu kan abin dakeda mahimmanci suka bar fadeel da hankalinshi ya tashi matuka besan ta ina xe iya convincing iyayen nashi ba.!!!

Bangaren wajan Muhammad abubuwa sun kara zafi sosai, tunda yakoma gidansu ya bude dakinshi ya koma, zamanshi a gidan ya dawo dashi da babu duk daya. Hatta abinci wannan ba me bashi da shi da gidan ubanshi.
Gashi kuma har yanxu mahaifinshi baya bi takanshi, gaisuwarashi sam baya amsawa, yayi mai kashedin shigowa part dnshi da sunan gaisuwa in ba concrete bayani da ze mai.  A na haka ne saiga zeenat ta dowo gidan. Tafi karfin wata daya bata gidan, aiko tana dawowa yayrta ta fesa mata cewa Muhammad fa ya dawo, kuma har yanxu mahaifinshi na kan bakarshi na auranki. Wani tsalle zeenatu ta daka kafin tace " dagske aunty, wlh xan aureshi inda nake son aurannan sosai yanxu gashi na rasa me aurena , Allah ya aiko mn da tsuntsu dg sama gasashe, wlh wannan karan baxn bari yayi slipperyn mun ba dole saina aure shi! Mark my words dole in aureshi.!!!

A take zeenat ta cire arnan kayan jikinta. Ta shiga kitchen dan shirya ma Muhammad abinci gangariya. Bayan ta gama ne tashiga wanka tasa kayan mutunci harda zumbulelan hijjab dinta ta wuce side dinshi. Wannan karan bazatayi amfani da boka ba wajn karkato da hankalinshi, da kisisinan ta xatayi amfani ta yanayin da ya fiso, wato a zubin ustazai.

   Da sallama cikakke ta shiga cikin dakin shi, da sauri ta durkusa har kasa tace " yaya ina wuni" zeenat ta fada bayan taji amsa sallamanta da yayi. Kicin kicin Muhammad yayi da fuska, damn aiki yakeyi gaban system dinshi dake dakin, sbd haka ko takanta be kara bi ba. " yaya muhd ga abincin ka nan. " nan ma din banxa da ita yayi. Todan Muhammad ya kware a wannan harkan.

"Yaya kayarda dani, ni yanxu na chanxa halina, shiriya ba ta inda bata xuwa ma bayin Allah wlh ynxu i'm totally a changed person". Ta dire tana mai kuka matsananci gunin ban tausayi. Da abin ya ishe Muhammad sai juyo wa yayi yace "ke! Get out of here, get out of here right nw b4 i descend on you!"  Ya fada murya cike da tsawa.
Zeenat ta lankwasa murya zata kara cewa wani abu knm taga ya mike a fusace, ba arxike ta nannade hijjab dnta ta fita da sauri, ba ita ta tsaya ba saida tayi nisa da part dnshi tana mai dafe kirji da sauke numfashi da sauri da sauri. " dan zaffin kai kawai, bari ka shigo hannuna zanyi maganinka ne". Zeenat ta fada tana mai hararan part din Muhammad.

A kwana a tashi dai zeenat ta dage akan kudirinta, so da dama Muhammad kan ganta ta dawo daga islamia sanye da zumbulelen hijjab da Qur'an a hannunta.kuma a duk inda ta ganshi saita fara yin mai sallama kafin ta durkusa har kasa ta gaisheshi. Sallaman dai yana amsawa dg nan kuma sai ya dauke kanshi dg wajanta.

Mahakurci dai mawadaci to dan har xuciyan Muhammad tafara laushi dg muguwar tsanan da yake ma zeenat, indai har auranta shine zai zama silan shiryawansu da mahaifinshi wanda yake matukar so, to zai iya daurewa ya aureta duk da dai kap a tarihin rayuwarshi mace daya ce yaji Yana kauna matuka kuma yanaji alheri zata zama a gareshi indai ya sameta, wato SURAYYA A ABBA!!!!!!

⊙⊙AMMIN EEMAAD ♥♡♥

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now