episode 4

49 5 0
                                    

KAWANCEN MU
2017

Washegari kowa ya tashi da kuzari, wa enda basu tafiba suna ta shirin tafia gida yau, haka kowa keta kaiwa da kawowa wajan ganin an tsaftace gida tsaf, haka yake wajan su haneefa to Dan suma sun shirya tafia gida amma kafin su tafi sai sun biya sunwa mommy da Hajya kaka sallama dgnan suje gidan amarya sai kowa ya ware gida. Bayan sunje sun ma Hajya kaka sallama ne ta hado su da abun biki sha Tara ta arxiki bayan wanda umma da mommy suka basu. Daganan ne Kuma suka kama hanyan u/dosa legislative qtrs inda gidan Aunty faixa yake. 
Gida yayi kyau sosai komai yaji mashaallah, bayan sun Dan xauna ne sai suka mata sallama suka tafi cike da kewan juna. 
Aunty faixa ne tace ai ba inda su sumayya zasu to Dan ta gaji sosai cox ko jigilan kai cin cin da dumblan ma aiki ne ga baki ta ko ina se xua sukeyi.
Haka su sumayya suka wuni a gidan Aunty faixa suna tayata aiki da fira, har girki tare suka yi, har mijinta ya dawo suna gidan shima ya shga anata hiran dashi suna fadin yanda xasuyi missing dnta da me tare musu in Yaya masood xe musu mugunta. Can Kuma aka gangaro Kan lbrn biki da yanda ya kayatar. 
Haka su sumayya suke yi da Aunty faixa sun maidata kamn kawarsu haka itama tana san su sosai, so dayawa in sukai rashinji ko tsokana ita ke shiga musu to Dan yayyunsu basa daukan raini ko kadan. 
Wajan karfe takwas Yaya mahmoud yaxo ya daukesu, Aunty faixa na jadda da musu cewa gobe su xo da wuri. Shikam mahmoud se fadi yake to karamar mama asha amarci lafya keda ki kara ganin kafan wani ai sai bayan wata daya Kuma , yana fada yana daria cike da tsokana. Da yake ta gama sanin halinshi sai cewa tayi Dalla matsa dama ai ba kai nace kaxo ba Mara kunya aini kam ka gama rainani tunda kafini tsawo ko??
Angonta ibrahm ne wanda ke rike da hannunta yace mahmud ka fita idon mu iyayenka muke ba kannin ka ba tsawon ka baxe bamu tsoro ba, ya fada cikin raha. 
Ahap ai indai Ni xan kawo su sumayya aiko se bayan wata daya. Inji mahmoud. 
Ai ko baka kawosu ba da kaina xn dauko su, inji ibrahm 
Itako faixa da ta daina biye masu ta xagaya bangaren su sumayya tana kara jaddada musu su kulan mata da mamanta sosai suce mata tana nan xua ran Monday. 
A'a fa Aunty kar musawa Hajya kaka rai mun San fa amare basa fita sai bayan wata uku... Ta auna musu harara, dgnn mahmoud yaja mota suka yi gaba. 
Ibrahm kuwa ya kama hannun amaryan shi suka koma gida.
*** *** ***

Yau ta kama ranan Monday, da misalin karfe hudu saura kwata, surayya da sumayya ne tafe cikin kayan islamia suna tafe sannu a hankali suna en hirarrakinsu gunun ban sha'awa, sun karyo kwanan wajan shehu mai Kanti kenan wanda yayi dai dai da sanda surayya ke cewa blad, yanxu ya xa muyi da mallam auwal? Wlh kilan ma ya ganmu lkcn bikin Nan xe ce bamu ji nasihan da ya mana ba wlh tsoron haduwa da shi nake yi.
Inshaallah ma baxa mu hadu da shi ba , ni wlh har kinsa gabana ya fadi to Dan haduwar mu da shi baxe kyau ba, xe iya sawa a bi jikin mu da bulala ko abamu punishment mai tsanani irin yanda Yama su ainau , mutumin Nan.....
Kamn daga Sama suka ga mutumi ya diro gaban su fuska dauke da murmushi yana hura musu ragowan hayakin taban bakinshi. MUSA BLACK knan!
Kai gaskya baby na kin kara kyau wlh, nayi missing dinki ba kadan ba baby, kwana biu banga wucewarki ba baby na. Daga jin magnan na kauraye ne, yana yi yana kallan fuskan sumayya.
A duniya sumayya ta tsani ganin mutumn Nan tun tana tsoronshi har ta bari, gashi yabi ya nace mata kamn Maye . Duk inda ya ganta sai ya taho yazo har inda take gashi yana san matsowa dab da ita sosai kamn xe shge jikinta duk warin Taba yabi ya takurata ba kadan ba, wai shi ala dole Santa yakeyi gashi duk wanda ya ganshi yaga Dan shaye shaye Dan daba. Black gani yake kaf cikin mata ba wanda yakai sumayya kyau da diri.
Surayya Kam ko kallo bata ishe black ba, idan kunga ya mata mgna to bega babyn shi tare da ita bane sai ya tambayeta. Surayya na balain jin tsoron black kmn mutuwantaa.

Mtsw, tsakin da sumayya ta ja kenan tana kallan black up nd down, duk da gabanta na dukan uku uku haka be hanata toshe hanci ba, tare da fadin 
"Dalla mallam ka matsa mana mu wuce baka ganin islamia xamu ne?"
Sorry babay sai kun dawo nayi missing dinki ne shi yasa, black ya fada tare da matsawa ya basu hanya.
Idan kun dawo xamu hadu, ina Nan ina jiranki, I love u.

Sukam tuni sun kama hanya cikin sauri, surayya tai gum da bakinta to Dan gabanta be daina faduwa ba to Dan tana balain tsoron musa black, duk rashin kunyanta baxata iya mishi ba sbd shi kankat ne wajan rashn mutunci. Itama sumayya Dan yana Santa ne shiyasa yake raga mata.
haka suka cigba da tafya dukansu sunyi shiru ba wanda ya kara ma wani mgna har suka Isa islamia. Tun a gate prefects suka xaida su cewar sunyi latti, ko a duke su dukan latti ko Kuma su biya kudin latti.
A nan kuke jin bakin surayya ya bude 
" sai kixo ki danne Ni ki buga er rainin wayau, dalla matsa mana mu wuce. Dayake prefects din duk kusan kawayen su ne Kuma ba wanda besan halin surayya ya ba yasa suka matsa musu suka wuje ajinsu aji biyar.
Kan su tsaye suka wuce cikin ajin ba taree da sun kula da malamin da ke rubutu a kan white board ba. Kai tsaye suka wuce seat din da suka maida nasu permanent ala dole (wato tsakiya). 
" kai su waye haka xaku shigo ma mutane aji ba sallama? Wannan wane irin rashin da'a ne ?"
Jin bakuwar murya yasa suka juya, suna hada ido suka ganeshi, tabbas mutumin da suka gani a office din headmaster ne.
To Meye yakeyi a ajinsu ko dama malamine??
" by d way kun mayi latti, so Ku fitammin a aji sai sanda kuka koyo sallama kafin in kara ganin Ku" 
muryan malamin knn da ya ratsa kunnuwan su a karo na biu.
Taurin kai ba nasu bane, gwanda kawai su bada hakuri kafin karamar magana ya dawo babba. Ba sa so mgn ya kai wajan headmaster ba tunda su din masu laifi ne, gashi wannan sabon malami ne ba sanin shi sukayi ba. Wannan duk tunanin sumayya ne.
"mallam Dan Allah kayi hkr baxa mu sake ba" inji sumayya. Unlike surayya da ta hada giran Sama da kasa bata da niyyan bada hkr ba Kuma da niyyar fita.
To naji, tunda kin bada hkr kije kiyi sallama yanda kowa xeji sai ki shigo. 
Ke Kuma, ya nuna surayya da markern hannunshi, 
Ba ki da bakin bada hkr na? Wa kike daure ma fuska a nan.??
"fitan min a aji yanxu"... 
Fuuu... Surayya ta fice ta bar ajin da harabar ajin gaba daya.
Sumayya dake kokarin shigowa taga blad dinta ta fice cikin fushi, da axama tayi niyyan Binta tana blad...
Idan kika bita kema kin bar ajin kenan so u better come in. Malamin ya fada.
*** *** ***
Mallaka
Faumsyk family 
Ammeen  Eemad

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now