Episode 20

21 2 0
                                    

*KAWANCEN MU*
2017

MALLAKA........FAUMSYK FAMILY

Tun bayan da sumayya ta dawo gida, ta lura da farincikin da blad dinta ke ciki, sosai itama tayi murna jin cewa yayan su na nan tafe, tare da ma blad dinta fatan alkahairi na samun yaya fadeel, to dan tanajin kila in bata sameshi ba mutuwa xatayi. " blad inata kiranki shine kika ki dauka ko?? Inji SURAYYA . Uhm blad yau xuciya na ta kusa bugawa, ni banmaji kiranki ba sam wayana na silent tun jiya da dare. Anan sumayya tabawa blad dinta lbrn abinda yaso faruwa da ita da yanda dakyar wani good Samaritan ya taimakata, to dan da yanxu nashiga cikin list din zarya office dn mr bawa da banyi test dinnan ba. Sam surayya bata wani emphasizing akan side din taufeeq ba sbd bata dade da fitowa dga pit dn da akaso jefata ba, sosai yanxu namiji baya gabanta. Tana dai jiran MR RIGHT wanda tasan sooner or later yana nan tafe!!

Ranan monday tun da safe su sumayya da surayya ke makranta, dayake test aketa musu sbd gabatowan mid semester break. Tun bayan da driver ya saukesu kowannen su ya nufi dept dnshi, haka suke indai suka shgo basu cika haduwa sai can da yamma in lokacin tafiyansu gida ya xama dai dai.

Sumayya ce ke tafe sannu a hankali, a zahiri kuma yunwa ce ke cinta bana wasa ba shiyasa fuskanta sam ba far'a, hanyan dept dnsu surayya tabi taga if she's available suje cafeteria suci abinci. Dai dai gaban mosque kamn ance mata ta daga kai ta hango mr taufeeq da buta a hannunshi, da alama alawla xeyi, sam bataso idanuwansu suka hadu ba, amma saita maxa ta dauke kai ta kuma dukar da Kanta tayi kmn bata ganshi ba. Da sauri ta wuce wajn ba tare da ta kara kallan side din da yake ba.

Tun safe mr taufeeq yake expecting dnta taxo office dnshi ko godiya sbd yasan definitely yanxu tasan ko waye shi kuma tasan office dnshi, amma abn mamaki sai yaga ta dauke kai. Kilan sbd nan duk maxa ne kuma taga sallah xanyi. Taufeeq ya ayyana a ranshi.

Har 4:00 pm yayi taufeeq beji sallaman sumayya ba, ko mekama da ita be kara gani around his office ba. Bini bini ya tashi ya leka ta window dn office dnshi amma be ganta. Ikon Allah taufeeq ya fada. Another classy lady. Abin ya dan bashi mamaki amma kiln ya ganta gobe. Ya ayyana a ranshi.

Wasa wasa har weekdays ya kusa karewa taufeeq bega zuwan sumayya ba, ko da dai yakan hangeta ta window dn office sai yayi tunanin yanxu xata shigo amma sai yaji shiru. Hakan nan yaji abin ya bata mai rai. Haba, ai ko Allah ma yanaso a gode mishi balle mutum. Yana ganinta kmn me hankali. Bari ai Allah xe kara hada su.! !

*■*

Fadeel kam ya riga ya sadakar ba me tankwarar dasu dad dinshi sai hajiyarsu, sbd haka kaya sosai ya diba na cewa sai yayi succeeding xai bar kd. To dan b4 Xmas yakeson komawa U.K. A dai dai lokacin ne kuma aka ba en university hutun mid semester, wanda yayi dai dai da lokacin shagalin babban sallah. Sosai yanayin shagalin sallan yamusu dadi. Fadeel mutum ne da ba ruwanshi sam, kusan kowa nashi ne yana jin dadin ya tasa mutum a gaba yayita tsokanan su yana shan dariya. Damn sun saba yin haka da aunty faixa gashi yanxu basa nan. Sam Baya nuna banbanci a yanda yake wasa da sumayya ko surayya, saidai hiransu yafi tsawo da surayya sbd tafi biye mishi suyi tayi. Sumayya ta taba mai complain da cewa " su yaya ba kirki, shine a U.K. sam baka taba tuunawa da mu, ko sau daya baka taba ko kiran mu ba."
" hmmm baxaku ganeba my siss, inason boko sosai fa musamman my field shiyasa smtyms nike mantawa da komai fa. Amma time to time ina tunawa my adorable sisters ♡ " fadeel ya fada yana murmushi mai kara mai kyau.
Ya dora da eyya ku tayani rokon hajya kaka mana wlh i hav un finished task sosai a U.K. (to dan koda fadeel yama hajya kaka xancen komawa UK, da masifa ta balbale tare da fadin saidai ya maida hankali kan neman matan aure to dan saanin shi masoud da naxeefi har sun tsaida mata, damn su kadai ne suka rage basuyi aure ba a maza.)
Nan take annurin fuskan surayya ya dauke, ta rasa gane focus din fadeel,, har yanxu batasan ko a wani matsayi ya ajiyeta ba, da tana murna ta fara succeeding gashi yanxu kuma yanaso ya gudu ya barta (lol).

"Yaya kmn kana gudun Nigeria, kamn bakaso ka zauna tare damu, yaya muna sanka dan Allah karka tafi." Surayya ta fada muryanta har yana rawa. Fadeel dake da niyyan tashi da sauri ya matso kusa da ita, ya rike hannayenta biyu cikin nashi ya matsa su da dan karfi, murya cike da kulawa yace" it's not like dat cute sis, is abt smth very important, smth i made vow to it, i can't abandon it not for now, so pls ku fahimceni, one day i Will surely come back nd live here with u all" . Wani Takaici ne ya tokare surayya, bata san sanda ta furta " is there another woman? I mean d vow u made is connected to a lady right? Ta tambaya idanuwanta cike da kishi. Da sauri fadeel ya dan zaro ido, da alama be zaci xatayi irin tunanin nan ba. Da sauri ya saketa tare da mikewa, yace ' haba cute sis sai kace wani wawa, haha mace kadai bata kai matsayin Dan zata maidani UK ba. So stop thinking nonsense.' Kafin ya fita ya bar parlourn.
Sumayya kuwa tun daxu take kallonsu cike da shauki, xuciyanta na bugawa da sauri sakamakon wani tunani da ta fara. Da sauri kuma ta kauda tunanin . Bataso ta Kara sa kanta cikin damuwa, musamman ma na maxa, she dnt knw if she can trust dem anymore!!

Ranar wata lahadi, sumayya , surayya da fadeel sun dawo dg koyon tukin mota, fadeel da surayya na tafe cike da nishadi, sumayya kam sai turo baki takeyi tana ta kunci. Suna sallama gidan hajya kaka suka tadda ita gaban murhu tana jefa dan wake a tsakar gida. A gajye suma suka nema waje tsakar gidan suka xauna. " wlh hajya kaaka nake fada miki mun kusa fasowa gari, ashe ma driving ba wahala, ki bani kwana kadan har Lagos xamu tuka ki nida blad dina. "

Kaka ta washe hakora tace" dayake bature da kanshi ke koya muku wato har kun fara iyawa??"

A'A hajya kaka surayya ce kadai ta fara iyawa, ammn wancan matsoraciyar ko ba abinda ta iya sai tsoro da ihu, fadeel ke nuna sumayya yana dariya. A take ko sumayya ta kara cuno baki, tace eh din gwara na shiga driving school hankali na kwance......
A dai dai Lokacin sumayya taji kamn ana mata yawo a riga."wai meye nake ji kmn ana mn tafiya a jiki?" Sumayya ta fada tana soshe soshe.
Laaaa blad daxu kamn naga hundred legs ta wura ren ki..... kafin surayya ta rufe baki sumayya har ta daka wani uban tsalle tare da wani ihu sai jikin fadeel, a tare suka kara mikewa sumayya nata tsalle tare da ihu. A kokarin fadeel ya taimaka mata kawai sai ya nemi ya daga mata riga. Da sauri sumayya ta ture shi da iya karfin ta. A dai dai lokacin kaka tace gashi can, tana nuna kwaron, da sauri kuma surayya ta tafi da tsintsiya domin ta bige shi.
Sumayya da mugun kallo kawai take bin fadeel, shi kam sam bai lura ba sai da ya maida kallonshi kanta kafin ya gani. " ahhh what....see dis thing wooo, i'm just trying to hel......, mtssss fadeel ke fada tare da kallan sumayya kallon up nd down yana yatsina fuska, wanda yake nuna inma sumayya na tunanin da gayya ya tabata to tana hauka sbd shi bega abn tabawa a jikinta ba. Daidai lkcn ne kuma ya koma inda yake ya dau wayanshi ya maida hankalin shi kai.
Sumayya kam data gama harzuka tace blad kixo mu tafi ni na tafi gida, ta figi gyalenta. Da sauri surayya ta jawo nata tana ta jirata. Dai dai kofan fita sumayya ta waigo ta kalli inda fadeel yake, dai dai shima ya daga kanshi domn ya kara nkallonta, a take idanuwan su suka hadu, ta murguda mai baki sukayi waje, shikam fadeel sai ya tsinci kanshi da yin lallausan murmushi yana shafa suman kanshi......!!!!!

AMMIN EEMAD ♥

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now